Sashe 27
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
d'aya ya takura ya k'agara yaji ance su koma gida,yana son ganin yareemah Ngari domin yanzu yana yawaita mafarkin shi cewar gashi ya warke yana magana yana iya tashi zaune ayita hira duk sanda yayi mafarkin nan ranar jinshi yake cikin nishad'i wayar shi ya janyo yana son jin muryar Basma sannan ya sanar mata cewar su biyu zai aura koya zata ji idan ya sanar mata da wannan maganar oho...; Ringing biyu tayi Basma ta d'auka cikin so da shauk'in ganin kiran kasan cewar yanzu shima yana yawan kiranta sab'anin da sai dai ta kira shi,tana karawa ta saki ajiyar zuciya har yana jiyowa ya tambaye ta cewa; Ya?! M fine my boo kawai inajin dad'i ne idan naga ka kirani,nasan yanzu ina da muhimmanci a cikin ranka ko?! Ta tambaye shi tana gyara zamanta kasan cewar tana cikin hall d'in da suka gama lecture.Shafa saman sumar shi yayi ba tare da yace mata komai ba,cikin daddad'ar muryar shi yace mata; Basma we need to discuss something and it s serious please ki bani aran hankalinki nd bana son kiyi min mummunar fahimta domin komai na iya faruwa kinajina?! Duk da taji fad'uwar gaba hakan be hanata daurewa tace mai; Ok my boo inajinka,kuma zan fahimceka insha Allahu. Ok kinsan anje gidanku an nemar min auranki kuma nasan kece kika nuna da saninki aka aika har yasa aka bani ba wani jayayya.so i want to you to know.... Am.. Am, Basma you know I love you ba yadda zanyi yanzu haka ku biyu zan aura keda wata cousin d'in..... Bata bari ya k'arasa ba cikin tashin hankali wanda besan tana dashi ba yaji tana cewa; "And so what?!yareemah ni zaka wulak anta? Ka yaudareni dama tun ba yanzu ba nasan baka k aunata amma babu damuwa ni na hak ura na bar mata kaje ka aure ta yareemah I.. I.. I.. h.." Ta kasa k'arasawa kawai ta kashe wayar,sosai yaji tausayinta fiye da yadda yak i tsammani toh ya zai yi gabaki d'aya sai hankalin shi ya koma ga yadda zai yi ya koma school dan yaga Basma ya nuna mata cewar ita *SAN RAN* shi ce Meenah kuma*ZAB'IN IYAYE* ce domin sune suke son had'a su. Oh god darn it...! Yareemah Aliyu hydar ya fad'a yana dukan pillow duk duniyar tayi mai zafi ya mik'e tsaye dan neman Modu ya sanar dashi cewar gobe zasu koma ya gaji da zaman yola... Yana fita ya hangeshi shida Meenah da gid o a zaune sai b'abbaka dariya yake kai da kagani kasan labarin dariya suke bashi,kamar ya juya haka yaji amma sai ya fasa ya doshi gurin cikin takunshi na k'asaita wanda zai iya tabbatar maka da cewar lallai prince ne ba tare da an sanar dakai ba.yana zuwa suka had'a idanuwa da Modu dake rik'e da ciki saboda dariya yayi saurin d'auke kanshi cikin basarwa ya kuma damk'ar tulun gashin dake kan Meenah. Wayyo Allah nashiga uku aunty yafendo zai cire min gashin kaina..! Meenah ta fad'a tana ihu Modu ya mik'e da sauri dan k watar ta yareemah Aliyu hydar yayi saurin d'aga mishi hannu tare da cewa; yaleni guy yarinyar nan sai na koya mata hankali kafin mubar gidan nan,ba tada kunya at-all ta rainani tamkar ta tab'a ganin hak orana a waje Kuka kawai take harda su majina yareemah Aliyu hydar yace; Zaki kuma kallo na daga yau?! Meenah tayi shiru tana hawaye bata ce komai ba ya kuma jan gashin yadda zataji zafi tayi magana amma taurin kai irin na Meenah ya hana tayin magana,ganin haka ne yasa yareemah Aliyu hydar janta zuwa apartment d'insu su Bulama da gid'ad'o sai hakuri suke bashi amma kallo d'aya yayi musu suka ruga da gudu apartment d'in aunty yafendo dan su gaya mata. Modu kuwa anan ya ci gaba da zama saboda karya bisu abin ya zama rigima Allah kad'ai yasan abinda zai mata kasan cewar Meenah ta bashi labarin tsakuwar data watsa mai harda ce mai yareemah Aliyu hydar yayi kuka dan k'arya. *s*una shiga ya tura keyarta cikin parlorn sannan ya bita da kallon babu wasa sai faman zara idanuwa take tana soshe-soshe tare da turo baki tana kus-kus dashi alamar gunguni take mai abinda yafi tsana cikin rayuwar shi dan yafison ka fito fili kayi magana koda bazaka ce komai ba. Kneel down Meenah kona b'allaki a gurin nan. Share hawaye tayi batace mai komai ba sannan tak'i yin abinda ya sanyata, k'arasawa yayi inda take tsaye tayi saurin b oye fuskarta da hannunta da suka sha maroon d'in lalle suka yi mata kyau yayi kamar zai mareta cikin sauri tace mai; "Wallahi da na cewa Baffa eh zan aureka amma yanzu zanje nace mishi na fasa saboda kasheni kake nemanyi,ni dama sai da nace bakai nake so ba Yaya Modu nake so amma Baffan nan yace wani kai,toh wallahi sai na fasa dan ma kasamu na amsa. Sakin baki yayi cikin tsananin mamaki da takaicin maganar ta yace mata; "Shut up!Ni zaki cewa dan na samu kince zaki aure ni? Ok go ahead jeki fad'awa Baffan tunda baki da kunya fitsararriya sai na gyara miki zaman kwakwalwarki get the out stupid girl...! Da gudu tabar parlorn tana maijin haushin shi sai dai kafin taje apartment d'in aunty yafendo sun had'u itama ta taho,kallon su tayi kamar ba itace tagama kuka ba yanzu idanuwan fayau bako d'igwan hawaye aunty yafendo ta tambayeta; Meenah meya had'aki da Yaya Aliyu?! Ta kalli bayanta tare da maido da kallon gurin aunty yafendo tace; Ba shine d'azu ya kayar dani ba shine na watsa mai tsakuwar dana d'iba kawai yanzu muna hira da Yaya Modu yazo yajani ya kaini parlorn su,har da cewa wai zai gyara min zaman k'wak'walwata sai kace wata mahaukaciya. Tayi maganar cike da yarinta aunty yafendo ta kalleta tare da kad'a kai tana cewa; Ikon Allah! Kukuma irin taku salon soyayyar kenan?! Nifa ba shi nake so ba Yaya Modu nake so dan ma ya samu nace wa Baffa eh na yadda zan aure shi shine yake cin zalina. Meenah ta fad'a tana kallon hannun gid'ad'o dake rik'e da wata 'yar ball tana tunanin yadda zata fizge ta ruga da ita. Cikin sa'a kuwa tayi wuf ta ansa tare da kwasawa a guje tamkar iska zata kayar da ita aunty yafendo ta bita da kallo tare da girgiza kai tana fad'in. Allah ya shirya min ku amin. Da haka ta wuce gurin aunty Maijidda kasancewar dama tana da niyar zuwa sai kuma akazo aka sanar mata cewar yareemah Aliyu hydar ya shak'i Meenah..... Team#BASMAH AUR MEENAH? WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!*