← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 99

Sashe 71

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy ce ta turo k'ofar ta shigo Dady na biye a bayanta, k'arasawa tayi kusa da Inteesar ta rungume ta hawaye tab a idanunta ta fara magana
"Sannu Daughter ya jikin naki?"
Take hawaye suka dinga ambaliya daga fuskarta kamr an bud'e famfo, Mummy tasa hannayenta tana goge mata hawayen tana cewa
"Ki daina kuka Daughter zaki samu lafiya, insha Allah komai zaizo k'arshe da yardar Allah."
Jabeer ne ya turo k'ofar ya shigo, ganin Inteesar zaune yass ya saki murmushi tare da cewa
"Alhamdulillah"
Kallonta yake yana cewa
"Ashe ta farfad'o"
Dady dai baisan me ya faru ba kuma baisan dalilin kwanciyarta Asibiti ba, kallon Mummy yayi tare da cewa
"Accident ta samu ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"Sai dai idan mun koma gida muji daga bakinta amma yanzun kam bansani ba."
Kallon Doctor yayi tare da cewa
"Yaushe za'a iya sallamarta?"
"Dama ba wani abu da zamuyi mata tunda ta farfad'o, sai dai ciwon kai da ba'a rasa ba, kuma zamu bata magungunan da zata dinga sha."
Fita yayi tare da sanar dasu yana zuwa
"Inteesar ce ta fashe da kuka tana cewa,
"Mummy dan Allah kada ku mayar dani gidan Yaya wallahi bazan iya jurar zaman gidansa ba."
Ta k'arasa maganar tana mai sake fashewa da wani sabon kukan, rungume ta Mummy tayi tana cewa
"Daina kukan haka nan ba zaki koma gidansa ba kinji? ki kwantar da hankalinki ba zaki koma can ba, haka Mummy ta dinga rarrashinta saosai har tsagaita da kukan da take, shi dai Dady abun ya d'aure masa kai, don baisan me ke faruwa ba, ganin yadda Inteesar ta rikice yasa yayi shiru yana jiran su koma gida.

A cikin mintuna talatin aka sallame su suka koma gida inda Jabeer ma ya bisu.

Da sallama suka shiga cikin falon Gwaggo tana zaune kan kujera tana kallon T.V Africa Tv3 inda suka saka wa'azin Shekh Jabeer Sani mai hula.

Amsa masu sallama tayi tare da zuba masu ido, ganin Inteesar yasa ta mik'a ta sauri tana salati
"Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku ni kuluwa me ya same ki 'yar albarka naga anbi an nannad'e maki kai da bandeji?"
Ba wanda ya iya magana cikinsu k'arasowa sukayi suka zauna yayin da Inteesar ta k'arasa wajen Gwaggo ta zauna a saman center carpet kusa da kujerar da Gwaggo take zaune, kallonta Gwaggo tayi tare da cewa
"Kada dai zargin da nake akanki ya tabbata, mijinki yazo nemanki ya ce baki gida kin fita kada dai a ce hakkinsa ne ya kamaki da kika fita ba tare da saninsa ba kika samu hatsarin mota naga an wani yi maki rawani da bandeji."
"Bayan sun zauna ne Dady ya kalli Mummy ya ce wai me ya same ta kuma ina mijinta?"
Mummy ce ta kalli Mufida ta ce,
"Ki fad'a masu abunda ta sanar da ke."
Gyara zama tayi ta sannan ta basu labarin irin zamantakewar da ke tsakanin Inteesar da Muhdeen da duk wahalhalun da tasha a gidansa a hannunsa da matarsa, komai sai da ta sanar da su kamar yadda Inteesar ta bata labarin komai ba abuda ta 'boye masu, da yadda Inteesar ta nuna cewa subar maganar a sirri kada ta fad'awa kowa.

Gaba d'aya Falon tsit sukayi kamar ruwa ya cinye su, ran kowa ya 'baci sosai da abunda Muhdeen ya aikata, tausayin Inteesar kawai ke cikin zuciyarsu musamman Gwaggo da ita ce sanadiyar had'in auren nasu, gani take ko wane hali Inteesar ta shiga ita ce ta jefa ta ita ce sanadiyar komai.

