← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 107

Sashe 104

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaskia ne ina xaka koma Peaceful environment may be kasar ma xanbari I dunno saboda banyi deciding ba de tukun.. cewar Modu Sannan ya mike hade da sakala earpiece din Aliyu a kunnensa.. Guy..ya da haka?! cewar Aliyu Hydar Yup nima nakoya irin arrogant halinka plus I don t have your time abeg cewar Modu sannan yabar garden din Murmushi kawai Aliyu Hydar yai hade da kamo kasan lips d insa yana taunewa,mikewa yai hannuwansa zube cikin aljihunsa ciro wayarsa yai daga aljihu ya kira Basman a awaya kasancewar a sashenta yake basu wani jima suna waya ba yakashe yai site din Meenah.. Da dare aka had a liyafa ta yan uwa da abokanan arziki dukdan taya sarki Ngari shehu hawa karagar mulkin jihar Bornu,anci ansha angyatse,matar sarki Ngari usman wato Gimbiya Asmy Bunami tayi kyau itama ba karya sanye cikin wani dandatsetsan Royal lace blue da laffaya pusher pink hakama su Meenah da matan Modu duk ankon lace suma sukai abinde se sam barka kawai,duk inda Meenah tai se Aliyu ya kalleta da k yar yake iya dedeta kansa yana dan dannewa don ba karamin kyau tayiba musanman yanzun da dan cikinta yadago kadan dayake doguwa ce ba a ganewa ma sosai,Basma dake gefensa dakewa kawai take tana sanyawa zuciyarta salama tareda kauda duk wani rudi da shedan yake kissaya mata akansu tunda yanxun tagane laifinta ne tun farko idanuwanta sun rufe tabi sharrin shaidan ta aikata ba dede ba gashi yanzun ta girbi abunda ta shuka abaya musanman rashin samun haihuwa dabatayi tayi gwaje gwajen harta gaji maganar de dayace mahaifarta s weak ko tasamu ciki se andaure bakin mahaifar tukun... <<<<>>>>> Shiga cikin d'akin da yake a matsayin nata yayi ya hangeta kwance tana bawa Hassana nono har bacci ya fara d'a ukarta ya lallab'a yaje ya zare yarinyar daga jikin nonon ya matsar da ita shi kuma ya maye gurbin ya kamo yana wasa dashi,Billy kuwa cikin bacci taji salon shan ya canza dan ji tayi jikinta ya fara yin wani iri hakan yasa ta saurin bud'e ido kawai taga k'aton mutum a wajan da sauri ta bud'e baki zata kurma ihu yareemah babagana yayi saurin toshe mata shi da hannunshi yana mai kallon kofar dan kar Umma ta shigo. Kiciniyar kwatar kanta ta farayi amma ya hana sai ma kwanciya yayi a saman cikin ta yana kallonta idanunta sai juyawa suke sabida tsabar tsoro da tashin hankali. My precious na gaji wallahi kin wahalar dani ina azabtuwa please ki barni ko bazan yi komai ba naji d'umin jikinki please... Billy ta hau girgiza mai kai alamar a'a ya d'agata amma yak'i,yana toshe da bakinta yayin da d'aya hannun yake shafar jikinta nan da nan abinka da lafiyayyar mace ta fara d'aukar sakon jikinta ya mutu tsigar jikinta ya fara tashi ganin haka yasa babagana zare hannunshi daga kan bakinta ya sanya nashi yana tsosa ta lumshe ido a hankali tana taya shi ba tare da tasan hakan na faruwa ba. Tsawon lokaci suka d'auka a haka kafin Billy tayi karfin halin tureshi daga jikinta sai hawaye shi kuma duk jikinshi yayi wani sanyi wata muguwar buk'atarta na taso mai sai faman had'iyar yawu yake cikin b'acin rai