← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 99

Sashe 75

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya kuwa tana cikin bedroom d'inta zaune saman gado, waya ne kare a kunnenta, tana magana tana cewa
"Ba haka bane shila har yanzun mutumin a sama yake, tunda waccan 'yar matsiyata aka rasa inda take gaba d'aya hankalinsa na kanta, ko damuwa dani baya yi, ina naga sakin fuska a wajensa daga na fad'i magana akanta kinga yadda ya hauni da fad'a kamar zai cinye ni d'anya?"
Banko k'ofara d'akin yayi da k'arfi, a firgice ta mik'e tsaye tana kallonsa ganin fuskarsa ba alamun rahama be yasa zuciyarta tsinkewa, ganin yadda yanayinsa da fuskarsa suka canza ne yasa ta fara ja baya, cikin k'arfin hali ta bud'e baki ta fara magana
"Baby lafiya kuw..."
Kafin ta kai k'arshen zancenta taji ya sauke mata tagwayen maruka biyu a kumatunta, d'ayan kumatun ma haka ya sake sauke mata tagwayen maruka biyu, jiri ne ya fara d'ibanta, don tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba marinta ba sai yau, yau d'in ma maruka hud'u lokaci guda, k'eyarta ya rik'e ya buga goshinta a bango take sai goshinta ya fashe jini ya fara fita, wuyanta ya shak'e wajen mak'ogoronta ya rike take ta fara kakari idanunta suka fito waje miyau ya fara dalala daga bakinta, cikin kakkausar murya ya fara magana.

"Zaki kashe ta ko? to kafin ki kashe ta ni zan fara kashe ki, a kin had'ani da iyaye na suna fushi dani duk ta sanadiyarki, baiwar Allah da bata maki laifin komai ba kike neman kashe ta, dama Gwaggo ta fad'a mani cewa ke ba matar aure bace amma na dinga k'alubalantarta, amma gashi naga gaskiyarta a yanzun."
Jifa da ita yayi gefe sannan ya nufi hanyar fita yana huci, ita kuma yanda yayi jifa da ita ta zube wajen ko numfashi bata yi.

A can gidansu Mummy kuwa bayan fitarsa ne da Dady ya kalli Mummy ya ce,
"Waye ya sanar da shi cewa tana gidan nan?"
Mummy ce ta kalle shi tare da cewa
"Ba wanda ya fad'a masa , daga ya ci abinci shine fa ya ce wai ita ta dafa abincin nan wannan d'and'anon girkinta ne, daga nan ya dinga k'wala mata kira."
Shiru Dady yayi yana nazari, tabbas ya gane cewa Inteesar ce ta dafa masu abincin, don shi dama haka ya ke tun yana yaro indai ya d'and'ana abincin da ba mahaifiyasa ce ta dafa ba ya sani, yana ganewa Dan a lokacin Dadynsa har yana mamakinsa sai yanzunn ya ke tunowa da wani abun, wato har girkin Inteesar ma yana ganewa, gajeren murmushi Dady yayi tare da komawa ciki, Mummy ce ta kalle Gwaggo ta ce,
"Lamarin nan fa ya fara d'aure mani kai."
Dariya irin ta su ta manya Gwaggo tayi tare da cewa
"Ba abunda ke d'aure mani kai a lamarin su, ki zuba ido kawai kada ki ce komai."
Da misalin k'arfe takwas na dare ne Sumayya ta soma tari a hankali, dak'yar ya iya tashi zaune saboda tana rik'e da mak'ogoronta da ke mata zafi, goshinta dake mata rad'ad'i ta kai hannu ta shafo shi,jin yadda ya fashe ya kumbura ga jini da ta shafo, kuka ta sake da shi mai cike da tsantsar bak'in ciki da takaici, jikinta gaba d'aya ji tayi yana mata ciwo, dak'yar ta lalla'ba ta shiga toilet, tana kuka tana wanka har ta gasa jikinta, har zuwa wannan lokacin mak'oshinta na mata ciwa ga goshinta sai zugi yake mata, raki da son jiki bai bari ta gasa wurin ba.

Haka ta ta fito ta zube a Kan gado, don dama sallah bai dame ta ba ko da kafiyarta ballantana yanzun da ba lafiyar,kuka ta cigaba da yi, wayarta ta kalla inda ta fad'i k'asa lokacin da Muhdeen ya mare ta, tashi tayi ta d'auko wayar tare da lalubo number Dad dinta, sau uku tana jaraba Kira amma bai shiga ba, kuma ba zata iya kiran Mum d'inta ta sanar da ita ba, dan tunda ta lura Mum ta daina goyon bayanta ta daina sanar da ita halin da take ciki, kwanciya tayi a kan gadon har barci ya d'auke ta.

A 'bangaren Muhdeen kuwa shima haka ta kasance a gare shi, ya kwana cikin bak'in cikin abunda Sumayya ta aikata, wanda a dalilin haka kowa na fushi da shi, duk da cewar shima da nasa laifin amma nata ya janyo wannan matsalar har aka kawo wannan matakin, dan shi yanzun yayi niyyar gyara zamantakewarsa da matarsa, ya mantar da ita rayuwarsu na baya.

A haka dai bai samu isashshen barci ba har k'arfe hud'u na asuba, toilet ya shiga yayi wanka ya nufi masallaci.

Daga masallaci ya zauna yayi azkar da karatun al'qur'ani mai girma, sai k'arfe bakwai sannan ya dawo gidan, yana tafiya yana tunanin yadda zai fuskanci Dady da Mummy da Gwaggo akan Inteesar, amma ko ba komai ya samu sassauci a cikin zuciyarsa, kaso hamsin ciki d'ari na damuwar da yake ciki ya ragu, domin yanzun yasan cewa Inteesar bata mugun hannu, duk da dai akwai babban aiki a gabansa.

