← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 99

Sashe 4

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan hira suka d'an taba ,daga bisani ya Mik'e yayi masu sallama sallama ya fice.
*WANE NE DADY*
Asalin sunan sa shine Alhaji Sani shi mutumin Garin kontagora ne dake nan jihar niger.sunan mahaifinsa Alhaji Mahmud da matar sa Hajiya Hauwa.'ya'yan su uku suka haifa,Babban sunan sa Adam sai mai binsa sunan sa Sani, wato mahaifin Muhdeen kenan sai karamar su Maryam,Babban yayan su Adam yana da 'ya'ya biyu Khalil da Jabir,Jabir ne abokin muhdeen.sai Sani wato mahaifin Muhdeen Yana da 'ya'ya uku Muhdeen ne Babba,Asiya ce ta biyu sai ta ukun su Mufida 'yar autar Mummy kenan,Maryam ita ce kanwar Sani wato itace take bin mahaifin Muhdeen d'in.tana da 'ya'ya biyu tunda ta haifi 'yan biyu bata sake haihuwa ba.daga ita sai tagwayenta Azeeza da Azeema,Adam Babban ma'aikacn gwamnati ne Yana zaune a garin Abuja,yayin da Sani wato mahaifin Muhdeen Yana zaune a Babban birnin jihar niger wato Minna kenan, shahararren 'Dan kasuwa ne da yake kasuwanci kasashe daban-daban yayin da yakai wata ziyara a garin Katsina wajen wani a bokin sa Alhaji Hassan,to a garin ya hadu da Fatima wato Mummy mahaifiyar su Muhdeen kenan,Allah ya k'addara auren su inda ta tare a gidan sa dake unguwar Bosso Estate nan garin Minna,har ta haifi yaran ta guda ukuDuk da a yanxun takan ce 'ya'yan ta hudu har da Inteesar wacce a shekaru uku da suka wuce Allah ya hada ta da inteesar.

Shekaru uku baya wata Rana da safe Mummy zataje unguwa direban ta ya dauko ta a mota tsautsayi ya gifta har Direban ya 'Dan kad'e ta da mota ta fadi a k'asa, kasancewar bataji ciwo ba yasa ta Mik'e da sauri yayin da direban da Mummy suka fito suna salati, cikin hanzari Mummy ta k'arasa gare ta ta ri'ke ta ta ce,
"Sannu ko zo mu tafi asibiti"
Inteesar dake sanye da uniform d'in school ta girgizawa Mummy kai cikin sanyin muryarta ta ce,
"Kada ki damu ba abunda ya same ni Ina lafiya,banji ciwo baAllah ya kawo abun da sauk'i"
Take Mummy taji son yarinyar har cikin ranta,shafa kanta tayi ta ce,
"To muje ga chemist can ko magani ya 'Dan baki saboda tsamin jiki."
Girgiza Kai tayi tare da cewa,
"Wlh ba komai kada ki damu."
Kai mummy ta girgiza tare da cewa,
Ina ne gidan KU take?

Kallonta Inteesar tayi ta ce
"Acan bayan layin ne ba nisa."
Mummy tace
" To muje na rakaki gida.."
Dak'yar Inteesar ta yadda ta shiga motar suka karasa har kofar gidan su Inteesar din,da sallama suka shiga Abba dake zaune kan tabarma yana shan Koko da k'osai yayin da Umma ke gefen shi zaune,tozali sukayi da Hajiya Fatima kamilalliyar mace mai kwarjini,Ummace ta Mi'ke ta d'auko tabarma daga d'aki ta shinfid'e a gefe tare da cewa,
"Maraba lale sannu da zuwa"
Murmushi mummy tayi ta karasa ta zauna,a gefen tabarma,ta zaunar da Inteesar a gefen ta,sannan ta kalli Abba cikin girmamawa ta ce,
"Ina kwana mallam"
Cikin sakin fuska da Kamala irin tasa ya amsa Mata da cewa
"Lafiya qalau ya aik?"
"Alhamdulillah"
tace tare da kallon Umma ta sakar mata murmushi kafin ta gaishe ta Umma ce tayi saurin cewa.