yaji tana cewa. Me yasa kake min haka ne duk kabi ka takura min?nasan bani kake so ba jikina kake so dan haka kuma ni bani ba kai ka fita a harkata wallahi tallahi ana dole ne?! Babagana yaji tamkar ya fashe da kuka,me zai mata har ta gano yadda soyayyarta tayi mai muguwar illah a cikin zuciyarshi,yana ganin k'iyayyar shi sosai a cikin idanunta gashi ko zuwa yayi tayi mai rashin mutunci toh bazai hakura ba sai ya dawo sabida yana son ta soyayyar tata har tayi masa mugun kamu. Tashi yayi yana gyara riga kallonta yayi sannan ya d'auki Husaina mai sunan Ammi ya kalleta itama shi take kallo da mamaki yayi murmushin sa mai k'ara k'awata zuciyar 'yan mata akan kaunarshi yace mata. Ai 'ya'ya dai nawane ko?toh na hakura ki rik'e d'aya ke d'ayan ma na fasa badawa. Ya fad'a tare da d'auke Hassanar ma sannan ya juya yana cewa, Sune suka had'a mu toh kin dena ganina sai anjima. Yana fad'a yayi ficewar shi dasu ai kuwa ta biyo shi da gudu sukayi kicibis da Umma tace, Ke lafiyar ki kuwa....?! Umma ya d'auke min su na shiga uku ya tafi dasu Umma wai ya rabamu wallahi bazan yadda ba sai ya bani su. Kokafin su fita ya tada mota yabar k'ofar gidan dan haka da saurin Umma tayiwa Abba waya nan ta sanar mai yayi dariya cikin ranshi yana hango rashin wayon mata yace su bari ya dawo.Billy ta zauna sai kuka takeyi har bayan magrib lokacin abba ya dawo yana shiga Umma ta tare shi da tambaya abba yace. Wallahi in gaya miki yaron nan ya hanasu yama kullesu yace babu wanda zai bawa. Abba ya fad'a yayinda Billy ta koma tad'aki dama sauran kwana biyu tayi arba'in abba da Umma suna tsaye sai ga billy cikin hijjab tana kuka ta cewa abba. Abba tunda bazai dawo dasu ba gara ni na koma wallahi bazan barmai su ba haka kurum ya koya musu banzar d'abi'a. Umma tayi sakato da baki yayin da abba yayi dariya "lallai dabarar babagana tayi tasiri." Amma a fili ya yace, Bilkisu rabu dashi ki kyale mai anjima zanje na karb'o miki takardar sakinki kuma dole ya bayar. Abba zan koma wallahi bazan barmai yaran nan ba ai ni na haifi abuna. Toh bilkisu ai yafimu iko akan su sai dai da zamu kai k'ara toh ke za'a bawa su tunda nono suke sha sai ace idan sun girma sun d'an tasa sai a mayar dasu wajan shi haka musulinci yace amma idan muka kai kara bilkisu ba saurarar mu za'ayi ba sabida matsayin Mu ba d'aya bane sun fimu ta ko'ina. Na shiga uku abba toh zan koma gidan ni dai gurin 'ya'yan wallahi ni bazan barsu ba. Shikenan toh ai ba komai abin ma yazo da sauki tunda dama har yanzu ke Matar shice kuma suma yaran zasuji dad'i idan suka ga iyayan su atare sai ku had'u kuyi rainansu cikin mutunci. Umma ta hau fad'a abba ya nuna mata rashin dacewar abinda take yi dan haka da kanshi ya d'auketa ya kaita shehuri sai da suka fara zuwa wajan shehu bulama sannan ya kira su Ammi dashi babaganar yazo kuwa da yaran a cikin baby bag ta goyo d'aya a cikinshi d'aya a bayanshi shehu bulama ya sassanta su Billy nata kuka sannan su Ammi suka rakasu apartment d'insu babagana sai murna yake farin ciki fal zuciyar shi da haka abba ya koma gida sai dai Umma fushi take sai da yayi lallashi da nuna mata illar abinda rabuwar zata janyo sannan suka