Sashe 31
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
dad'i toh na gobe baxai yiba garama a duba kodai a had'a su auran ko koma shi Aliyu yayi hak uri ayina babagana tunda shine magajinka indai da gaskiya da kuma adalci... Ke ma dai kya fad'a mai. Cewar hajja gajiram tana karkad'a k afarta sai faman huci take dama abinka dame jiki tabarakallah Masha Allah. Sai da ya gama jin ta bakin su sannan ya kallesu cikin salo na manyantaka ya fara magana; A duk cikin tsarina bana yanke hukunci koda a cikin yaranane sai na bawa kowa hakk'insa ke gajiram idan kinyi k arya yanzu a gurin mahaliccinmu ba'ayi sau nawa ina kiranki keda babagana akan maganar yayi aure? Sau nawa nake ce miki idan beyi ba da kaina zan zab'a mishi mata dake da shi kuka nuna min ku bayanzu ba,shi cewa yayi min ma dakyar idan zai yi auran saboda bashi da burin ajiye mata,amma wai yanzu ke zaki min maganar cewa sai an jira babagana yayi aure sannan Aliyu hydar zai yi saboda ni banda iko akan ku ko?! Suka yi tsit kamar ruwa ya cinye su yayi murmushin takaici tare da ci gaba da magana; Amman da yake ba kuda adalci ni zaku cewa na fiye san kai,toh ku gaya min ta wanne fanni nake muku rashin adalcin?! Oho dai ai kowa ma yasa ni...! Hajja gajiram ta kuma fad'a,ganin suna neman tayar mai da hawan jini ne yasa shi cewa; Toh dai na fita hak inku na sanar muku,zai yi aure acikin watan nan kafin ya dawo daga k'arasa clearing d'in project d'inshi nake so akai kaya ayi duk wasu abubuwan da za'ayi,daya dawo sai d'aurin aure.koda baku tambayi wad'anda zai auraba dan karkuce ba'a sanar muku ba to ba kuwa bane wadda ta kasan ce *SON RAN* shi a kano iyayenta suke,sai kuma ta biyun da takasan ce *ZAB'IN IYAYE* wato Aminatu 'yar gidan Baffan su wato kawu Mai Alooma Ghaji,karku ce ban gaya muku ba ku tashi kuje ina buk atar hutu..... Ganin ya dafe k'irji yasa hajja yakolo saurin mik'ewa tabar parlorn da sauri sannan hajja gajiram ta zabga wani mugun tsaki ta mik'e itama tabar parlorn tana maganganu had e da lailayo ashar ta d urawa hajjagana da zuri arta kaf a zuciyarta, girgiza kai kurum maimartaba yayi tare da yi musu fatan shiriya nan da nan ya fara tari wanda dai-dai lokacin Hajjagana (Ammin su hydar) ta bugo mai waya.Da kyar ya iya d'agawa duk da haka yana yin tarin tanajin shi ta dinga mai sannu yana amsawa da kyar kafin wasu 'yan mintina tarin ya lafa mai Ammi tace; Sannu ka d'an sha ruwa mana. Sai a lokacin ya juya ya d'auki cup tare da tsiyayar zam-zam dake gefansa yayi basmalah yasha, Na gode matar kwarai,Allah yayi miki albarka. Maimartaba ya fad'a bayan yasha ruwan zam zam d in cikin jin dad'i Ammi tayi murmushi tare da cewa; Amin nagode Abu Hydar. Suka d'an tab'a hira duk akan yadda tsarin bikin zai kasance kafin su ajiye wayar kowa na farin ciki da yadda hirar ta kasance musu. _*KANO_* Flight yabi ya sauka a Malam Aminu Kano International airport, already dama daddyn Basma ya riga ya tura mai da driver dan haka suna sauka driver yayi wa yareemah Aliyu hydar waya suka had'u ya d'akko shi,basu tsaya a ko'ina ba sai a unguwar sultan road dake nassarawa GRA a kantameman compound d'in gidan su princess Basma Lol. Idanta kyar akan motar ta window har ya zuro kafafuwan shi ya fito,tana ganin shi taji wata zazzafar k aunar shi ta kuma cakar mata zuciya, Hmmm yama za ayi na iya rabuwa da sugar boo?haba this can't be happening Ta fad'a a fili tana murmushi,Yayan ta ne Usama yayi mai jagoranci zuwa cikin sitting room d'in da aka k'ara gyara shi sai kamshi yake tamkar company d in yin turaruka,yareema Aliyu hydar kenan sai wani taku yake tamkar yana jin kyankyami ya k'arasa ya zauna bayan sun gaisa da Usama wanda zasu yi kai d'aya a shekaru dashi Usama na fita wayar Aliyu hydar ta fara neman agaji yana ganin kiran yayi wani murmushi irin na gefen bakin nan sannan ya d'aga tare da karawa a kunne yace; Guy ya?! Modu ya d'anyi tsaki kad'an cikeda takaici yace; Wai kana inane tun d'azu nake neman ka?! Murmushi yareemah Aliyu hydar yayi wanda har Modu na iya jiyowa sannan cikin isa yace mai; Kano! What?...!" Dai-dai lokacin Basma da layla suka shigo cikin sitting room d'in yana jin shigowarsu amma yak'i juyawa harsai da suka k'araso idanuwan su ya had'a dana juna ta sakar mai murmushi tana bin kayan jikin shi da kallo don bak aramin tafiya yai da gangar jikinta da zuciyarta ba sosai yamata kyau, Sanye yake cikin d inkin riga Bauchi style(buhari style)riga da wando na dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya tasha aiki dark color se hular zanna bukhr datai mugun amsan kayan dakuma gashin kansa daya kwanta luff Kai abinde sede afurta kalmar tubarkAllah kawai don d an sarkin bornu yayi kyau babu k arya gakuma uban k amshin dayake tashi daga jikinsa... M serious guy,kaje kasamu Mami tarakaka bulabulin ngarnam d in ko Allah zesa adace it yakashe kiran yana daria ahankali don sosai yake jiyo k arar sautin tsakin Modu yasan yanacan yakusa fashewa don haushi, Team#SRKZB?! Y,ALIYU(BASMA AUR MEENAH?!) WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB IN IYAYE*