Sashe 103
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*80* *END...* *G*urfane sarki Aliyu hydar yayi a gaban maimartaba maimurabus yayin da gefe guda Ammi ce take dama fura da nono kasan cewar baya son shan wadda akayi blending d'inta,kusa da Aliyun kuma yareemah Ngari ne da yareemah babagana sai Modu a kusa da Ammi duk girman parlor'n amma yaje ya nanik'e mata. Shehu Bulama ya gyara zama yana kallon Aliyu hydar yace, Ranka ya dad'e kai muke jira ka taramu kayi shiru sai faman kallonmu kakeyi ince dai lafiya ko?! Kuma gyara zama Aliyu hydar yayi tare da shafa gashin dake zagaye a fuskarshi,sunkuyar da kai yayi yana neman ta inda zai fara dan kowa na gurin shi yake kallo ganin haka yasa shi cewa. Amm....Dama....Baba abinda yasa nace zanyi magana daku akan maganar kujerar da nake kai ne.. Yayi shiru su kuma suka sake zura mai ido danjin k'arin bayani,shi kuma ya sake sunkuyar da kai sannan yace. Ina son na sauka daga kai na bawa d'an uwana zaifi kulawa da ita sannan shine yafi cancanta da ita ba niba,ina son na sauka na bawa baah Ngari dan Allah karkuce a'a tunda duk d'aya ne nida shi. Bak'ara min mamaki kowa yaji ba amma banda Modu kasan cewar tare suka shirya komai,baki bud'e shehu bulama yake kallon Aliyu hydar kafin ya d'ora Modu ya karb'e zancen da cewa. Haka ne baba wallahi gara ya sauka ya bawa wanda zai iya dan wannan sarkin kawai cukwan kujera ne amma baya komai sai tara mutane yana binsu da eh ko a'a, dan Allah baba a bawa baah kawai... Why me brother?ni yanzu me na sani akan sarauta zaku ce a bani?bana so baba bansan komai akanta ba taya za'a bani ragamar jagorantar mutane?kuna gani sai yanzu nake fara sanin abubuwa da kuma yanayin rayuwa, gaskiya bana so a bawa babagana idan shi yana ganin baya so. Cewar yareemah Ngari yana magana cikin yanayin damuwa da jimami dan shi yasan akwai abubuwan dabe sani ba dayawa a cikin masarautar,baba maimartaba yayi shiru na tsawon lokaci yareemah babagana yayi dariya kowa ya maida hankali gurin shi yana dariyar yace, Ni za'a bawa sarauta ko?hmmm da kunjawa masarautar nan zagi dan wallahi sai tayi rugu-rugu sabida ba zaman fada zanyi ba,babu abinda na tsana a rayuwata irin naga an takura min ko an samin ido bare a kaiga kawo min koke-koke kunsan babu wanda zan saurara bikon matata nake yi kuna gani dai tak'i dawowa. Dariya Ammi tayi jin abinda babagana ya fad'a sai faman kad'a kai takeyi yayinda shehu bulama ya sake gyara zama ya kalli Aliyu hydar sosai dan yana son gano da gaske ne baya son sarautar kokuwa dai akwai abinda yake damun shi,murmushi ya saki sannan yace. Idan na fahimceka Aliyu kana sone kawai ka zauna a gurin matanka ko?! Shiru Aliyu hydar yayi domin da kunya ya amsa wannan tambayar ta maimartaba,muryar Ammi suka ji tana cewa. Hakuri zakayi Aliyu kaci gaba da rikon wannan matsayin domin Yayan ka yafika gaskiya kafishi sanin duk wasu abubuwa dake faruwa da kuma akeyi ko ake so a cikin masarautar nan tunda dai shi duk a kwance yayi rayuwarsa so kar a takura mai gaskiya. Turo baki Aliyu hydar yayi jin abinda Ammi ta fad'a,wato da alama tafi son Ngari akanshi,baba bulama yana kallonshi duk turo bakin da yake yi yayin da Modu keta yi mai dariya harda su gwalo nan ma ran Aliyu hydar ya sake b'aci