"Ina kwana Hajiya?ya aiki?"
Murmushi Mummy tayi tare da cewa
" Alhamdulillah angodewa Allah."
Umma ce ta K'ara cewa
"Masha Allah Allah dai yasa ba laifi tayi ba naga ankawo ta har gida."
Atunanin ummi ta d'auka Mummy malamar su Inteesar ce.

Mummy ce ta danyi ajiyar zuciya sannan ta basu labarin Yadda akayi direban ya kad'e Inteesar kuma tak'i yadda suje Koda chemist ne,sannan ta basu hak'uri suka ce kada ta damu ba komai.

Abba ne yace to me ya dawo da ita a wannan lokacin ?

Cikin sanyin ta take sanar dasu an Kore ta ta kudin school fees ne shiru sukayi yayinda Abba ya dafa goshin sa
Mummy ce ta Ciro kud'i a jakkar ta masu yawa kimanin naira dubu ashiri
tace gashinan susayi Mata magunguna,
Amma fir sukaki karba kud'in nan Babu yadda Mummy batayi ba har aje masu tayi amma Abba ya rantse akan cewa bazasu kar'bi kud'in ba,ba yadda ta iya dole ta tafi tare da yi masu sallama ta tafi.

Bayan tafiyar ta ne mallam Ali wato Abba ya kalli Umma cikin damuwa ya ce,
"Tun satin da ya wuce nake ta tunanin kud'in makarantar nan Amma na kasa samu wlh."
Umma ce ta kalle shi ta ce,
"To mallam mai zai hana mu mayar da ita makarantar Gwamnati?"
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*DON K'ARIN BAYANI*
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.

Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta ta Shi dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya,to KU gafarceni ni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Page0
Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da kallon ta ya ce,
"A zahirin gaskiya bana son nasaka Inteesar makarantar Gwamnati,zanyi k'ok'ari na naga na samu kud'in nan."
Aijyar zuciya umma ta sauke tare da kallon Inteesar.

Ya cigaba da cewa
"Bari dai naje kasuwar na dawo muga Abunda Allah zaiyi."
"To Allah ya bada sa'a ya rufa Mana asiri."
cewar umma
Abba ne ya amsa da Ameen.

Inteesar dai tagumi tayi.

To a ranar da yammaci Mummy ta dawo gidan su Inteesar Don ta K'ara duba jikin ta,inda ta kawo masu Sha tara na arzikisannan ta nemi alfarmar cewa tunda unguwa d'aya suke basu da nisa tana son tasa Inteesar makarantar da 'yar ta take zuwa wato mufida dukkan su kusan sa'annin juna ne bazasu wuce shekaru goma Sha biyar ba a lokacin,umma ta ce,
" Yanzun ni bazance komai ba idan mahaifin ta yazo zan sanar dashi duk shawara da muka yanke shikenan."
Daga nan tayi masu sallama kan cewa jibi zata dawo taji shawarar da suka yanke.

Haka kuwa akayi da Abba ya dawo kasuwa bayan yaci abinci ya huta,Umma ta kalleshi tare da cewa,
"Yauwa mallam wannan matar da suka kusan Kad'e Inteesar da mota tazo ta kawo mana abin arziki sannan ta nemi alfarmar a wirin mu."
Kallonta yayi tare da cewa
"Wace Alfarma kuma zata nema a wurin mu kuma?"
"Wai dama cewa tayi Tana son ta canzawa Inteesar makarantar boko ce,wai zata saka ta inda 'yar ta sa'ar Inteesar take makaranta.wai zata had'a su su dinga tafiya tare inda Direban ta zai dinga kaisu idan lokacin tashi yayi yaje ya dauko su."
Girgiza Kai Abba yayi alamun rashin amincewa
"Bazai yuwu ba,bana buk'ata wato don taji Inteesar tace an Kore ta kud'in school fees shine tayi tunanin haka"
Gyada Kai Ummu tayi tace ,
"To shikenan"
Yaci gaba da cewa
"Insha Allah yadda nad'uki nauyin karatun ta tun daga nursery har primary yanzun Tana secondary jss 3 ,insha Allah bazai gagare ni ba,Allah zai shige Mani gaba."
Bayan kwana biyu kuwa sai ga Mummy ta dawo,cikin sa'a kuma ta samau mallam Ali a gidan,bayan sun shimfid'a Mata tabarma ta zauna ne ta kalli malam Ali.

