← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 99

Sashe 51

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance take a d'akinta tana danne-danne a waya, Jabeer ne ya fito daga bedroom da alama wanka yayi, kallonsa tayi tare da cewa
"Ya maganar da mukayi da kai ne na cewa gobe zaka kaini gidan Muhdeen."
Murmushi yayi tare da cewa
"Maryam kenan ki bari sai wani jik'on, don gobe da sassafe zanbar gidan nan."
"Nifa na kula da kai kamar baka son zuwa ka kaini, sau biyu ina maka magana kana kawo mani uzuri."
"Ba haka bane duk lokacin da nake da uzuri shine kike magana."
"Ina son ne na tabbatar da gaskiyar abunda naji."
Kallon mamaki ya mata sannan ya ce,
"Me kike son ki tabbatar a gidan nasa?"
Murmushi tayi
"Naji ance budurwarka ya aura?"
Nuna k'irjinsa yayi da yatsarsa manuniya
"Ni kuma?waye ya ce maki budurwa ta ce Inteesar?"
"Ba wanda ya fad'a mani,amma ni nasan abunda nakeyi."
"To hasashenki ba gaskiya bane ban ta'ba soyayya da Inteesar ba."
Dariya tayi
"Ko da ace baka ta'ba soyayya da ita ba ni nasan kana sonta,na kalli yadda ka dinga rawan jiki da ita likacin auren Muhdeen na farko,sannan lokacin da ka kawota gidan nan kuka siyo mani agwaluma naga tsantsar soyayyarta a cikin idanunka da irin kallon da kake mata,bayan haka nasaha kamaka kana kallon photonta lokuta da dama,sannan ranar da Muhdeen ke sanar da kai cewa Inteesar aka aura masa bayan dawowarka gida naga yanayinka ya canza sosai ka shiga damuwa da yawan tunani."
Shiru yayi yana sauraranta, don yasa duk abinda ta fad'a gaskiya ne, don haka daga nan bai sake cewa komai ba do baida ta cewa yanzun sai ta samu abun fad'a,don haka ya share ta kamar baiji maganar da take fad'a ba.

"Kuma nikam gaskiya naji dad'in auren Inteesar da Muhdeen,domin kuwa ko ba komai hankali na ya kwanta,don gaskiya tunda na fahimci cewa kana sonta hankili na ya tashi miatuk'a ban dai nuna maka bane, amma lokacin da naji labarin abokinka kuma d'an uwa a gare ka ne ya aureta sai hankali na ya kwanta.

Ta k'arasa maganar tana dariya,ido ya zuba mata yana nazari,tabbas abunda ta fad'a gaskiya ne shima ya san da haka.

"Allah ya kaimu goben zan kaiki."
Murmushi tayi tare da cewa
"Ameen ya rabbi"
Da misalin 'karfe biyar na yamma ne ta farka daga barcin da tayi, toilet ta shiga ta d'auro alwala hijabin da ke jikinta ne tasa taji k'arar k'ofar gate alamun an bu'de za'a fita,matsawa tayi kusa da window ta d'an zuge labaulen window ta lek'a,hangosa tayi sanye da farar jallabiya ya fita zuwa masallaci,a zuciyarta ta ce
"Nikan nan na samu wurin kwana har Gwaggo ta wuce sannan na koma d'aki na."
Matsawa tayi ta shinfid'a sallaya ta tayar da sallah.

Gwaggo ma haka ne daga 'bangaren ta sallah take,don ita a zatonta Inteesar na can d'akin Muhdeen kamar yadda ta tura ta.

Da misalin k'arfe shida na safe ne ta fito daga d'akin ta nufi d'akinta,da sallamata a bakinta ta shiga, Gwaggo na kwance akan gado bayan ta amsa sallamar, Inteesar ce ta k'araso cikin d'akin ta durk'usa ta ce,
"Gwaggo ina kwanana?"
"Lafiya lumui 'yar albarka kin tashi lafiya?"
"Lafiya qalau Gwaggo."
"To ya kwanan mijin naki?"
"Yana lafiya lau"
Kai Gwaggo ta jinjina tare da cewa
"Masha Allahu,Allah yayi maku albarka ya azurta ku da samum yara masu albarka."
Tura baki Inteesar tayi tare da cewa a cikin zuciyarta
"Ya dai azurtashi da matarsa Sumayya."mi'kewa tayi don fara aikace -aikacen gidan kamar yadda ta Saba kowace rana
Bayan ta gama komai ne amma bata gyara masa d'aiksa ba,don tasan yana ciki,kuma ba zata iya shiga yana ciki ba don tasan kila har yau bai huce ba.

