← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 99

Sashe 46

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ya same su suna ta cin abinci suna zuba santi,sunci lafiyayyan girkin Inteesar kuma daddad'i da lemun da ta had'a masu,Salisu ne ya ce,
"Gaskiya zan kawo Saliha ta nan gidan a koya mata irin wannan girkin."
Jabeer ne ya yi dariya yana cewa
"Ashe matar ta ka bata iya girki ba kenan."
"Inji waye ya ce mata ta bata iya girki ba?da wa ke dafa mani abincin da nake ci?"
Dariya Jabeer ya k'ara yi tare da cewa
"Oho na sani ko kaima matarka irin ta o o ne bata iya komai ba sai anje restaurant anyo mata takeaway sannan suci."
Ya k'arasa maganar ya na kora lemu a bakinsa
Muhdeen ne ya kalle shi dan yasan da shi ya ke yi bada kowa ba k'ara tsuke fuska ya yi tare da cewa
"Jabeer da wa kake?"
Murmushi ya saki
"Na kira sunanka ne?fira muke yi idan zaka shiga to bisimillah."
Dariya ya sake yi tare da cewa
"Oh ashe fa haka ne dama hausawa na cewa mai kaza a cikin aljihu baya jimirin ass."
"Jabeer Nagode da ziyara zaka iya tafiya ka gaida iyali"
"Korata ka ke yi ?"
"Eh ko na kore ka gida na ne ai ina da ikon yin hakan."
Dariyar rainin hankali Jabber yayi kafin ya ce
"Sannu takobi sarkin gida,ba yadda zaka yi dani na zame maka ciwon ido sai hak'uri,kuma ba yanzun zan tafi ba sai munsha fira da kaka ta Gwaggo sai magariba zan tafi,ka fad'awa Inteesar idan zata yi girkin dare ta dafa har da ni da Maryam ta zuba mana a flask na tafi dashi gida."
"Saboda kai ka ajiye ta ko?."
Daga nan dai bai sake ce masu komai ba suna ta cin abincinsu suna fira,bayan sun kammala ne suka yi masa sallama tare da cewa wai ya kira amarya su yi mata godiyan girkin da suka ci,ya ce wai zai isar masu da sak'on godiya yanzun ta kwanta ne ba zata samu damar fitowa ba,sun san ya fad'a ne kawai amma ba wani barcin da take yana dai fad'a ne,nan suka dinga masa tsiyarsa bai tanka masu ba,suka sallami Gwaggo suka tafi,nan ya zauna tare da Gwaggotana ta jansa da fira duk da cewar hankalinsa ba wajenta ya ke ba,ya kasa gane dalilin da yasa hankalinsa ya k'ikwanciya akan wayar da ya tarar Inteesar na yi,gaba d'aya ransa a 'bace ya ke da lamarin, Inteesar ce ta fito ta nufi kitchen ta kawo ma Gwaggo abinci tare da Gwaggo suka cin abincin,suna fira ya yinda shi kuma idonsa na kan Inteesar abubuwa da yawa yake sak'awa akanta.

Da misalin k'arfe biyar ne Inteesar ta shiga kitchen don d'ora masu abincin dare, Gwaggo ce ta biyo ta kitchen d'in tana cewa.

"'Yar albarka me kuma xaki girka ne?"
Murmushi Inteesar ta yi tare da cewa
" Duk abunda kike so shi zan girka maki Gwaggo na ta kaina."
"A'a nikan kada kibi ra'ayina kibi ra'ayin mijinki duk abunda kika san ya fi so shi zaki yi."
Shiru ta yi tana tunani ita kanta bata ta'ba zama da shi a inuwa d'aya ba,ta ya ya zata san abunda yafi so? mutumin da ma har yau bai tunda tazo gidan sau d'aya ya ci abincin ta shima ganin idon bak'uwa ne.

