Sashe 78
Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
matar ko kin manta?! Ta kuma ware idanuwa cikin sarkewar murya tace, Toh bari na gayawa Ammi. Jin abinda ta ce ne yasa shi saurin cewa, No barshima kawai na fasa ya hidima?! Taji ya fad'a cikin basarwa,a hankali tace, An gama komai sai zuwa dare za'ayi wushe wushe Dinner sai a... Tayi shiru ta kasa k'arasawa sabida kunya,shine da kanshi ya k'arasa mata abinda take son fad'a tayi shiru yace, Sai a kawo ki ko?! Wani shirun ta kuma yi shi kuma yayi dariya tare da cewa, Bye-bye sai an kawokin yau sai na zane ki tunda ina miki magana kina min shiru. Kit taji ya katse tabi screen d'in da kallo,turo baki tayi sannan ta k'arasa inda Modu yake ta mik'a mai wayar shi ita kuma ta koma inda ta tashi ta zauna,nan aka cigaba da hira ana wasa da dariya har Yaya gumsu tazo taja Meenah dan zuwa a sake kamsasata da gyarata. *** Babagana kuwa tunda yaje gidan su billy be samu fuskar ganinta ba yasan ta tonamai asiri yayi kukan yayi magiyar akan subarshi ya ganta amma ita kanta billyn taki yadda har yau da aketa shagalin biki kowa yana murna amma shi ko fitowa beyi daga apartment d'inshi ba. Ammi ce taga sam tunda tazo bata sashi a idanunshi ba shida matarshi dan haka yanzu ta nufi apartment d'in nashi da nufin bashi hakuri ko wani abun suka yi mishi basu sani ba haka ta dinga wuce mutane ana mika mata gaisuwa tare da fatan sanya alkairi a cikin taron bikin har ta karasa cikin apartment d'in dogarawan shi suka gaida ita sannan ta tambayesu ko yana nan suka ce mata eh dan haka ta shiga tare da sallama. Tsit cikin parlon hakan yasa ta kuma yin sallama tana kallon yanayin gurin karaf ta hangeshi kwance k'asan carpet yayi ruf da ciki yana sauke numfashi da kyar,da sauri ta k'arasa kusa dashi tana salati ta riko hannunshi mai rik'e da tabar wiwi wadda duk gata nan ansha an yar da k'asan wajan kwali biyu Ammi cikin tashin hankali tace, Subhanallahi yareemah mezan gani haka?ina matarka bilkisu har kake wannan abun...?! Yana jin abinda ta fad'a ya rushe da kuka tare da sake makalo hannunta cikin nashi,ganin haka yasa tayi saurin ciro wayarta ta kira maimurabus yace gashi nan zuwa,sake kallon shi tayi cikin tausayawa duk da batasan matsalar shiba tace, Ina bilkisu babagana..?! Ya mik'e zaune da kyar tamkar wanda yayi jinya yace mata, Ammi billy na ta gudu ta gujeni,Ammi dama ace kece kika haifeni ba Mami ba nayi nadamar kasan cewa tsatsonta wallahi da ace 'ya'ya na tsinewa iyayansu ko da tuni na tsinewa Ma.... Ammi tayi saurin rufe mai baki tana rintsa idanuwa dai-dai lokacin maimartaba ya karasaso cikin parlorn,abin da ya ganine a zube a d'akin ya k'ara d'aga mai hankali sannan ya kalli babagana cikin takaici yace, Yanzu wannan kayan da kasha sune suka sanyaka jin relief? Tur da wannan d'abi'ar taka na sani ko a gaban Allah za iya tsayawa akan tabbatar da cewar na baka tarbiya da ilimin addini dana zamani sai dai kai din bakayi amfani da suba yau da ace kaikad'aine d'ana na tabbatar da yanzu idan ban mutu da bakin cikin kaba toh ina kwance bana moruwa sabida bakin cikinka,amma yanzu Alhamdulillahi inada masu sharemin hawayena kai kuma Allah ya shiryeka gashi son mace yana neman haukataka. Ammi ta kalli babagana