Kitchen ta nufa don ta girka masu breakfast.

Bayan ta gama had'a breakfast d'in ne inda ta dama kunun gyad'a sannan ta soya k'osai,sai Indomie da ta dafa yare da dafaffen k'wai.

Fitowa yayi daga cikin d'akinsa ya nufi d'akinta don zuwa gaida Gwaggo,da sallama ya tare da tura k'ofar ya shiga, Gwaggo dake kwance ne ta mik'e ta zauna tare da amsa sallama r
"Barka da safiya Gwaggo"
"Yauwa barka dai ya kwanan iyali?"
Shiru yayi yana kallonta don shi dai kam baima sakasa a idonsa ba ballantana yasan ya ta kwana.yana son ya ma Gwaggo tamabaya shin ya akayi ne tabar Inteesar ta kwana tare da ita,bayan yasan cewa bata ta'ba barin ta kwana amma yau ta barta,sai dai yabar zancen kan cewa kila Gwaggo tabarta ne ta kwana tare da ita saboda ganin yadda ransa ya 'baci har yana Shirin dukanta ne yasa ta barta,don bata son abunda zai 'bata mata rai.

Daga nan sai ga Inteesar ta gama ayyukan da zata yi ta shigo,ido ya zuba mata ganin da fara'arta ta shigo amma tana kallonsa sai ta had'e fuska,kamar wacce bata ta'ba dariya ba a rayuwarta,tuna yadda yadda ganta a cikin mota da Usman tana ta masa dariya sosai,amma shi da ta gansa zata had'e fuska kamar taga mala'ikar d'aukar rai, jinjina kai yayi tare da maganar zuci tabbas sai yayi maganin yarinyar nan,badai tana tak'ama da Gwaggo bane nan zata tafi ta barshi da ita sai yayi maganinta.

"Gwaggo ga breakfast can a dinning table na kammala."
Jinjina kai Gwaggo tayi
"To 'yar albarka sannu da aiki."
Murmushi kawai tayi ta ce
"Yauwa Gwaggo"
"To kundai san bana da juriyar yunwa,to don haka ku muje muci da wuri ."
"Ta'be baki Inteesar tayi tare da cewa
"Gwaggo don Allah kuje ku fara ci,ni sai nayi wanka zanci kuma ba na Jin yunwa "
"Ke kenan kowane rana sai anyi da gaske kafin kici abinci?to kiyi sauri zamuje mu fara cin abincin ki tabbatar kafin nabar wajen cin abincin ki kinzo."
Kai ta jinjina Mata
"To Gwaggo"
Hannun Muhdeen taja suka fita daga d'akin,dagan Inteesar ta shiga wanka
Daga Gwaggo har Muhdeen ba Wanda yaci Indomie, dukkansu kunun gyad'a da k'osai suka ci, Muhdeen ne ya kalli Gwaggo ya ce,
"Yanzun Gwaggo sai ki dinga nuna mani wariya akan 'yarki ko?