yama dena kallon Modun dan yaga alamar so yake ya konamai zuciya da takaicin shi. Toh ni duk naji abinda kuka fad'a sannan na gano solution akan abin a zahirin gaskiya dama a k'a'ida yareemah Ngari shine magajina abinda yasa na sakarwa Aliyu hydar ragamar sarautar shine ganin bashida lafiya shi Ngarin kuma ni nagaji ina buk'atar hutawa hakan yasa na bashi, Toh kuma tunda yanzu Allah ya tashi kafad'un shi magajin nawa sai a bashi kujerarsa da matsayinsa batun besan komai ba akan masarauta be tashi ba sabida yana da duk wasu qualities da ake buk'a a gurin nagartaccen sarki dan haka idan Allah ya kaimu jibi juma'a kenan sai a sauya ni kuma yau sai na fara shaidawa shuwagabannin da ya kamata ace sun sani Allah ya taya shi riko inaji a jikina zai iya Aliyu kuma sai aje aji da iyali. Aka kyalkyale da dariya musamman Modu shida har buga hannu yake a kan tumtum dake kusa dashi,hararar Aliyu hydar ya dinga aika mai amma be fasayi ba musamman idan suka had'a ido shi kuwa Ngari shiru yayi kanshi a k'asa yana hawaye ashe yana da tsawon kwanan da za'ace yau shine da mulkin Barno,shehuri ta dawo hannunshi shida a da yake a matsayin mutum-mutumi Allahu akhubar. Cikin kwanaki uku aka fara gudanar da shirye shiryen nad in sarautar yareemah Ngari,duk wasu manyan dignitaries na kasar nan seda aka aika masu da invitation cards na nad in sarautar,sarakuna,masu hannu da shuni yan kasuwa kai dama manyan malamai na nahiyar afrika gaba d aya.. Zuciyar Aliyu Hydar k al k al kamar anwanketa da ruwan klin se wani dashe baki yake yana murmushi kwance suke akan Coach na dakin su shida Meenah data sanya gefen rigarta ta toshe hancinta dashi,cikin tab e baki hade da shafa gashinta yace, Ajlaal wai meye hakane yanxu kuma wani laipin nayi?!i just can t hold it anymore.. Cikin sake ture hannunshi daga kanta ta cuno baki gaba, Banason warin kayan ka yana sani kaman Xanyi throw up Cikin gwalalo idanuwa Aliyu Hydar ya dan xame ta daga jikinsa ya sanya idanuwansa cikin nata da sauri yace Wifey kikace mene?! Kinsan wani turare na fesa ajikina kuwa,latest Armani ne fa Nide kobah wari nake jiba.. Cikin kasa da voice Aliyu Hydar kamar mai rada yace, Yakike so nayi yanzu uhm?! Shiru tai tana sake danne hancinta da kasan rigarta,hannu yasa xe shafi cikinta ta goce, Baby yakike so nayi?! Kacire kayan pls banason warin so irritating.. Tohm Mrs Aliyu I will yanxu ma kuwa.. Mikewa yai ya cire kayan gaba d aya sannan ya koma bathroom yai wanka yaxura singlet kawai da boxers kasancewar a sashen Meenan kwanansa yake.. Dakyar ya iya janyota jikinsa da turjiya da komai don sam batason ya kusanceta,cikin shakar kamshin gashin kanta Aliyu ya tallafo fuskar Meenah ya sakar mata da peck akan hanci cikin wata irin siga yace, Ajlaal.. am ya Aliyu Kinji decision dn dana yanke ko?? Uhm Ammi ta fadamin amma nibanji dadi ba Why?! cewar Aliuu cikin gwalalo idanuwa cikeda son jin Meyasa batason yasauka daga karagar mulki Ya Aliyu kobah kullum nad i yafi maka kyau ba Allah kaman ninja turtles baka ga yadda turban din yake maka kyau ba.. Aliyu da farko yai tsammanin wani almuhim abune yasa Meenah rashin jin dadi jin tabakinta yanzun abinda tace yasanyashi sakin daria ba kakkautawa yi yake yana dafe da ciki cikin kuluwa