← Book details Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 107

Sashe 14

Son Rai Ko Zab'in Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

(A STUNNING LOVE STORY)
NA
NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
_20_
This page is urs SEEMBY LUFF
I love you beyond words
Allah ya k'ara basira acigaba da suburbud'o mana SAHR_KHULAYD
.....
WASHEGARI;
Federal capital territory(Abuja).....
Ganges street maitama Abuja.
Modu indimi ne kwance idanuwansa a lumshe da misalin k'arfe takwas na dare da alama bai dad'e da isowa daga tafiyar dayaiba gefensa d'an k'aramin trolly ne bak'i wanda xe iyacin kaya kala biyu kawai,kwance yake akan royal kujerun dake parlorn side table d'in dake gefan 3 sitter kujerar dayake take away ne me d'auke da tambarin tulip bistro se lemon don simon na kwali da ruwan gorar nestle wayarshi ce tafara ringing jin sautin taken 'ganga kuraa' yaganar dashi mai martaba ne don shi kad'ai yasanyawa ringing d'in saboda yadinga fayyace kiransa akodayaushe akuma ko'ina yake. Hanxarin d'auka yai yana mik'ewa daga kwancen dayake;
"Assalamu alykm... Na'am baba! Eh ina cikin gidan yanzu haka,eh bandad'e da shigowa ba... To to Shikenan baba bakomai seka k'araso Allah yadawo dakai lapia,nabarka lapia.''katse wayar yai ya ajiye gefe tareda komawa yasake kwanciya a kan kujerar dayake
Ko'ina na cikin parlorn agayre yake tatas,don kullum akwai ma'aikatan dake gyarashi saboda mai martaba anan yake sauka idan yaje Abujan,makaken parlor ne me d'auke da kujerun Royal har set biyu kowanne da kalarsa,haka curtains d'in parlorn kalar kujerun ne,makekiyar tv ce had'e da set d'in kallo a jikin bango,gefe guda kuma dinning table ne mecin mutane 6 shima k'irar Royal... Modu indimi har bacci yafara d'aukarsa yajiyo karakainan shamakin mai martaba yana isar da isowarsa kafin ya mik'e yatashi har mai martaba yashigo cikin parlorn,da sauri modu ya mik'e yana rufe bakinsa saboda hammar dayai shamakin mai martaba ne yafice yabasu waje shikuma modu ya durk'usa yana gayda mai martaban amsawa mai martaban yai tareda fad'in;
"Jeka samu hutu Modu Idan Allah ya ara mana ran ganin gobe cikin k'oshin lapia xamu tattauna da safe da izininsa Insha Allah.."
"To Allah yakymu baba Nagode Allah yatashemu lapia.. Ahuta lapia nabarka lapia"yak'arashe xancen had'e da d'an rissinawa sannan ya mik'e yasauka k'asa wani d'aki da aka tanadar masu gefan corridor duk sanda sukazo Abujan anan suke sauka.
...Da safe da misalin k'arfe 10 da rabi na safiya Modu yatashi daga bacci bayan komawar dayai daga sallar subhi,cikin sauri yai hanxarin shiga band'aki wanka yayi had'e da d'auro alwala yajima yana shafe shafen kayan k'amshinsa don abune daya xama wajib d'insu shida yareemah Aliyu Hydar ta b'angaren k'amshi sede ayi hamdalah kawai don har yareemah Aliyu Hydar yafi Modu son turaruka da kuma tuttulasu ajikinsa kamar ruwa..yajima yana aikin shafa wancen goga wancan kamar wanda xashi gasar xab'en wanda yafi kowa k'amshi,yana gamawa yaxura kayansa wannan karon wanka shadda yai dark blue anmata aikin light blue 'zanna bukhr'hula ya d'ora light bak'aramin kyau yayiba sosai,safa yasaka bak'a had'e da xura takalminsa samfarin