Sashe 67
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waige -waige ta dingayi tana neman abunda zata bugawa Inteesar, dai -dai lokacin Inteesar ta farka ganin Sumayya n huci yasa ta tashi a firgice ta sauka daga Kan gadon, Idanun Sumayya be ya sauka akan jug na glass dake ajiye a side drawer,ta d'auko shi Inteesar na saukowa ta Sumayya ta buga mata jug d'inan a kanta, k'ara ta saki tare da zubewa k'asa a wurin sumammiya, jini na fita daga cikin kanta.
A can gidan Mummy kuwa gaba d'aya Mufida habkainta bai kwanta ba, tunda Inteesar ta bata labarin halin da take ciki a giadan aurenta, don haka ta tashi ta nufi d'akin Mummy dan ta sanar da ita halin da d'anta yake ciki da matar da suka aura masa asan matakin da za'a d'auka akai.
*Daga alk'alamin*
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
Don Karin bayani
09965327995
Love you oll
Comments and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page5
A can gidan Mummy kuwa gaba d'aya Mufida hankalinta bai kwanta ba, tunda Inteesar ta bata labrin halin da take ciki a gidan aurenta, don haka ta tashi ta nufi d'akin Mummy dan ta sanar da ita halin da d'anta yake ciki da matar da suka aura masa asan matakin da za'a d'auka akai.
Koda ta shiga d'akin Mummy bata same ta a ciki ba, don haka ta nufi kitchen don tasan yanzun tana kitchen tana had'a masu breakfast, ko da ta shiga Mummy na cikin kitchen d'in tana aiki.
"Sannu da aiki Mummy"
"Yauwa Mufida kin shiga d'aki kina barci kin barni da aiki ni kad'ai ko?"
Girgiza kai tayi tare da cewa
"Hmm Mummy Ina naga ta barci wallahi ko jiya daddare banyi isashshen barci ba."
Mummy da ke k'ok'arin sauke tunkuyar farfesun kayan ciki ne, ta dakata tare da kallon Mufida ta ce,
"Me ke damunki ?
Ta kashe gas d'in tare da kallon Mufida ta ce
"Ina sauraronki me ke damunki?"
"Mummy kun k'ulla auren yaya da Inteesar, kuna zaton suna zaune lafiya amma ba haka bane Mummy, yaya baya son Inteesar kuna za ganin yana nuna maku kamar yana k'aunarta bayan azabtar da ita yakeyi, yanzun haka matarsa da kuke ganin kamar baya tare da ita to tana nan cikin gidansa, tare da ita suke k'untatawa Inteesar sun mayar da ita kamar baiwa mara 'yanci."
Zuciyar Mummy ce gaba d'aya ta tsinke, ta zuba ma Mufida Ido ta ce,
"Ya akayi kika sani."
Gyara tsayuwa Mufida tayi ta bawa ta bawa Mummy labarin da Inteesar ta bata tun daga ranar aurensu har zuwa dawowar matarsa da yadda sukayi amfani da ita wajen biyan buk'atarsu har ya zuwa jiya da suka had'u asibiti.
Mummy ki tayi gaba d'aya k'afarta ya gagara d'aukarta, zuciyarta sai tafarfasa take kallon Mufida tayi tare da cewa
"Je ki d'auko mayafinki mu tafi."
"Ina zamu je gidan son"
Fita sukayi gaba d'aya kowace ta nufi d'akinta, ba jimawa Mummy ta fito sanye da hijab Mufida ma mayafinta ta d'auko suka nufi harabar gidan, tun kafin su k'arasa Mummy ke k'walawa direbanta Kira, a guje a k'araso don jin yanayin Kiran yasan ba na lafiya bane, kallonsa tayi tare cewa
"Kad'auko mota yanzun ka kaini gidan son."
Cikin rawar jiki ya fito da mota suka shiga yaja suka bar gidan
A can gida kuwa tunda Sumayya taga inteesar kwance bata motsi tayi ficewarta daga cikin d'akin, karo sukayi da jumy da shigowarta kenan, kallon Sumayya tayi ta ce
"Kinga na biyo ki gida da safe ko? waya ta ce na mance a cikin motarki."
Ganin yadda Sumayya ke huci yasa ta ce
"Sumy what happened"
Kasa magana tayi illa waige -waige ta dinga yi kamar me neman wani abu,rik'e ta tayi tare da cewa
"Please talk to me waya ta'ba ki yanzu-yanzu?
Cikin karaji ta fara magana
"Jumy Wai ni za'ayiwa cin amana? ya ce baya sonta iyayensa suka aura masa ita dole, ya ce kada na damu kaina shi bai d'auki aurenta a matsayin aure ba zaman gidansa tamkar zaman gidan kurkuku ne a wajenta, mu d'auke ta tamkar 'yar aiki haka ya dinga Mani dad'in baki har na yarda dashi akan cewa maganarsa gaskiya ce, jiya naga d'an kunnenta da d'an kwalinta akan gadonsa, tunda ita ke gyara mana d'aki nida shi sai na d'auka wajen gyara ne ya fad'i ashe har kwana yake da ita, ni kuma bazan iya sharing nashi da kowace mace ba ballantana ita k'ask'antacciya 'yar matsiyata, wallahi bazai yiwu ba gara ta mutu duk macen da ta ra'be shi sai na kashe ta."