sannan ta kalli mijin nata cikin sanyin murya da kwantar da kai ta ce, A'a rankashi dad'e kayi hakuri ka gafarta mai sannan ka zauna muji matsakar shi na sani kaid'in mai saurin afuwane. Kujera ya janyo ya zauna tare da kallon Ammi yace, Nasan ke baki son me yake faruwa ba amma ni nasani kuma macace ta maida shi haka shine yazo yana shan kayan maye sabida hauka. Anan ya sanar mata da abinda ya sani yareemah babagana ya kalleshi cikin bugun zuciya yace, Baba na kayi hakuri ka yafemin,hakika kamar yadda kace da bakada 'ya'ya da yanzu na nakasa ka toh hakama da bakada Ammi da tuni sauran matan sun nakasaka domin su Mami ba mata bane na gari duk da cewar akwai mahaifiyata a ciki amma hakan bazai hana na yabi Ammi ba,wayyo Allah na ina ma ace ta tsatsonta na fito da yanzu nima ina cikin 'ya'yan da zakayi alfahari dasu, Kayi hakuri baba ka gafarce ni sannan kayi min exchange d'in uwa domin Mami ba uwar da mutum zai nuna bace yana kuri tana alfahari da nagartarta ba,Mami ta cuceni ta cuceka baba sannan cutarwarta duk akan Ammi ne please baba ka gafarta min ka yafemin don gaf nake da rasa rayuwata tunda har na rasa billy.. Ya k'arasa maganar cikin fashewa da wani irin kuka Ammi tayi ta lallashinsa yayin da maimartaba yayi shiru yana son ya gano inda maganar babaganan ta nufa inda yace anfi cutar da hajjagana yana son gano shin tayaya kuma akan mene sai dai baya son tambayar shi dan karya gaya mai abinda zai k'ara d'aga mai hankali, suna nan zaune Ammi na tayi mai nasiha su hajja gajiram da yakolo suka shigo fuskarnan tasu a had'e ba kamarta hajja gajiram cikin isa da tak'amar cewar d'anta ne tace, Mezan gani haka banda tsabar cin mutunci ina gidan yarona bashida lafiya a kasa sanar min sai kishin-kishin danaji?ashe kuna nan ku kuma?! Mami ya haka?! Ban sani sabida banida kima a wajanka shine ka kasa aikamin cewar bakajin dad'i sai su zaka aika mawa...?! Babagana ya kalleta cikin takaici sannan ya kalli mahaifinnashi yace, Ka gani ko baba?wallahi na tabbatar da ace Ammi zataje tagansu a lokacin da baah Ngari na kwance ta gansu a kusa dashi godiya zatayi musu koda kuwa da nufin cutarwa sukaje,amma yanzu ni dubi bani nakira Ammi ba jitayi bata ganniba yasa tazo amma ita da take ikirarin cewar ta haifeni bata zoba tun lokacin da muka samu rabuwar kai tsakanina da matata sai yanzu dataji labarin kuna nan. Da mamaki hajja gajiram ta kalleshi shima itan yake kallo sannan tace, Ni kake gayawa haka yareemah?! Shiru yayi mata maimartaba ya mik'e tsaye tare da cewa, Allah ya baka lafiya ya kuma shiryaka duniya da lahira, ke kuma tashi kije kinbar mutane baki a can.. Daga haka suka zagaye su suka fita,shima babagana bedroom ya wuce yana wani layi tamkar hajijiya zata kayardashi yayin da aka bar hajja yakolo da ita cikin tsananin mamaki kafin suma su juya su fita zuciyar hajja gajiram cikin tsananin damuwa da takaici tare da d'aura aniyar wannan karon da kanta zataje gurin boka dan ayi mata maganin hajjagana. Bayan sallar isha aka shiga shirya amarya Meenah Cikin wani tsadadden uban su lace ne ajikinta Black me torches golden,komi na jikanta gold ne har anklet(sarkar kafa)na k afarta da bular hancinta duk gold abu tasa,sarkar wuyanta ma abun kallo ce me kwandalelen