"Ke ya naga kunyi shiru anya kuwa 'yar albarka kina kula da miji?kar fa ki manta yana da wata matar da ya ke so, ke da ba soyayya ce ta had'aku ba zage dantse zaki yi ki nemi soyayyarsa so nake ki zarce waccan matar a wajensa,kafin ta dawo ma sai dai ta ganki da ciki."
Da sauri Inteesar ta juya ta kalli Gwaggo.

"Meye zaki jalleni haka?me ye ribar auren idan ba soyayya ba?indai shi jarimi ne ma yakamata ace kina da shigar ciki,shin ma na tambaye ki yana da k'wazo kuwa?idan har baida k'wazo da jarumta ki fad'a mani,akwai wani garin yaji da zan baki ki dinga zuba masa a cikin abinci,ina mai tabbatar maki da zaki zuba masa wannan yajin da kanki zaki mani godiya da addu'a."
Ta k'arasa maganar tana dariy,dafe goshi Inteesar ta yi cikin kunya da takaicin maganar Gwaggo,don ta lura Gwaggo sam bata kunyar fad'ar ko wace irin magana,don haka ta yi shiru bata ce komai ba,ganin ta yi shiru ne yasa Gwaggo ta k'ara cewa
"Naji kunyi shiru na baki ne 'yar albarka?"
Nan ma bata ce komai ba
"Bari na je na d'auko maki ko?"
Ta k'arasa maganar zata fita daga kitchen d'in sai ta ji muryar Inteesar tana cewa
"Kubarshi Gwaggo."
Wangale baki ta yi
" To masha Allah ni nasan jika na ba ragon namiji bane."
Haka Gwaggo ta cigaba da suratanta tun tana tsaye har ta zauna, ita dai Inteesar bata ce komai ba har ta gama girkin jallop d'in taliya ta girka da ya ji kayan lambu da busashshen kifi.

Da misalin k'arfe takwas na dare bayan sun idar da sallan isha'i Gwaggo na zaune a falo, Inteesar ta k'araso sanye da duguwar riga na material,kallon Gwaggo ta yi tare da cewa
"Gwaggo ki tashi muci abinci"
"Ina shi mijin naki ya tsaya an idar da sallah bai shigo ba?"
Ta'be baki ta yi a zuciyarta ta ce
"Oho masa ina zan sani me ye ruwana da shi?"
A zahiri kuma ta ce
"Maybe akwai abunda ya tsayar da shi ne."
Gwaggo ta sake jefa mata tambaya
"Dama ba daga sallar isha'i ya ke shigowa ba?"
Shiru Inteesar ta yi don bata da amsar tamayar da Gwaggo ta ke Mata,ita da idan ta gama ayyukan bautan da ya ke saka ta ta shige d'aki bata fitowa sai washe gari,bata sanin fitarsa ko dawowarsa.

Turo k'ofar falon aka yi tare da sallma yana ri'ke da leda a hannunsa,amsa sallmar sukayi Gwaggo ta yiwa Inteesar alamun ta kar'bi ledar hannunsa,ba musu ta d'an durk'usa ta kar'ba dan kada Gwaggo ta ga laifinta.

Fruits ne a ciki ta nufi kitchen ta wanko su ta zuba a faranti ta yayyanka su ta ajiye a dinning table,Gwaggo ne ta rik'o hannun Muhdeen zuwa dinning table,bayan sun zauna ne Inteesar ta zubawa kowanne abincin da zai ci ne suka fara ci,ita dai Bata ci na kirki ba ta mi'ke zata bar wajen,
"Yar albarka ya haka ba kici abinci da yawa ba,har yanzun kina nan da rashi son abincinki?"
Shagwa'be fuska ta yi Gwaggo na k'oshi."
Daga nan ta koma falo ta zauna, Gwaggo kuma suka dinga fira da Muhdeen,kafin ya ce bari ya shiga ciki ya fito, Gwaggo ma falon ta dawo Inteesar ta je ta tattara kayan da suka 'bata ta gyara wajen.

