← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 99

Sashe 94

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin
arfin hali Sumayya tayi tare da cewa
"Kun fito?"
Muhdeen dai bai bi ta kanta ba ya nufi
akinsa, yayin da Sumayya ta cigaba da cewa
"Ance ka girmama ba
onka, amma ni naga kamar bakiyi farin ciki da zuwa na ba ko? shikenan bari na tashi na bar maki gidanki."
ewa tasaye tayi tare da kallon Inteesar, har ta kai ba
ofa Inteesar tayi saurin binta ta ri
e hannunta tare da cewa
"Kiyi ha
uri Aunty Sumayya ba haka bane, mamaki ne ya hana ni magana"
"Mamakin me kike yi?"
arasa maganar da sakarwa Inteesar murmushi, itama martani murmushi ta maida mata ta janyo hannunta ta ce,
"Dawo ki zauna Aunty Sumayya nan ma ai gidanki na"
Zama sukayi ta kalli Sumayya da ke murmushi ta ce,
"Ina wuni Aunty Sumayya?"
"Lafiya lau
anwata ya kike ya amarci?"
Sunkuyar da kanta kawai tayi tana murmushi, yayinda Sumayya ke wata mata harara ji take kamar ta sha
eta ta mutu.

Ganin Inteesar ta
ago da fuskarta ne yasa ta yi saurin sakin murmushi
"Kunga ki saki jikinki da Ni kinji? ki
auke ni a matsayin ya a gare ki, ki mance da abubuwan da na maki a baya, nayi nadama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, ko makamancinsa ma na
auke ki tamkar
anwa ta da muke uwa
aya uba
aya da ita, haka nake so nima ki
auke ni, kinsan ba iya girki ba kuma mijinki baya son na masu aiki, saboda haka na yanke shawarar idan ba zaki damu ba zan dinga zuwa kina koya mani girki na tsawo sati
aya."
Kallonta Inteesar tayi tana tunani kafin ta ce
"Bakomai"
Kin amincewa shawara ta?"
Kai ta girgiza alamar amincewa ta ce
"Na amince bari na sanar da yaya."
Daga nan ta mi
e ta nufi
akinsa, ya gama shirinsa zai fita, murmushi ya sakar mata tare da cewa
"Nazo na tayaki girkin ne?"
arasa maganar yana murmushi
"Ka barshi kawai ba aikinka bane, zamu shiga kitchen yanzun tare da Aunty Sumayya."
Take fara'ar fysakarsa ya
auke ya ce,
"Kinga kada da
in bakinta ya ru
e ki, Sumayya tafi
arfin ki ta wuce sanin tunaninki, nasan wace ce ita haka nan awai ba zata zo gidan nan da sunan ki koya mata girki ba, domin yadda masana da jinkai hakan zai zama kamar
anci ne a wurinta, matu
ar ta ajiye jin kanta da ta
amarta yazo gare ki da sunan koyon wani abu to ki tabbata da biyu tayi hakan, akwai dalili da kuma wani buri da take da shi akanki, ki bita a sannu dan ta fiki wayo da dabara kina da saurin yarda da mutane hakan zai bata damar samun abinda take so daga gare ki cikin sau
i, shiyasa kika ji na ce ban amince da ita ba, ni kaina zanso zaman lafiya da ha
in kai da junanku, amma tunda na ce maki a'a akwai abunda na hango."
Murmushi tayi tare da cewa
"Ta nuna mani nadamarta naga sauyi a tattare da ita, bazan shige mata ba sai dai bazan iya
in amincewa da alfarmar da tazo nema daga gare ni ba."
Jinjina kai yayi tare da cewa
"Shikenan Allah ya ya ka
e fitina a tsakanin ku ya ha
a kanku."
Murmushi tayi tare da cewa
"Ameen ya rabbil izzati"
Tare suka fito daga bedroom
in, suka tarar da Sumayya a falo, zama yayi a akan kujerar da ke kusa da Sumayya, ido ya zuba mata dan haka kawai bai yarda ba abinda ta zo da shi ba , dan yasan halinta sarai, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta ce,
"Wai Baby naga kamar baka so zuwa na gidan nan ba, ko baka son kaga kan matanka ya ha
u ne?"
Murmushi yayi wanda iya fatan bakinsa ya tsaya
"Idan akwai wanda zai so ha
in kanku da zaman lafiyarku a baya na yake, domin zaman lafiyarku shine kwanciyar hanakali na."
"To me yasa naga yanayinka ya canza?"
.Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Sumayya Inteesar
aramar yarinya ce a gare ki, dan Allah ki ri
e ta amana da zuciya
aya, bata da matsala idan kika kama girmaniki nasan zata maki biyayya, ke kanaki shaida ce akan biyayyar ta
an zaman da kuka yi da ita, ki
auke ta
anwa ba kishiya ba ki ri
e girmaniki a matsayinki na babba."
Juyawa yayi ya kalli Inteesar tare da cewa
"Inteesar Sumayya ba tsararki bace ta girme ki a shekaru da kuma gidan aure, ki bata girmanta a matsayinta na babba a gare ki, bana son raini ya shiga tsakaninki da ita, kuyi ha
uri da junanku banda
aukar zuga, duk wacce ta batawa 'yar uwarta rai kata ce zatayi fa
a da ita, ta same ta ta sanar da ita abinda tayi mata wanda bata ji da
insa ba su fahimci juna, Allah ya ha
a kanku."
Amsawa sukayi da Ameen, daga nan ya tashi ya nufi masallaci, Inteesar ta kalli Sumayya tare da cewa
"Aunty duk da rana tayi bari na dafa mana ko Taliya ce ko?"
Murmushi tayi tare da bin bayanta tana cewa
"Muje muyi tare na fara koya tun yanzun ."
Tare suka shiga kitchen
in Inteesar na mata bayanin yadda ake komai, tana kuma yi a akace yadda zata gane, wani abun ma da kanta zata kar
a ta zuba, a haka har suka girka jallop
in taliya da yaji kayan lambu da busashshen kifi.

