← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 99

Sashe 43

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gwaggo ta sanar da ke ko akwai wata matsala?"
Kai Gwaggo ta girgiza yayin da take zama a kan kujera
"Ba abunda ta fad'a itama 'yar nema tayi shiru tana rufa masa asiri badai namiji ba ki cigaba da rufa masa asiri shi zai tona naki ne,ba'a goyon bayan namiji don ba d'an goyo bane kuma tunda na tambayeki kika mani shiru to duk ranar da kika zo kika ce ga abunda ya maki na cutarwa ba abunda zance masa sai dai nayi maki dariya."
"Mummy ce ta yi ajiyar zuciya
"Son Inteesar amana ce aka baka don Allah kada ka cutar da ita kaga k'aramar yarinya ce ita sai kayi hak'uri da ita,idan ta yi abu ba dai-dai ba ka nusar da ita ta lallami da hikima ka yi hak'uri da ita kada ka zaince ta."
Kai ya jinjina tare da cewa
"To Mummy kada ki damu insha Allah ba zakiji komai na rash...

Gwaggo ta yi saurin katse sa da cewa
"Ai dole ka ce ba za'aji ba tunda ka hanata fad'a kayi mata barazana me kuwa zamuji?amma ni ba iya ji ba har gani sai na yi dani kake zance."
Kallon Gwaggon ya yi tare da fad'in
"Me kum zaki gani rigimammiyar tsohuwa?ai ba abunda zaki gani,zancen da kike ma na cewa zaki zo gidana kiyi wata d'aya ban gayyaceki ba kiyi zamanki,ko na wuni d'aya bana buk'atarki ballantana na wata d'aya ki yi z
amanki mu zamu zo ki ganmu idan kina buk'atar ganinmu."
"Wallahi baka Isa ba sai nazo"
Murmushin gefen baki ya yi
"Aiko duka ranar da kika zo sai kinyi jinya kin gwammaci da baki zo ba."
Da mamaki take kallonsa
"To me zaka yi mani"
"Ba abunda zan maki amma ina Mai tabbatar making da cewa kika zo gida na sai karen gida na ya yayyaga maki fatar jikinki."
Salati Gwaggo ta saki tana tafa hannu tana ceqa
"Oh ni Kuluwa yanzun kare ka ajiye a gidanka?saboda me?"
"Saboda ke na ajiye duk randa kika saka k'afa gida na sunanki sorry."
"Muhammadu haka zamuyi da kai d'an jakkar uba?"
Mi'kewa ya yi tare da cewa
"Ni zan d'an fita anjima zan dawo na d'auke ta mu koma gida."
Mummy ce ta amsa masa da
"Adawo lafiya"
Dady ya kalli Inteesar ya ce
"Daughter ba wani matsala ko?

Kai ta girgiza tare da cewa
"Bakomai Dady"
"Ba wani abunda kike buk'ata ?"
"Ba komai Dady"
Mi'kewa ya bar wajen.

Wunin ranar Inteesar a gidan ta yi shi Mummy ta Kira ta har d'akinta ta yi mata dabara da lallami, ko zata fad'a mata wani abu na rashin kyautatawa da Muhdeen ke mata amma sam tak'i yarda ta sanar da su haka suka hak'ura suka k'yale ta, Mufida ta ji dad'in zuwan Inteesar sun yini suna fira.

Bayan sallar isha'i ne Muhdeen ya dawo gidan don d'aukar Inteesar su tafi gida,bayan ya ci abinci ne Mummy ke sanar da shi cewa ya je tana d'akin Gwaggo,da sallama ya shiga d'akin Gwaggo da kezaune kan sallaya tana jan carbi ta amsa masa,kwance ya samu Inteesar ganin Gwaggo ya sa ya fara magana mai dad'i
"Sweet heart har kinyi barci kenan tun yanzun?"ashe daren yau ba zamuyi fira ba kenan?"
Ita kuma Inteesar cikin barcinta da yanzun ta saba aikin wahala safe da yamma, kuma yaune bata yi ba sai ta mafarkin wai yana mata hukunci me yasa ba tayi ayyukan da ya ce ta dinga yi kowa ne yamma ba?a cikin mafarkin ta wai gata kwance tana barci shi kuma yana tsaye kanta zai dake ta ne ta fara magana,daga shi har Gwaggo suna kallonta tana mutsu-mutsu sai suka ji ta fashe da kuka tana cewa.

"Yaya dan Allah ka yi hak'uri wallahi narci ne ya d'auke ni banyi ayyukan da kake sani ba,dan Allah kada ka dake ni wallahi bazan k'ara b...

Dafe goshi Muhdeen ya yi tare da sauri ya k'arasa bakin gadon yana jijjiga ta tare da kiran sunanta.

"Baby lafiyarki kuwa wani irin mafarki kike yi ne ai mafarki ba gaskiya ba ce."
Tana bud'e ido ta ganshi a gabanta sai ta k'ara rikicewa tana girgiza kai tana ja baya idanunta na zubda hawaye,goshinsa ya dafe cikin takaicin abunda ya ke 'boyewa yarinyar nan na fiddo da shi,Muryar Gwaggo da Inteesar ta ji ne yasa ta dawo hayyacinta ta gane ashe mafarki take.

"Ba shakka!