Meenah tasaki tsaki tana turo baki gaba,shiru yai yana dedeta kansa M sorry Ajlaal abunne yaban daria buh abinda xaki lura shine bancancanci sarautar bornu ba Ajlaal ni lover boy ne nafuson muje somewhere far far away from Nigeria ma muyi enjoying life d inmu daga ni se ke Mrs Aliyu Hydar.. Murmushi Meenah tai dakyar tasanya hannu tai hugging dinshi dama kiris Aliyu yake jira ya damkota yana sumbatar koina na jikinta harde hakarsa ta cinma ruwa seda ya samu nutsuwa sannan ya kyaleta yana shi mata albarka ita kuwa banda kuka da kai masa duka ba abinda take.. <><><> Ranar asabar da misalin k arfe sha biyun rana aka fara gudanar da nadawa yareemah Ngari nadin sarautar jihar Bornu,ahankali aka sunce nad in rawanin kan Aliyu Hydar aka maidashi kan usman Ngari tareda karbar sandar mulkin hannunsa abaiwa Ngarin sannan me shela ya shaidawa jama a cewar yanzu yareemah Ngari yakoma sarki Usman Ngari Shehu Bulama while Sarki Aliyu Hydar yakoma Yareemah Aliyu Hydar kamar yadda yake a da,ba abar fada ba seda aka sake sunce kan rawanin wazirin sarki nada aka nad ashi akan babagana yaxamto shine wazirin sarki Ngari shehu bulama,Daria Aliyu da Modu suka shiga yi ba kakkautawa seda mai Alooma ghaji ya musu dakuwa sannan suka fice sum sum suna gimtse sauran dariar Haaa at long last cewar Aliyu Hydar yana goge gumin dake tsattsafo masa a goshi, Ai Guy namaka murna dole kayi gumi mutumina sarauta ba wasa bace.. m telling you yadda kasan freeing dina akai daga prison haka naji kai,Allah katsayar akansu Kecewa Modu yai da daria cikin daria yace, Sekace wani balai?! Abun so ne fa Idan abun so ne dan Allah mukoma abaka plss Da sauri Modu yadena dariar yawani tab e baki, Hum uhm akai kasuwa wallahi,kaima kasan nafika rashin son sarauta tunda har baba ya kirani jia da daddare yaji tabakina akan naxaba title da nakeso tuni naja pullstop nace masa wlhy banaso sede nan gaba kuma Daria suka shiga yi kamar wasu xautattu seda Mai Alooma Ghaji yasake fitowa da kansa daga cikin wajen taron yai masu dakuwa tareda alamar subar wajen tukun sannan suka nufi cikin garden kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki dubada yadda fuskar kowannensu ke d auke da annushuwa tsantsarsa... Koda suka xauna a garden Modu ne yadubi Aliyu dake k arin saka earpiece akunnensa cikin isa yaxare earpiece din yana jefa masa harara, Kaifa tsiyata dakai kenan wallahi one min ai mutunci another minutes ka koma arrogant dnka to wabillahil lazi idan ka soka shirmen abunnan a kunnenka sede Mommodu yabar wajen nan Dan murmushi Aliyu yai hade da sa hannunsa yana gyara links din dake sanye jikin dakakkiyar sky blue dn getzner shaddar dake jikinsa wanda Modun ma itace sede kowanne tasa kalar davance cikin nuna rashin damuwa yace, i abunda xakace guy..Ina naxarin wani abu ne Tsaki Modu yai batare daya dubeshi ba yace, Toh yanzu daka sauke sarautar ka ina xakaje ne kasande baxakai nisa da baba ba atoh?! Sauke ajiyar zuciya Aliyu Hydar yai yana shafa cyboc d insa, Bornu xan bari guy I was born and raised n bornu nayi aure a bornu na xauna a bornu haba abun yayi yawa anason change of environment ai ar daria Modu yai cikeda tsokana Modu yace, Okay Yola xaka koma kenan?! Aa kamanta kano xan koma gidansu Basma Yo ai