← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 107

Sashe 8

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Wannan shafin nakune;
Humayra b (MELODY)da VESMERH er lele
10
Bayan modu indimi yashiga fada yad'ebi gaisuwa wajen mai martaba sun d'an tab'a hira,mai martaba yace dashi yaje yahuta tukun da safe xe nemeshi,d'akin dake kusa dana yareemah Aliyu Hydar aka gyarawa modu indimi kasancewar nanne dama d'akinsa,modu indimi yana fita daga fada ya nupi sashen hajia gajiram. Saboda abune dayaxama wajibi inde kaje masarautar tofa bayan ka kwashi gaisuwa wajen mai martaba to dole ka kwashi wata gaisuwar wajen matansa,yana zuwa sashenta jakadiya ta masa iso yashiga ya gaisheta murmushi fad'ade a fuskarta ta amsa kaida kagani kasan akwai wata a k'asa,shi kanshi modun yayi mamaki k'warai matuk'a bayan sungaysa ne ya nupi wajen hajia yokolo itama amsawan tai da fara'a;
"Banyi wushe(lapia qalau babana)ya ya makaranta an k'are kenan?!"
"Alhamdulillah Aunty.A'a nazo... Naxo ganin gidah ne kawai"yatsinci kanshi dabata amsa haka
"To Allah yabada sa'a"
"Amiin aunty nagode"yak'arashe xancen tareda mik'ewa tsaye
Sallama yamataa sannan yafice waje yanupi apartment d'insu wato b'angaren su yareemah Aliyu Hydar,d'akin yareemah Aliyu Hydar yafara nufa tareda yin knocking kusan sau biyar kafin yareeman yace;
"Yasss"
Ahankali modun yabud'e k'ofan yashiga,kwance yahango yareeman kansa asama yana kallon p.o.p da alama tunani yake jin sallamar modun ne yadawo da aliyun daga tunanin daya tafi,amsawa yai had'e da gyara xaman dayai..
"The charming prince..."modu indimi yafad'i haka yana me bin fuskar yareemah Aliyun da kallo had'e da bashi hannu su gaysa.
"Guy..yanzu kaxo?!"
"Noo nad'an jimafa though ba sosai ba"
"Oh okay.."
"Meke faruwane guy?! Fuskarka duk ya fad'a kayi looking so pale,lokaci d'aya kaman wani wanda kai wata kana cuta,haba mana daga maganar aure,idan nine kaima wallahi mata hud'u xan aura rana d'aya"yak'arashe xancen yana dafa kafad'ar Aliyun
Murmushi Aliyu Hydar Yayi sannan yace;
"You are sick..."
"M serious wallahi,y'ammata gasunan birjik a family d'innan ga y'ammatan family d'in uncle mai idris katakarmabe dake t'chad,gana uncle Goni Mele dake nan nan bulunkutu..."
Siririn tsaki Aliyu Hydar yaja had'e da mik'ewa tsaye da sauri modu indimi ya rik'o hannunsa yadawo dashi yana daria k'asa k'asa;
"Shikenan my mouth pim.. Anbar xancen .Yawwa d'axu xanshiga fada wajen baba nahango jakadiyar Aunty gajiram taraka wasu babes sunshiga mota,kagansu guy?!full option ga skin d'insu so gloomy kuma suna kama da aunty gajiram sosai,dan Allah ko kasan su?!"
"No I don't"shine kawai abinda yareemah Aliyu yace
"Please guy..."
"Kaima bakasan suba bare ni"
"To ni xanyi k'ok'arin sanin su waye,cuz babes d'innan akwai structures,though wadda tai laffayan tafi kyau"
"Okay fine...,ya kukai da baba?!"cewar Aliyu Hydar
"Nothing much,yace de anjima ze neme ni,koya ake ciki de i will let you know"
"Good"
Mik'ewa modu indimi yai had'e da d'aukar jakar system d'insa bin d'akin yai da kallo kamar me neman wani abu,sannan ya dubi Hydar daya sake maida kansa kan p'o'p kai kace tv ne a jiki tsabar yadda yamaida hankalinsa can yana tunani
"Guy nikam ina babagana?! Banganshiba tun shigowata"
"bansaniba wlhy,rabona de dashi tun jiya"yabashi amsa still kansa a p'o'p
"Okay... Tohm later barinje nai wanka nad'an samu nap"
"Alright "
Murmushin takaici modu indimi yai had'e da girgixa kansa tareda jajantawa irin na halin ko'inkula da yareemah Aliyu Hydar kedashi,abu meyakwan yayi baya se k'ara gaba yake,fita yai had'e da rufe masa k'ofar sannan yashiga nasa d'akin..