kambun gold a tsakiya,har kanta seda aka mata kwalliya da gold yayi d as akan kela yasken(kitson gaba)kanta ga had addiyar Arabian laffayarta da aunty yaruwaiya tashiga nad a mata abinde se wanda yagani kawai... Mamza beauty ce itace taiwa Meenah kwalliya da kawayenta gaba d aya photographers su mai gaskiya da Georgeokoro se snapping Meenah suke wanda se murmushi take abunta kamar yadda aunty yaruwaiya tace tadingayi... Dangosho ne pusher pink and black kawayen Amarya sukai se mandil mayafi kamar yadda al adar take,yan uwa kuwa blue dangasho sukasa kowanne da kela yaske.. Taf shehuri tacika da manyan mutane da abokan arziki kai dama yan gayyar sodi dake san ganin kwakwaf,yadda kasan rana haka masarautar Ke tashi koina da dal da dal d in fitulu ne... Kowa ya hallarci taron duk koda card admits one,Fulani night din da akai a damboa road shima yahadu over amma wushe wushen yafi haduwa saboda anfi bashi muhimmanci tunda abin al dane da yaxama dole ayi shi... Motoci a tawaga sune suka fara tafiya harabar da xa ai event din daya sha kwalliya cikin gold and black abinde se sam barka Banda kamshin aroma na abincin kanuri su dangin kisre da brabusko kai harda kunun mard om shima ba a barshi a baya ba gefe d aya kuma local dishes ne na hausa se international dishes wanda suma aka dakkosu na musanman don manyan da suka halarta.. Taro ne daya kun shi governors wives diplomats,ministers,matayen sarakuna da kuma manyan malamai da attajirai da ma yan kasuwa ciki harda abokanan arziki da ba a barsu abaya ba.. Se bayan kowa yashiga mc tai announcing shigowar Amarya Meenah wadda tashigo da friends nata dakebin taken gangaa kura kowanensu yasha kitson gaba abinde se sam barka kawai... Su astuto_Nina best frnd sune agaba gefen amarya kuma miss pinki ce ta bayanta kuwa Nabeelah ce da dota billy s fari su Humayrah da summaya da rukynamango se watsa hannuwa ake anabin wajar ganga kuraa.. Bayanta kuwa yan uwa ne su aunty yaruwaiya da su aysah da sauran step sisters na sarki aliyu Hydar ,can k arshe kuwa su Yaya gumsu ne da gidado dayai burning face shima yana bin tawagar amaryar sanye suke wasunsu cikin dangashe,jene klabe da kuguna karibe.. Tuni aka fara xubawa makadan gangaa kura yirne,waje kuwa jin kida yana tashi yasa aka fara sakin al adar durum kageye,su kaka deeja kuwa se bada ngaya ka ajiye suke(turare wuta)... Meenah na dosar tsakiyar fili aka canxa waka xuwa na shuwas wato dangin aunty maijiddah mahaifiyarta wakokin khamal yaqub/mansur ne ke ta tashi dana Amina rawaram.. Meenah na xama aka fara gudanar da al ada saboda sarki Aliyu Hydar baxe samu damar halarta ba komi anmata shi itade se k aro murmushi kawai take, Anci ansha ankuma gyatse can na hango yan home of novels suna lafta loma idanuwa hudu mukai da rano dake saye kisre tana dannawa a nursing bag d in affan girgiza kai kawai nai don tasaba,mama arfat ce a gefanta d auke da arfatu a cinya tanata dannawa cikinta kunun mard om..gefanta kuwa my billyn abdul ce banda lodawa cikinta fried rice ba abinda take.. Dariata na gimtse ganin mom Heena da maryam umar suna yagar cowleg Dankari na fada a fili can na hango su aysha hamxa anata snapping plate din abinci tana uploading a Instagram nashiga uku nace ganin yan