Ajiyar zuciya jumy tayi tare da cewa
"Yanzun ina suke?"
"Da alma baya gidan amma ita na same ta kwance a gadonsa na kashe ta."
Cikin firgici da rud'ewa Jumy ta zaro ido waje tana ja da baya ta ce,
"Kin kashe ta? ta yaya kuma ya akayi kika kashe ta ba tare da kinyi tunanin abunda zai biyo baya ba?"
"Ba abunda zai biyo baya na kashe banza wallahi, don iyayenta ba suda komai da zasu iya ja da Mahaifi na."
Girgiza kai Jumy tayi tare da cewa
"Kinyi kuskure idan iyayanta basu da komai da zasu tsaya mata ai iyayen mijinki suna da shi, kuma ke da kanki kike bani labarin irin k'aunar da suke mata da har suka aura masa ita, kinsan kuwa ba zasu barki kisha ba, yanzun Ina mijinki yasan abunda kikayi?"
Girgiza kai tayi tare da cewa
"Bai San na kashe ta ba, da alama baya cikin gidan nan"
"To Alhamdulillah yanzun tunda bai san kin dawo ba kiyi gaggawar barin gidan, nan sai kin tabbatar ya dawo kafin ki dawo, cikin ma'aikatan gidan nan akwai Wanda yaga dawowarki ne?"
"Mai gadi kawai yasan na dawo"
"To shima kija masa kunne kada ya sanar da kowa kin dawo, koda an tambaye sa ya ce baki dawo gidan ba, kiyi masa barazana sosai ta hanyar idan ya fad'a k'arshen aikinsa ya zo."
Haka kuwa akayi Jumy taja hannuna suka nufibhanyar fita, Kiran mai gadin tayi tare da masa gargad'i da barazana akan ko an tambaye sa ya ce bata dawo gidan ba, ya kuma tsorata don baya son rasa aikinsa.
Motarta suka shiga ta fige ta suka bar gidan.
Tafiyarta ba jimawa Mummy suka k'araso gidan, horn direbanta yayi mai gadi ya lek'o ganin su ne yasa ya wangle masu gate, shigowa yayi tare da yin parking suka fito, mai gadin ya gaishe su basu ma tsaya kula shi ba suka nufi cikin gidan.
Da sallma suka shiga ba kowa a falon, d'akin Inteesar suka nufa nan ma bata nan, suka duba kitchen bata nan, wayar Muhdeen Mummy ta Kira a kashe don haka ta d'an jira tsawon mintuna goma ba alamar motsi yasa Mufida ta ce
"Kodai basu nan be?"
Mummy ta kalle ta ta ce,
"Ina inteesar zata je da safen nan?"
Mufida ta mik'e tare da cewa
"Bari na duba d'akin yaya ko yana ciki."
Kai kawai Mummy ta gyad'a mata, yayi da ta nufi d'akin Muhdeen, knocking tayi har sau uku shiru, kawai sai ta tura k'ofar ta shiga idanunta ya sauka akan Inteesar dake kwance a sume kanta na zubar da jini, K'ara ta saki Wanda ya razana Mummy ta nufi d'akin da sauri, idanunta ya sauka akan Inteesar k'araswa tayi tare da tallabota idanunta na zubda hawaye tana kuka tana jijjiga ta Mufida ma kuka take yi tana Kiran sunanta bata motsi bata numfashi, ruwa ta umarci Mufida da ta kawo mata da sauri ta k'arasa ta bud'e fridge dake cikin d'akin ta d'auko goran ruwa ciki ta kawowa Mummy, kar'ba tayi ta yayyafa mata mata shiru ba numfashi,sau hud'u tabna zuba mata ruwa shiru.
Wayar ta ta duba ta laluno number Jabeer tare da kiransa, fitowarsa kenan daga d'akin tiyata yana kunna wayar sai ga Kira Mummy, d'agawa yayi ko jira batayi yayi magana ta ce
"Jabeer kana ina?"
"Ina asibiti Mummy"
Kayi sauri kazo ka same ni a gidan son kuma kada ka sanar da shi kazo kawai yanzun nan ba sai anjima ba."
Kashe wayar yayi ya nufi motarsa yana tambayar kansa ko me ke faruwa yaji muryar Mummy kamar tana kuka, figar mota yayi tare da barin asibitin, gidan Muhdeen ya nufa, Mummy ce tayi wani tunani ta ce kada ya shigo ciki ya tsaya d'an nesa da gidan gasu nan zuwa, sai kuma ta share hawayenta tare da k'ok'arin dai daita nutsuwarta sannan ta fita waje ta umarci mai gadin da ya je bakin titi ya siyo mata bottle of water mara sanyi na gidan duk sunyi sanyi yaje can bakin tati ya siyo a can, tunda yasan Mahaifiyar mai gidansa ne yasa ya tafi yabar gidan.
Yana fita ta umarci Mufida ta taimaka mata su d'auki Inteesar su tafi da ita, haka kuwa suka kama ta suka fita Direban Mummy ne yana ganinsu yayi saurin bud'e masu bayan motar suka kwantar da ita.