Dady ne ya kalli Inteesar ya ce,
"Mu a iya saninmu matarsa tana can London bamu san cewa ta dawo ba tana gidan ba, tun yaushe ta dawo k'asar?"
Cikin sanyin muryarta ta ce,
Tun ranar da Gwaggo ta bar gidan, don tafiyar Gwaggo kenan naji yana waya yana cewa zaizo ya d'auke ta, ya ce mani nayi girki na musamman zamuyi bak'uwa sai da tazo naga ashe ita ce."
Gwaggo ce ta fara magana
"Ke kuma da kina shashasha kika zauna yana wahalar dake da bautar dake ko? sannan har wannan matar tasa zata maidake baiwarta kina ji kina gani ko? ta kwanta da miji akan gado suyi abunda zasuyi su shiga toilet suyi wanka su fito, ke zaki shiga ki gyara masu gadon ki wanke masu toilet d'in ko?"
Ta k'arasa maganar cikin k'unar rai, kafin ta cigaba da cewa
"Allah ya wadaran naka ya lalace, Inteesar kin bani kunya, wai bata iya girki ba kece zata bawa umarnin ki dafa mata abunda take so, kiyi mata duk wani aiki, bata aikin komai sai dai ta ci ta Sha ta kwanta ko?"
K'wallar da suka cika mata idanu ne ta goge tare da cewa
"Ni na d'auka zaman aure nakeyi, kuma aure ibada ne, na kudirta cewa duk abunda ya umarce ni nayi zanyi shi ne matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba, saboda neman Aljannah ta nakeyi, kuma shine ya umarce ni da nayi mata duk..."
Wani tsawa ta daka nata tare da cewa
"Dalla rufe mani baki, tunda nake baki ta'ba 'bata mani rai irin na yau ba, me matar tasa ta fiki da shi kyawu ko kuma diri? ba abunda zata nuna maki wanda ta fiki da shi, wato shiyasa ranar da zan dawo nan ya dinga farin ciki yana Allah Allah na tafi ashe akwai abunda yake k'ullawa."
Dady ne ya kalli Inteesar ya ce,
"Wannan ciwon na kanki fa ya akayi kika jishi?"
Kuka ne ya k'wace mata nan suka dinga rarrashinta har ta tsagaita ta fara magana
"Ina kwane ina barci ne shine na bud'e Ido na naganta a kaina, da sauri na sauka daga gadon kawai sai naji saukar abu a kaina daga nan bansan komai ba sai da na farka na ganni a asibiti tare da Mufida."
Daga nan suka saka salati suna jimamin abuda ke faruwa, Dady ne ya ce,
"Anya kuwa Sumayya kanta d'aya?"
Murmushin takaici Jabeer yayi ya ce,
"Kafiyarta k'alau Dady ba abunda ya same ta haka take dama ba k'aramin aikinta bane ta illata mutum, shiyasa na sanar da Muhdeen kada ya had'a su gida d'aya bai saurare ni ba."
Sakin baki Gwaggo tayi tana kallonsa cikin mamaki
"Au dama yasan halinta shine ya had'a su gida d'aya dan ta illata 'yar mutane?"
Dady ne ya kalli Mufida ya ce,
"Tashi ki raka ta d'akinki tayi wanka ta ci abinci."
Mik'ewa Mufida tayi taja hannun inteesar suka shiga cikin d'akinta.

Jabeer ne yayi musu sallama zai koma wajen aikinsa, har ya kai bakin k'ofar ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa
"Koda kun had'u da shi kada ka sake ka sanar da shi tana nan gidan."
Kai ya jinjina alamar to, sannan ya saka kai ya fice abinsa.

Koda Jabeer ya isa asibitin ne ya sallami Umma inda ya ce zai jira su gama tattara kayansu ya kaisu gida, a motarsa ya zauna jiransu, Umman Inteesar ce sai k'anwar ta Mama Huraira, inda ya d'auke su a mota ya kaisu har k'ofar gida sannan ya juyo.

'Bangaren Muhdeen kuwa tunda ya koma gida sai faman safa da marwa yake yi, gaba d'aya ya rasa hankalinsa da nutsuwarsa, ganin yanayin da yake ciki da kuma tunawa da kalamansa da take ne yasa ta kama bakinta tayi shiru bata sake ce masa komai ba, wayarsa ya d'auka ya kira Jabeer, lokacin Jabeer na tuk'in mota ne yayi parking a gefen hanya tare da amsa kiran Muhdeen.

"Assalamu alaikum"
Muhdeen da ke tsaye a falo cikin tashin hankali ya fara magana
"Jabeer ka sallami su Umma ne?"
"Eh na sallame su, yanzun nan ma na kaisu gida na ajiye ina kan hanyar komawa ma yanzun nan"
"Ok su nawa ne ka kai gidan?"
"Su biyu ne"
"Wace da wace?"
"Umma ce sai k'anwar Umma wacce take jinyarta."
"Babu Inteesar a cikinsa?"
"Gaskiya bata tare da su."
"Jabeer akwai matsala wallahi, bansan inda Inteesar take ba na neme ta banganta ba."
Shiru Jabeer yayi kamar baisan komai ba ya ce,
"Ikon Allah, to Allah yasa ka ganta."
Daga nan ya katse kiran, yana shirin tada motar ne ya kuma jin wani kiran .

D'agawa yayi yaji muryar Muhdeen na cewa
"Jabeer magana fa nake maka mai mahimmanci, amma naga baka d'auki maganar serious ba."
"To banda addu'a me zan maka bayan wannan?"
"Haba Jabeer ai da sai kazo ka tayani nemanta muyi duk wani fad'i tashi da zamuyi ko Allah zaisa a ganta, dan Allah kazo gida na gani nan ina jiranka."
"Okay gani nan zuwa"
Daga nan ya katse kiran ya d'auki hanyar zuwa gidan Muhdeen.

Koda ya k'arasa gidan a falo ya same shi kallo d'aya tayi masa yaga har ya fita hayyacinsa, yana ganin Jabeer ya fare magana yana cewa
"Jabeer bata gidan nan kuma na je wajen Ummanta bata can bata je na na je gidanmu ko ta je wajen Mummy da Gwaggo duk sun tabbatar mani da bata nan, ta ina zan fara nemanta, Jabeer inacimin tashin hankali."
"Kallonsa yayi tare da cewa
"Kada ka damu kanka tunda dama ba wai kana k'aunar ta bane, to meye naka na damuwa tunda gaka ga Sumynka abar sonka da k'aunarka, ka manata da waccan kucak..."
Kafin ya kai k'arshen zancensa yaji Muhdeen ya kai masa naushi a baki har sai da bakinsa yayi jini, hankici ya ciro daga aljihunsa yakai wajen sai kuwa ga jini ya gani dariya yayi yana kallon Muhdeen da ke ta huci.
Chapter 71 · 0% Book details