Ni tunda na kalle ki nasan baki cikin kwanciyar hankali,idan ba haka ba ace barcin mintuna Ashirin ne zaisa ki rikice haka?wannan tsoron da na gani a cikin idanunki da maganar ayyukan da ya ke saka ki kina kuka kina bashi hak'uri kad'ai na fahimci halin da kike ciki saboda abinda mutum yasa a ransa ne ya ke mafarkinsa,don haka tashi kibi mijinki ku tafi."
Mi'kewa ta yi tare da d'aukar posanta da wayarta suka nufi k'ofar fita tana gaba yana binta a baya,bayan fitar Inteesar Muhdeen na k'ok'arin fita ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa
"Idan baka kashe ta ba to ba sunanka Muhammadu ba."
Kamar ya yi mata magana sai kuma ya fasa ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi."
"Ai da ka dawo ka 'balle k'ofar gaba d'aya,mutumin banza."
A falo suka tarar da Mummy sallama suka mata suka fice.

Yana driving ransa a 'bace saboda yasan cewa Gwaggo ta gano halin da suke ciki.

"Wato ke bakijin magana ko?duk gargad'i da nayi maki sai da kika bari suka gane halin da muke ciki dake ko?."
Kai ya jinjina
"Zaki gane kuranki wallahi"
Hawaye ne ya fara fita daga idanunta cikin muryar kuka ta fara magana
"Wallahi ban fad'awa kowa ba duk yadda suka lalla'bani ban fad'a ba."
"Ni zaki raina ma hankali?kina magana a gaban Gwaggo har da kuka kina rok'ona Wai ayyukan da na saki ko?."
"Wallahi bansan na fad'a ba mafarki nayi."
"Kada ki damu mafarkin zai zama gaskiya idan muka k'arasa gida,bana buk'atata na sake Jin muryarki."
Daga nan ba Wanda ya sake magana har suka k'arasa gida,bayan Mai gadi ya wangale masa gate ya shiga ya yi parking need suka fito,yana gaba tana binsa a baya,suna shiga yaga tana k'ok'arin nufar d'akinta ya ce,
"Dakata
Tsayawa tayi tare da kallonsa,ya cigaba da magana.

"Yanzunan ki tabbatar da cewa duka falon gidannan kin goge share su kin goge,sannan duka d'akuna guda takwas dake gidannan ki tabbatar a daren nan kin sharesu kin goge su,duka toilets guda takwas ki wankesu a daren nan toilet na falon nan ma shima haka duka kitchen d'in ma haka fatan kin gana?"
Shiru tayi ta kalli time a wayarta ta ce,
"Yaya kafin na wuce da safe sai da suka ayyukan nan da ka lissafa na yi su,ba wanda banyi ba a cikinsu,bayan na gama ne muka rufe gidan muka tafi ba wani datti bamu zauna gidan ba kuma kaga yanzun k'arfe goma na dare ya kusa don Allah ka barni da safe sai nayi ba datti suka yi ba wallahi barci nake ji."
"Umarni na baki ba shawara na nemi ki bani ba, sannan bari na fad'a maki daga yau bana son uzuri."
Yana fad'in haka ya nufi parta d'in Sumayya,ita kuma ta nufi d'akinta idanunta tab da k'walla na tausayin kanta canja kayan jikinta ta yi zuwa kananun kaya yadda zata ji dad'in yin aikin.

Da paart d'inta ta soma daga nan bayan ta gama ta nufi part d'in Sumayya,haka ta dinga bin falon da d'akunan da toilets na kowane da kitchen duka biyu dinnan area ko ina sai da ta goge su tas.

Dama can ba wani datti sukayi ba fes suke kuma ba amfani ake dasu ba ba kowa a ciki,amma don mugunta sai ya sata ta yi safe da yamma.

Bata gama ayyukan da ya saka ta ba sai k'arfe d'aya na dare,duk ta gaji sai hawaye ne kawai ke tsiyaya masu d'umi daga idanunta.wanka ta yi tare da yin addu'ar kwanciya barci ta kwanta, lokacin k'arfe d'aya da rabi na dare.

K'arfe hud'u da rabi na asuba ta farka wanka ta yi ta d'auro alwala,ta yi nafila da addu'a ta samun sassauci a rayuwarta, har aka Kira assalatu ta yi sallah da azkar tana son ta tashi ta yi ayyukan safe ne barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita ba tare da ta shiryawa yin barcin ba.

Misalin k'arfe tara na safe ya fito daga bedroom d'insa ganin bai ganta a kitchen ba kuma bata shigo ta gyara masa d'aki ba yasa ya nufi d'akinta.

Tura k'ofar ya yi ya ganta kwance saman sallaya da hijab a jikinta,alamun daga sallah ta yi barcin,fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi sosai ya 'balle murfin robr ya tsiyaya mata ruwa tun daga Kan fuskarta har zuwa jikinta, a firgice ta farka tare da fad'in
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Jikinta ne ya soma rawa don ruwan ya yi sanyi da yawa,gashi dama bata son ruwan sanyi ko wanka dashi batayi Amma yau ruwa mai sanyi kamar K'ank'ara aka kwarara mata a jiki,kuka ta fashe da shi mai cin rai,yatsarsa ya sa a baki tare da furta
"Shhhhhhp"
Ba shiri ta had'ye kukan hawaye na tsiyaya a idanunta.

"K'arfe nawa yanzun?"
Kallon agogon da ke manne a d'akin ta yi
"K'arfe tara da minti biyar"
"Shine kike kwance kina barci?"
"Wallahi bansan lokacin da barci ya d'auke ni ba."
"Tashi kije ki yi ayyukan da kika San ya wajaba a kanki."
Mi'kewa ta yi zata shiga toilet taji muryarsa yana cewa
"Ina zaki je?"
"Zan shiga toilet ne na cire kayan nan sun jik'e da ruwan sanyi, idan na ce zan barsu a jikina sanyi zai kamani ne."
"Ya kamaki mana sai me?ba sanyi ba ko k'ank'ara zai kamaki ya kamaki ba matsalata bace,don haka fita ki fara ayyukan da na saka ki."
Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki ta fita ya bita da kallon banza.
Chapter 43 · 0% Book details