A falo ya had'u da Sumayya tana zaune kan kujera tana cin snacks da yogurt, don dama aikinta kenan tunda bata iya girki ba sai dai tayi ta fama da kayan su biscuits cake da sauransu, tana zaune tana tsaka da cin snacks ne ya shigo, sai da gabanta ya fad'i dan wani tsoronsa ne ya shige ta, ko kallonta baiyi ba har ya wuce ta zai nufi d'akinsa ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
"Kada ki sake kwana mani a gida, ki tattara naki ya naki kibar mani gida na."
Daga nan ya shige d'akinsa, kuka ta saki tana cewa
"Dan Allah kayi hak'uri ka gafarce ni wallahi bazan sake ba, kayi mani alk'awari na zamu rayu har k'arshen rayuwarmu ba zamu rabu da juna ba, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba dan Allah kayi hak'uri, soyayyar da nake maka ne ya saka ni cikin wannan halin.

Bai saurare ta ba ya shigewarsa d'akinsa.

A guje ta ruga d'akinta wayarta ta d'auka tana kuka, lamabar Jumy ta kira bugu d'aya ta d'auka, tana d'auka Sumayya ta fashe da kuka ta fara magana
"Jumy na shiga uku, Muhdeen ya kore ni ya ce nabar masa gidansa."
Cikin mamaki ta ce,
"What! akan me ya kore ki?"
Cikin muryar kuka ta fara magana
"Jumy ya gano gaskiya cewa nayi yunk'urin kashe Inteesar."
"Me kika ce? ta yaya ya gano gaskiya? ko dai bata mutu bane?"
Jinjina kai tayi kamar tana ganinta ta ce
"Ina tunanin bata mutu ba, kuma ta sanar cewa nice nayi mata wannan aiki."
"To yanzun ina ita yarinyar take?"
"Nima ban sani ba, amma da alamar ya sani tunda har yasan nayi yunk'urin kashe ta, kinga ta sanar da wani kenan, Jumy wallahi jiya na d'and'ani k'amshin mutuwa, kwana na ne kawai a gaba."
"To yanzun da ya ce kibar masa gidansa Ina zaki je?

London zaki koma?"
"Ba inda zanje Wallahi, bazan ta'ba rabuwa da shi ba, ni da shi takalmin kaza mutu ka raba."
"Kada fa yazo ya wulak'anta ki."
"A shirye nake da na fuskanci ko wane irin wulak'anci daga gare shi, amma bazan tabu da shi ba."
Ajiyar zuciya Jumy ta sauke ta ce
"Shikenan, Allah ya bada sa'a."
Daga nan ta katse kiran ."
Tana nan zaune har tsawon mintuna talatin, turo k'ofar yaayi ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
"Kada na dawo gidan nan na tarar da ke, don wallahi zaki sha mamaki a waje na."
Daga nan ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi,. kuka tan saki, domin Alah ya sani ba zata iya rabuwa da, gaba d'ya hankalin ta yatashi.

Wayar ce ta k'ara d'auka tare da Kiran shila a waya, labarin abunda ya faru tabbata, sannan ta cigaba da cewa
"Wallahi bana son rabuwa da shi, ya zanyi ya hak'ura ya barni, so nake mu cigaba da zaman mu, meye mafita?

"Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da dogon tunani ta ce,
"Ina zuwa k'awa ta zan kira ki"
Katse kiran tayi ta nufi k'ofar d'akinta da taji ana knocking.

Acan gida kuwa tunda Gwaggo ta shiga d'akinta Inteesar ta bita a baya, Gwaggo na zama Inteesar ta fad'a jikinta tare da sakin kuka, cikin tashin hankali Gwaggo ta d'ago ta tana cewa
"Yar albarka me ya faru kuma kike kuka?"
Cikin kuka ta fara magana
"Gwaggo kada ki mayar dani"
Kada mu mayar da ke Ina?"
"Gidan Yaya"
Murmushi Gwaggo tayi tare da cewa
"Akan wannan shine kike kuka? to ki kwantar da hankalinki tunda baki so ba zaki koma ba."
Cikin kwantar da murya tayi magana
"To kiyi mani alk'awari"
Dariya Gwaggo ta sake yi sosai ta ce,.

"Nayi maki alk'awari sai dai idan kece kika nuna kina kina son cigaba da zama da shi, idan ba haka ba ki d'auka aurenku ya rabu."
Dariya tayi sosai tare da cewa
"Ni ba abunda zaisa nayi sha'awar komawa gidansa, daga shi har matarsa basu da imani, kashe ni zasuyi idan na cigaba da zama da su."
"Ba zasu kashe ki ba sai dai idan kwananki ne suka k'are."
"Gwaggo kenan haka zancenki yake, amma ni kad'ai nasan wahalar da nake sha a gidansa."
"Dalla matsa ki bani waje, kinsan da haka shine na je gidanku tsawon wata d'aya baki sanar da ni halin da kike ciki ba?

"
"Gwaggo yadda yake nuna mani so da kulawa, da nace zan fad'a maki ba zaki yarda dani ba, saboda wayau ne da shi,yasan me yakeyi shiyasa ya ya dinga mani abubuwan da yake dan ki yarda da shi "
"Shikenan yanzundai ba inda zaki koma."
Cikin jindad'i ta jinjina kanta alamar gamsuwa da maganar Gwaggon .
Chapter 75 · 0% Book details