Falo ta dawo ta zauna suna kallon film da Gwaggo, Muhdeen ma ya zo ya zauna,
Da misalin k'arfe goma na dare Inteesar ta ce,
"Gwaggo barci nake ji zan je na kwanta."
Kallon Muhdeen Gwaggo ta ce
" A d'akin ka take kwana ne ko kuma Kai ke biyo ta d'akinta?"
Shiru ya yi yana kallon Gwaggo don dai bai isa ya ce Mata kowa d'akinsa ya ke kwana ba,don haka ya ce,
"Ita ce dai take bina d'aki na."
Jinjina Kai Gwaggo ta yi tare da cewa
"Hakan ya yi don dama na tambaya ne don nasan inda zan kwana,idan har d'akinka kuke kwana Ni sai na kwana a d'akinta idan kuwa d'akinta kuke kwana na shiga wancan d'ayan d'akin na bak'i."
"Tura baki Inteesar ta yi tare da cewa
"Gwaggo nikam da ke zan kwana."
"Wace ni yarinya kibi mijinki ba ruwa na,in banda salon munafurci irin ta ki da kafin nazo da wa kike kwana a gidan nan?"
"Ni kad'ai nake kwana"
Da sauri Gwaggo ta kalli bakinta jin abunda Inteesar ke fad'a
"Yar jakkar uba to ki bishi ki kwana ke dad'an."
Inteesar Bata sake magana ba ta nufi d'akinta tana k'unk'uni,dariya Gwaggo ta yi tare da kallon Muhdeen ta ce,
"Amma da dukkan alamu kana fama da yarinyar nan akan shimfid'a ko? alamu sun nuna haka shiyasa take gudunka,to bari na maka kada ka ce zaka raga mata ko kad'an idan ba haka ba mace raina ka zata yi."
Baice mata komai ba sai kallonta da yake tana ta zuba suratai.

Inteesar kuwa tana zuwa d'aki wanka ta yi ta ta shafa man Hajiya bilki da turarenta,gyara gashin kanta ta yi ta d'aure su kamar yadda ta saba ko wane dare,rigar barcinta ta shara sharan rigar barcinta ta d'auka ta saka iya guiwar ta rigar ta tsaya,gadonta ta haye tayi addur kwanciya barci ta kwanta.

A can falo kuwa Gwaggo ta mik'e ta ce
"Muhammadu mu kwana lafiya zanje na kwanta."
Mi'kewa ta yi ya yin da yake mata sai da safe.

Tana shiga d'aki ta saki baki da mamaki ganin Inteesar kwance tana barci,ranta ne ya yi masifar 'baci ta k'arasa ta yaye bargon da Inteesar ta lullu'be jikinta da shi,tare da kai mata duka a k'afarta.

"Tashi 'yar jakar uba tafi d'akin mijinki."
Tashi zaune Inteesar ta yi tare da cewa
"Don Allah ki barni na kwanta a nan."
Gwaggo ba ta ce komai ba ta janyo hannun Inteesar tana cewa
"Har turaka zan raka ki yau kuma wallahi idan baki fita daga idanuna ba sai naci mutuncinki"
Inteesar ganin da gaske
Gwaggo ta ke zata kaita ne yasa ta ce
"Don Allah Gwaggo ki barni na canza kaya."
"Ba kayan da Zaki canza ko tsirara kike haka zan kai ki ai mijinki ne."
"To ki barni na d'auki hijanin sallar asuba."
Jin haka ne yasa Gwagho sakin hannun Inteesar ta koma ta d'auko hijabinta ta zura a jikinta,har k'asa ya sauka mata,sake jan hannunta Gwaggo ta yi suka fita sai da ta kaita har k'ofar d'akin Muhdeen sannan ta saki hannunta tare da cewa
"Shiga"
Bata shiga ba sai da Gwaggo ta tura k'ofar ta hankad'ata sannan ta shiga,Gwaggo ta janyo masu k'ofar ta rufe.

Baya cikin d'akin ta ji karar ruwa a toilet alamun wanka ya ke, kasancewar barci ne a idonta ya sa ta kwanta a saman sofa dake d'akin, nan da nan barci ya yi awon gaba da ita ta k'udundune kanta cikin hijab.
Chapter 46 · 0% Book details