Murmushi tayi tare da cewa
"Wariyar me zan nuna maka.?"
"Nagani kinfi son Inteesar akaina"
Dariya tayi kafin ta d'ora da cewa
"Waye ya fad'a maki haka?"
"Ai naga kin fifita soyayyarta akaina ne"
"Waya fad'a maka haka?ai gurbin ido ba idon bane,karka manta kaifa shalele na ne kafi sauran jikokina soyuwa a cikin zuciya ta."
"Ada kenan Gwaggo amma a yanzun dai kam kinfi son yariyar can a kaina,tun ranar da kika zo kika kyallara ido kika ganta shikenan."
"Gaskiya ka fad'a yariyar ta shiga raina sosai,kuma naga dacewarka da ita sosai ba kad'an ba,kuma inaji a jiki na ita ce abokiyar rayiwarka ."
"Jiya bata fad'a maki abunda tayi bane?"
"Ta fad'a mani gaskiya shine na ce da ta tarar da Ishaq baya nan me yasa bata dawo ta sanar ba ta tafi?sannan wanda ka gansu tare ba kowa bane face Usman Wanda ya kad'e ta da mota a kwanakin baya,shine wajen dawowa shi da k'anwasa suka rage mata hanya."
"K'arya ne Gwaggo,k'arya take maki,ba wata k'anwarsa da ido na gansu suzo Ubasanjo complex ina tsaye tare da manager access bank,ita da zata zo gida mai ya had'a ta da complex?sannan zata zauna tayi ta wage masa baki kamar mara kamun kai da aurenta."
"To yanzun dai kayi hak'uri ba zata sake ba."
Da misalin k'arfe goma sha biyu na rana motarsa tayi horn a k'ofar gidan Muhdeen,mai gadin ne ya bud'e masa,bayan yayi parking ne suka fito, Jabeer ya gaida mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan sannan ya shiga gaba Maryam na binsa a baya.

Knocking sukayi Inteesar ce dake kitchen taji k'arar kofar,tazo ta bud'e ganin Jabeer ne yasa ta saki fara'a.

"Yaya Jabeer Kaine?"
Ganin Aunty Maryam yasa ta fad'ad'a fara'arta
"Oyoyo Aunty Maryam ashe yau muna da manyan bak'i, bisimillah ku shigo mana."
Kai Jabeer ya girgiza tare da cewa
"Ni yanzun zan koma Ina da aiki,anjima zanzo na d'auke ta, Gwaggo na ciki ne?"
"Eh amma tana barci."
"Ba damuwa idan na dawo sai mu gaisa."
Daga nan ya koma ita kuma Inteesar ta janyo hannunta suka shigo cikin falon ta zauna, kitchen Inteesar ta koma ta kawo mata abun ta'bawa sannan ta koma kitchen ta cigaba da aikinta.

Tana cikin aikinta ne a kitchen sai ga Aunty Maryam ta shigo tasa hannu wajen taya ta aiki,duk da Inteesar ta hanata kan cewa bata da lafiya,amma sam tak'i amincewa dole ta barta sukayi tare.

Bayan sun kammala ne Gwaggo ta farka fitowarta yayi dai-dai da kammalawarsu,da mamaki ta kalli Aunty Maryam ta ce,
"Wannan ba matar Jabeeru bace."
Murmushi sukayi dukkansu inda Inteesar ta ce,
"Ita ce Gwaggo,ya kawota lokacin kina barci yace idan ya dawo sai ku gaisa."
Aunty Maryam ta gaida Gwaggo ta amsa tana 'yar tsokanarta,daga nan Inteesar taja hannun Aunty Maryam tana cewa
"Aunty Maryam mu shiga ciki kiyi sallah ko?"
Tare suka shiga bayan Aunty Maryam ta d'auro alwala ta fito ne, Inteesar ta ahiga don yin wanka,bayan ta fito ne ta sanya kaya tayi sallah,sannan suka fita zuwa falo.

A dinning room suka samu Gwaggo tana cin white rice and chicken soup,zama sukayi inda Aunty Maryam ta tsiyayi ruwa Inteesar ta zuba mata abinci sannan ta d'ebi nata.

Da yamma ne Jabeer yazo ya d'auke ta suka tafi gida.

Da misalin k'arfe goma na dare ne Inteesar tana Sanya rigar barci da niyyar zuwa d'ayan d'akin ta kwana,sai ga wayar Gwaggo tayi k'ara,tana d'agawa raji muryar Muhdeen na cew wai ta sanar da Inteesar ta kawo masa coffee a d'akinsa.gabanta ne ya fad'i don tasan yau Bata da ma'buya.

Bata da wani za'bi dole haka ta nufi kitchen ta dafa masa.

Hijabi tasa har k'asa tare da k'ok'arin cire tsoron dake ranta,tura k'ofar tayi tare da shiga da sallama tana shiga ya mik'e ya nufi k'ofar d'akin tare da murzawa k'ofar key ya zare key d'in daga jikin k'ofar,gabanta ne ya fad'i ganin wani irin murmushi akan fuskarsa Wanda bata ta'ba ganin ya mata shi makamancinsa ba.
Chapter 51 · 0% Book details