WASHEGARI;
Da safe bayan modu indimi yai wanka fada ya nufa a bakin k'ofar shiga sukai kicib'is da yareemah Aliyu Hydar yafito shikuma xe shiga,murmushi modu indimi yai masa gaisawa sukai sannan yace;
"Tun asubah amma kake nanko?? Thought you were still lying on bed kamar baby..."
Daria kawai Aliyu Hydar yayi bebashi amsa ba,shima modun dariar yayi sannan yashiga cikin fada,gaisawa modun sukai da mai martaba sannan mai martaba yafara magana;
"Nasan zakai mamaki k'warai matuka na abinda yasa nace kazo ko?!"
"E..Eh baba"modu yabashi amsa kansa a k'asa.
"To bawani abun bane illa wani temako dana keso kayimun ina fatan zaka bani had'in kai?"
Murya atsorace modu yace;
"Insha Allah baba"
"To modu wannan magana da zamuyi dakai tsakaninmu ne ni da kai sekuma Allah daya haliccemu.."
"To baba Insha Allah"
"Modu,shekara da shekaru kunsan ina fama da ciwon lupus,wanda haryaci k'arfina dole se anmun dashen k'oda wanda kafinnan dole ne se anyiwa wajen remedy sosai,shine likitana yace indena stressing kaina yakamata nasauka daga kan karagar mulki.. Ina fatan kasan inda maganata ta dosa?!"
"A'a baabaa"modu indimi yafad'i haka muryarshi a sanyaye
"To modu xanyi murabus ne daga karagar mulki kuma babu wanda ya cancanta anad'awa wannan rawani fyace Aliyu... Kuma kaga babu inda aka tab'a sarki babu Iyali ko??"
"Eh baabaa"
"To wannan shine abinda yasa nakiraka modu,bakomai bane fyace inaso ka bincikomin Wacece yarinyar da Aliyu yake nema acan,shin y'ar mutunci da dattako ce ko kuwa? Ina fatan ka fahimta??"
"K'warai baba nagane"
"To yacemin acan makarantar tasu take,harnake tambayar sa shin kasanta?yace a'a don basu gama dedetawa ba tukun,amma nasande baxaka rasa wata hanyar daxasan wacece itan ba ko?!"
"Eh baabaa Insha Allah zan fara gudanar da bincike da zarar nakoma"
"To Masha Allahu,naji dad'i kwarai dagaske,idan kagama shirinka xuwa gobe ko jibi seka koma saboda banason ad'au lokaci..."
"To baba"
"Kaima idan da akwai wadda kuka dedeta sekai magana"
"To baba amma bamu gama dedetawaba tukun"
"To Allah ya xab'i abinda yafi alkhairi,kaima kayi k'ok'ari ku dedeta kaji ko?"
"To baba"
Modu indimi yace hakan tareda lulawa duniyar tunanin karfa shima ai masa irin na Aliyu Hydar,duk xancen dame martaba yakeyi hankalinsa baya jikinsa k'arshen xancen kawai yaji;
"Zaka iya tafiya"shine kawai abinda modun yaji,
Rissinawa yayi yaiwa mai martaba sallama sannan yafito dede k'ofar fada yaci karo da jakadiya mangu(hadixa) jakadiyar hajia gajiram se raba ido take a tsorace,duk'awa tai tana gaisheshi ko takan gaisuwar data kemai bebiba yarab'a tagefanta ya wuce saboda yadda yakejin ransa,yana wucewa tasauke nannauyar ajiyar zuciya ganin bai gano komai ba,a d'ari taja lomatsatstsun k'afafuwanta tai sashen hajia gajiram.
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo:
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!

(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Wannan babin nakine *_Aunty maijiddah
Allah ya k'ara raya mana y'an biyu cikin tafarkin islama yakymu aurensu musha biki.!

11
Jakadiya mangu(hadixa)na xuwa wajen hajia gajiram ta zub'e a k'asa tana raba idanuwa bayan ta kwashi gaisuwa,wata baiwa dake gefan hajia gajiram ce tafara magana;
"Sarauniya ta amshi gaisuwarki jakadiya mangu,shin meke tafe dake wannan karan?!"