vassace,shi kansa tsayawa yai yana kallon kansa a mudubi kunsan modun naku da d'an rawar kai,yakashe selfies harda mirror selfie sannan yad'akko sallaya ya shimfida yagabatar da sallar walha kamar yadda ya sabayi kullum addu'oinsa yai yashafa had'e da ninke sallayar ya mayar kan drawer cikin hanxari yafito yahau sama gurin Mai martaba don rabonsa dashi tunda asubah da suka gabatar da sallah,yana hawa ya hango mai martaban sanye cikin kayan sarakai kalar d'orawa yayi kyau sosai sede afurta kalmar tubarkAllah kawai,gaisawa suka k'arayi sannan mai Martaba yai gyaren murya cikin nutsuwa yafara magana;
"To Modu abinda yasa nace kazo Abuja mu tattauna yakashi kashi biyu,d'aya saboda taron da zamuyine ajiyan amma almuhim abinda yasa nazo Abuja saboda mu tattauna ne donta taro xan iya turo waziri ya wakilceni ina fatan ka fahimta?!"
"K'warai baba nagane.."
"To Masha Allahu.."abinda Mai martaba yace kenan atak'aice..
Gyara xaman gurfanensa yai yashiga fad'awa mai martaba komai akan binciken dayai ba'abinda ya b'oye masa,yak'arashe da;
"Kuma bayan ganinsu danai da idanuwana da temakon k'arin bayani da k'anwar abokina tai wallahi baba har wani abokina nasake bugar cikinsa don kauda zargi to amma dukde abinda suke fad'amin guda d'ayane kamar yadda nace da farko baba"Modu indimi yak'arasa xancen had'e da saukar da kansa k'asa
Ran mai martaba idan yayi dubu yab'aci,gashi da manyan idanuwana tubarkAllah sesuka sake fitowa saboda tsabar b'acin rai,mik'ewa yai tsaye yana magana cikeda b'acin rai;
"Zancen banza zancen wofi,dama irin yarinyar dayake kulawa kenan shysa yace min basu gama daidaitawa ba?!"
"Kayi hak'uri baba nide inada tabbacin cewa wallahi besan haka halayyarta takeba kuma kamar yadda nace d'in ance k'awar tatace take cusa mata wa'innan miyagun halayen"
"Duk naji naji magana d'ayace baxe aureta ba tunda ba y'ar mutunci bace Allah xe bashi wadda tafita ko yanada wacce yakeso bayan ita?.."
Kad'a kai kawai Modu yai alamar a'a k'asan xuciyarsa kuwa cike take da dana sanin fad'ar dayai ganin yadda mai martaban yai saurin yanke hukunci lokaci d'aya betab'a kawowa haka abin xe xama ba...
"To niyanxu xankoma Bornu base gobe ba,kai kagama project d'inne mutafi tare?!"
"A'a baba ban k'arasaba tukun"
"To Allah yatemaka"
"Ameen baba"
Sallama Mai Martaba sukai da Modu yahau pj d'insa yakoma Bornu,shikuma Modu se washegari xe hau jirgin safe yakoma school, da daddare a dunes mall yai having supper sannan yakoma gidah,wanka kawai yai yasa kayan baccinsa lokaci lokaci yake sakin tsaki kwata kwata hankalinsa baya kan Laliga ball da ake tsakanin RealMadrid da sociedad dake nunawa a tv daga k'arshe ma mik'ewa yai tsaye yana faman xagaye parlorn yana magana shi kad'ai;
"What if Aliyu yagano nine wanda na gudanar da binciken?! Oh ya Allah! Kawankeni acikin wannan ruguntsumi me wuyar sha'ani dake shirin faruwa..."haka Modu yaita sumbatu shi kad'ai kamar zaucacce yanayi yana tsaki harde bacci b'arawo yasaceshi,atak'aice de akan kujerar dayake mitar akai ya kwana....

HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of expert and prefect writers)
SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!
Chapter 14 · 0% Book details