"Mallam barka da safiya ya iyali?"
Cikin sakin fuska kuwa ya amsa Mata tare da cewa
"lapiya qalau Hajiya, ya gajiyan ki?na dawo Naga sako nace meye zakije wani kashe kud'i wajen yi mana siyayya da Ina gidan bazamu kar'bi komai daga gare ki ba ai tsautsayi ne kuma yarinyar da bataji ciwo ba ba buk'atar ki wahalar da kanki."
Murmushi tayi tare da cewa,
"Ai ba wannan ya kawo ni bama,nasan mai d'akin ka ta sanar dakai alfarmar da muke nema a wajen ka ko?"
Kai ya gyada Alamar Eh
"Ta sanar dani amma gsky kiyi hakuri kibar maganar nan kawai, d'aukar nauyin karatun Inteesar bazai gagare ni ba insha Allah, kamar yadda a can baya ban kasa ba."
Ajiyar zuciya ta sauke don ta fahimci inda maganar tasa ta dosa,yana ganin kamar don ya kasa ne zata d'aura daga yanda ya tsaya,ita kuma ba haka bane a zuciyar ta,soyayyar yarinyar take ji har cikin ranta Allah ya d'aura Mata kaunar 'yar su.

Cikin sanyin murya tace,
"Bawai ka kasa bace,a'a wallahi Allah ne ya d'aura Mani soyyayar 'yar ku,Ina kaunar ta fisabilillahi har cikin raina.duk da baku sanni ba kuke tsoron amincewa dani ko?"
Kai Mallam Ali ya girgiza tare da cewa,
"Duk da bansan Halin ku ba Amma da alamu ku mutanen k'warai ne domin inajin yanda jam'ar unguwa ke yabon ku akan kyautatawa da kukewa makwabtan ku,musamman Alhaji Sani mijin ki kowa yabon sa yakeyi akan kyawawan halayyar sa da kyautatawa mabukata musamman watan Ramadan Sai dai Allah ya saka masa da alkhairi."
Murmushi tayi cikin Jin dad'i,yayin da Umma ta amsa da Ameen.

Mummy ta ce,
"Naji dad'in jin hakan,kamar yadda ka sani muna da yara uku da miji na babban wato Muhammad muhdeen Yana can kasar waje Yana karatun masters d'in sayanzun 'yan matan su biyu ne a gaba na Asiya ita ke bin Muhammad Muhdeen,yanxun haka wannan shekaran insha Allah zata kammla karatun secondary din ta sai Auta wacce bazata wuce sa'ar Inteesar ba don Allah ka Amincewa mani da buk'atata kullun da safe idan ta shirya sai tazo Direban ya kaisu tare,idan an tashi yaje ya d'auko su,na d'auki nauyin karatun nata don Allah da soyayyar ka annabi Muhammad S.A.W."
Jikin mallam Ali ne yayi sanyi domin duk taurin kansa idan aka had'a shi da Allah da mazon sa angama yace to
" Shikenan Allah yasaka da khairan."
Waigawa tayi tana neman Inteesar cikin murmushi ta ce,
"Ina Yar tawa take?"
Umma ce ta ce,
"Ta tafi islamiya"
Kai ta gyada tare da cewa
"Agaida mani ita"
Mikewa tayi tare da masu sallama tabar gida.
Chapter 4 · 0% Book details