Jin an tada sallah ne ya sa Inteesar cewa
"Aunty bari naje nayi sallah ko?"
Kai Sumayya ta jinjina tana murmushi ta ce,
"To sai kin fito nima na je nayi"
Inteesar ce ya fita daga kitchen
in ta nufi
alibta dan yin sallah,tana fita Sumayya ta bita da harara tare da yin tsuki.

Bayan Inteesar ta shiga
auki ne ta fa
a toilet bayan ta
an gyara zanin gadon da ya yamutshe, ta kauda komai.

Alwala ta
auro yazo ta gabatar da sallar azahar, bayan ta idar tare da yin addu'a sannan ta bar salllayar a wajen tare da ajiye hijabin akan sallayar dan Sumayya idan tazo tayi amfani da shi, dan ba da hijab tazo gidan ba.

Bayan ta fita ne ta samu Sumayya a falo tana zaune a kujera.

"Aunty na idar kije kiyi sallar sai muci abinci ko?"
Jinjina kai tayi
"Okay to"
ewa tayi ta nufi
akin Inteesar dan yin sallah, dan da ba don da Inteesar ta ce tayi sallar ba ba yi zata yi ba, sai da ta tsaya ta na
arewa
akin kallo yadda aka tsara shi, gwanin sha'awa, komai tsaf a mahallin da ya dace, ta
a baki tayi ta nufi toilet
Muhdeen ne ya turo
ofar falo ya shigo tare da sallama, Inteesar dake zaune a falo ya amsa masa sallamar,
arasowa yayi tare da zama gefenta ya ri
on hannunta cikin nasa .

"Ina Auntynki take?

"Ta shiga tayi sallah, bari ta fito sai muci abinci."
Yana rufe baki sai ga Sumayya ta fito daga
akin Inteesar, idanunta ne suka sauka akan hannun Muhdeen dake sar
e a cikin na Inteesar, kauda kanta tayi gefe, Inteesar tayi
arin zame nata amma sai ya sake ri
e hannun da kyau kallon sa tayi ya
aga mata gira
aya kauda kanta gefe tayi tare da mi
ewa tsaye ta ce,
"Muje Aunty dame ke nake jira."
Jin hakan yasa Sumayya tayi saurin nufar dinning table dan ba zata iya sake kallonsu a haka ba, a haka suka nufi dinning room
in sai a lokacin da zai zauna ne ya saki hannunta.

Ta dauki plate da zuba ma Muhdeen ta ajiye masa, sannan ta zubawa Sumayya itama ta tsiyaya masu lemo da ruwa ta ajiye masu, sannan ta zuba nata itama, kallonta yayi tare da cewa
"Duk kiran yunwar da kike yi iya abincin da zaki ci kenan?"
Dariya tayi ta ce,
"Yaya wannan fa ya ishe ni."
Nan suka fara cin abincin a tare har suka kammala, Inteesar ta tattara kayan Muhdeen yayi falo kan kujera ya zauna, Sumayya ma ta biyo shi kasancewar a doguwar kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa da shi tare da kwantawa ta
aura kanta a saman cinyarsa, wasa ta fara yi da yatsun hannunsa, shima bai hana ta ba, har Inteesar ta kammala wanke kwanonin ta dawo falo ta same su a haka, bata nuna
acin rai ko damuwa ba ta zauna kujerar da ke gafensu.

Sai yamma bayan sun kammala cin abincin dare ne sannan Sumayya ta shirya don zuwa gida lokacin da zasu raka ta wajen mota ta kalli Inteesar ta ce,
"To
anwata sai kuma gobe idan na dawo ko? ango ma da zai mana kwana biyu biyu to na
ara maku kwanaki biyar, ku
auka yau ne aka kawo ki gidan mijinki a matsayin amarya."
Farin ciki a waje.

Muhdeen ba'a magana dan har ya kasa
oyuwa, godiya yayi wa Suamya dan ya ji da
in hakan da tayi, bayan ta ja motarta mai gadi ya bu
e mata gate ne ta bar gidan.

Haka rayuwa tayi ta tafiya Inteesar tana samun kulawa sosai daga wajen Muhdeen, kuma kullun Sumayya tana zuwa gidan dan koyon girki, dan yanzun ba girki kawai take koya mata ba, har da gyaran gado da
auki da duk wasu aikace-aikace na cikin gida.

Idan Muhdeen ya kwanaki biyu a gidan Inteesar haka zaiyi kawanki biyu a gidan Sumayya, yana
arin kwatanta adalci a tsakaninsu, sai dai matsayin Inteesar na musamman ne a cikin zuciyarsa, idan tana aiki a asibita da zaran ya samu sarari zai kira ta suyi ta fira da juna, ko suyi Video call tsabar kwanciyar hankali da ta samu da kula daga gare shi har ta
anyi
iba tayi kyau sosai.
Chapter 94 · 0% Book details