Jakadiya mangu tak'ara kaikace baki tana magana irin tasu wanda suka shahara a harkar munafurci;
"Allah yasake ja da ran uwar d'akina tadad'e tayi k'arko,kamar yadda jiya idanuwana suka gane mini modu bunami na indimi ban runtsa ba haryau danai asubanci zuwa fada.."shiru tai tana jiran amsar daxa'a bata
Firgigit hajia gajiram tai tareda mik'ewa daga kwanciyar k'asaitar datai Lalle jakadiya taxo da labari kenan,sallamar sauran bayin dake babban parlorn tai had'e da maida dubanta ga jakadiya mangu datai k'asa dakai tana jiran amsarta,dogon ajiyar zuciya gajiram tai sannan tafara magana;
"Kiyi hanx
arin sanar dani meke tafe dake,shin meke faruwa?! Namiki alk'awarin kud'i me tsoka,had'e da tufafi na alfarma ko kuwa ki fad'i duk abinda kikeso ni gajiram namiki alk'awarin cika maki burin ko menene kike buk'ata"
"Nazo da labari marar dad'i wanda tun sanda najishi jikina bebar tsuma ba,uwar d'akina ina fatan abinda bakina da labb'ana xasu furta yanxu babu tsattsauran hukuncin daxe biyo baya agareni?"tak'arashe maganar cikeda firgici
Murmushi hajia gajiram tai wanda har seda wawakeken bakinta yadashe gutsatstsarun hak'oranta suka bayyana awaje.A k'arafafe tafara magana;
"Karki damu jakadiya mangu,kada ki manta ked'in ta wajen muce,tun kafin musan yadda zamuyi k'ullun kutingwilar barin hajjagana(mahaifiyar Aliyu Hydar)daga shehurin nan muke tare dake,kuma hardake acikin mutanen da suke cikin abu mafi soyuwa awajena da baxan tab'a manta alkairin da sukaimin ba domin kinbada babbar gudanmawa wajen sake dunk'ufar da rayuwar yareemah Ngari,tabbas ked'in wani haske ce arayuwarmu mangu,domin badan keba da bamusan taimakon da ko waye boka na sambisa ba da har bak'in asirinsa tareda aljanunsa xedinga bibiyar ahalin Hajjagana ba,tabbas tun kafin ki fad'i koma menene mangu dagayau na y'antaki kuma nak'ara miki matsayi kece babbar jakadiyar shehurin nan"
Yadda kukasan ancewa mangu inta mutu aljanna zata shiga haka tadashe hak'oranta da suka rine saboda tsabar cin goro,ta wangale mici micin idanuwanta had'e da gyara zaman gurfanen datai tafara magana;
"Tabbas banda bakin gode miki uwar d'akina,hakik'a kalmomin bakina dazan mik'o godiata sunyi kad'an,uwar d'akina kisani zan iya salwantar da rayuwata akan inganki keda iyalinki koyaushe cikin farin ciki (Mak'aryacin mutum beyiba*
kujifa a life worth dying for,Allah karabamu da sharrin masu sharri/miyagun mutane)ke kika y'antani nadawo mutum kika sharemun kukana,uwar d'akina insha Allahu har izuwa ranar da mai duka ze karb'i numfashina baxan tab'a sab'a miki ba bare inbijire miki, nagode k'warai da Wannan kambamawa Allah ubangiji yaja da ran uwar d'akina ki dad'e kiyi kark'o"
shiru tai had'e da ajiyar zuciya tareda kad'a kai irin na jajantawa d'innan sannan tacigaba da magana;
"Da asubanci naje fada ko zan jiyo wani rahotan aikwa kunnuwana sunjiyo muni abinda harna koma ga mai sama baxan mance ba" nande ta fyed'e mata bindi harda wutsiya ma'ana tafada'a mata duk abinda tajiyo nadaga abinda mai martaba da modu indimi suka tattauna d'axu a fada....
Yadda kukasan jirgin sama haka gajiram tamik'e tafice bata zame ko'ina ba se b'angaren yakolo abokiyar asirinta kuma kishiyarta da suka ajiye tsoron Allah waje d'aya suka rungumi shirka(had'a Allah da waninsa)dankwa se abinda boka na sambisa yace dashi suke aiki koda kuwa abun yazarta k'ololuwa a shirka haka suke rungumar kowanne hukunci ya xartar agaresu hannu dubu bama biyu ba.......
12
Wannan shafinma nakine AUNTY MAIJIDDAH M
Nagaisheki gaisuwa mai d'imbin fatan alkhairi
may you be forever blessed
Chapter 8 · 0% Book details