shirya dama domin ya hango abinda ta kasa hangowa tuntuni. <<<<>>>>> Zaune take a cikin d'aki ta gama cin uban kukanta wanda ya zame mata tamkar ibadah,k aton cikinta ta shafa wanda yake niyar fitowa da kanshi kasan cewar haihuwarta yau ko gobe ne dan babu inda take fita koda harabar cikin shehurin ne baba ya hana sai dai akai mata komai duk abinda take so. Astagfurullah ya Allah ka yafe min, wannan abun kunyar idan ya fito bansan yadda zanyi ba,Allah ka d'auke shi ko ka d'auke ni bansan idan ya girma ko ta girma me zan ce ba game da yadda nayi na sameshi, na shiga uku wayyo ni ya zanyi...?! Falmata ta fad'a cikin kuka mai had'e da majina,gyara zama tayi da kyar ta kalli baiwarta dake hidimta mata tace, Please kirawo min Ammi kice dan Allah. Tayi maganar kamar zata yi kuka,tashi baiwar tayi ta fita zuwa apartment d'in Ammin suka hud'u itama zata fito nan ta sanar mata suka tafi tare.suna zuwa suka tarar ta fara zubar da jini ta kwanta kan cikin Ammi ta k'arasa cikin tashin hankali suka d'agota, da sauri Ammi tasa aka d'auketa sai asibitin cikin shehurin. Ana zuwa aka sanar dasu cewar sai an k'ara mata jini ana kokarin gwada na cikin asibitin sai ga yareemah Aliyu hydar da Modu sun k'araso ana gaya musu Modu yace a gwada nashi amma sam beyi ba ganin haka yasa Aliyu hydar yin kundunbalan cewa shima a gwada shi cikin ikon Allah kuwa yayi dai-dai aka d'iba aka sanya mata, gani likitocin sukayi babyn na cikin mawuyacin hali hakan yasa aka ce sai anyi mata c.s a take Modu ya sanya hannu tunda ba miji gareta ba bare ya sanya,wanda yayi cikin kuma ya gudu. Tun kafin ma a fara aikin suka gano cewar babyn baya numfashi dan haka yi kawai aka yi aka cire mata shi gashi fari kal kato dashi komai na hallita ya fito mai idanunshi ne kawai basu gama yi ba su Modu suka karb'e shi aka kaishi gurin maimartaba yayi mai hudu ba sannan aka yi mai wanka akaje aka rufeshi. Falmata bata farka ba sai k'arfe biyar na yamma,cikinta ta fara kallo taga wayam tayi saurin kallon d'akin babu kowa sai wata baiwa dake tsaye a gefenta ta kalleta tace. Na haihu ne...?! Eh rankishi dad'e Allah yayi. Innalillahi wa'innailaihir rajiun yanzu na haihu ina d'an ko nace 'yar?! Tayi maganar tana kuka sai mararta da taji tai wani iri ta shafo gurin tare da zaro ido tace, Meye wannan?! Kafin baiwar ta bata amsa su Ammi suka shigo tare da Basmah dasu aunty yaruwaiya falmata tayi saurin kallon Ammi tare da cewa, Ammi ashe na haihu wayyo Allah na shiga uku. Ke ya haka ne Falmata?sai kace ba musulma ba keda zaki godewa Allah kuma. Ammi na godewa Allah fa kikace, wallahi shi kanshi kunyarshi da tsoranshi nakeji bare nayi godiya,na shiga uku yanzu me na haifa?! Namiji ne amma Allah ya karb'i abinshi. Aunty yaruwaiya ta fad'a sai ga falmata tana hawayen dad'i cikin murna tace. Alhamdulillah Allah na gode maka. Ammi ta saki baki tana kallonta yayin da Basmah ta fara hawaye ganin ita neman haihuwar take yau ga wata tayi ya mutu tana murna ikon Allah kenan kowa a duniya da abinda ya dameshi, kwanaki uku tayi a asibitin Ammi na kulawa da ita kafin aka sallameta taje ta kuma bawa baba hakuri yace
Chapter 104 · 0% Book details