Sashe 50
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai lafiyarki kuwa duk kinbi kin fita hayyacinki wa kika gani ne."
Bata ce komai ba duk da cewar tana dai jinsa ne amma hankalinta baya jikinta.
"To yanzun gidan da zan kaiki gidan waye?"
"Gidan yaya na ne."
Suna isa k'ofar gidan,ko sallama bata tsaya sunyi ba ta fita,da sauri ta tura gate d'in gidan ta shiga, murmushi kawai ya yana kallonta har ta shige sannan ya juya akalar motar yabar k'ofar gidan ba tare da sanin me ya tsoratata ba.
Tana tura gate d'in gidan mai gadin da mai baiwa fulawowi ruwa suna gaishe ta ma bata ji ba,da mamaki suke kallonta ganin yanayin da ta shigo.
Ita kuma idan ta tuna yadda ya murtuk'e fuska ne da wahalarsa da tasha a baya musamman idan ta tuna zafin marukan da ya ta'ba mata kafin suyi aure ne ya ke k'ara saka mata tsoronsa.
Dai-dai kwanar shiga layin gidan Usman na fita yayi gabas,sannan Muhdeen ya fito ta yamma,basu had'u ba.
Da sallama ta shiga cikin falon,ganinta a firgice yasa Gwaggo mi'kewa tare da fad'in
"Lafiya kamar wacce aka jefo?"
"Lafiya lau Gwaggo."
Girgiza kai Gwaggo ta yi tare da cewa
"To me ya firgita ki ne?"
Shiru ta yi tana tunanin ta ina ma zata fara
"Dama dama lokacin da zan tafi gidan rasuwar ne Ishaq Direba naje ya kaini aka ce baya nan 'yarsa ce ko matarsa ce ba lafiya na manta,shine naje na hau ada..."
Bata kai K'arshen zancen ta ba ganin yadda ka turo k'ofa da k'arfi,ganinsa ne kuma ita ya ke kallo tare da nufo inda take yasa ta daka wani tsalle aguje ta shige d'akinta ta murza key,tura k'ofara ya yi yaji ta a ride
"Idan baki bud'e k'ofar nan kin fito kin sanar da ni gidan ubanwa kika je da kuma wanda na ganki gaban motarsa wallahi sai kin tausayawa kanki."
Haka ya dinga dukan k'ofar kamar zai 'balle ta, Gwaggo ce ta k'araso wajen ta ke tamabayarsa.
"Kai Muhammadu lafiyar ka kuwa?kodai ka fara shaye -shaye ne ban sani ba?"
Maganar da tayi masa ne ya basa takaici don haka ya bar wajen ya nufi d'akinsa,don yaga alamar matuk'ar ta tsaya wajen Gwaggo zata iya sawa ya aikata abunda ba shi kenan ba, musamman idan aka ce akan Inteesar ce to fa zata iya 'batawa da koma waye akanta.
Kai tsaye d'akinsa ya nufa,zaciyarsa sai zugi yake masa zama yayi yana tunani,to waye wannan da take zaune a gaban motarsa,sai faman sakin murmushi da dariya take masa da alama taji dad'in kasancewarta da shi,zama ya yi yama nazari ina yasan fuskar wannan Mutumin?don Kan gaskiya ya ta'ba ganinsa a wani wurin,duk da dai yanzun bazai iya tuna inda ya gansa ko ya ta'ba saninsa ba,take sai ya tuno da Usman tabbas shi ya gani a k'ofar gidansu Inteesar suna fira,washe garin da aka sallamota daga Asibiti bayan Mummy da Gwaggo sun saka shi gaba kan tunda baije asibiti dubota ba yaje gidansu,zuwan da yayi ne yaganta tsaye jikin motar Usman shi da ita.
Zuciyarsa ce ta fara tafarfasa wato saurayinta taje wajensa kenan?tayi k'aryar zuwa ta'aziyya yayinda ta tafi wajen saurayinta,bayan ya ce ta nemi Ishaq ya kaita ya dawo da ita amma tak'i amincewa da ya kaita, toilet ya shiga don watsa ruwa.
Inteesar kuwa da taji alamar tafiyar Muhdeen ta kuma ji muryar Gwaggo ne yasa ta bud'e k'ofar,kallonta Gwaggo ta yi tare da cewa
"Me ke faruwa?"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bawa Gwaggo labarin komai,tun zuwanta kiran Ishaq Direba baya nan har yadda ta had'u da Usaman da Khadija suka matsa ta shiga motar har dawowarsu gida bata 'boye mata komai ba.
"To naji me yasa da Direban baya nan baki baki dawo kin sanar da mij
inki ba?"
Shiru tayi tare da cewa
"Bakomai Gwaggo naga yana da uzuri kuma ba lallai ya dawo a lokacin ba shiyasa na tafi,kuma wallahi Khadija ta matsa kan na shigo shiyasa na shiga motar."
Zuba Mata ido Gwaggo ta yi tare da tuna yadda Muhdeen ya bi ya damu da bak'in ciki ta shiga motar wani, murmushi ta sake a zuciyarta tana cewa kenan ya fara sonta ne tunda har yake kishinta murmushi ta yi tare da hamdala a zuciyarta.
Daga nan suka nufi kitchen tare dan d'ora abincin dare .
Daga can d'akinsa kuwa bayan ya fito wanka ya shirya ne wayarsa ta fara ruri,d'auka yayi tare da sallama,maimako a amsa sallamar sai jin kukanta yayi a cikin dodon kunnensa.
"Haba my baby me kuma ya faru daga kiran waya sai kuka."
"Haba tambaya ta ma kake?ya zun yaushe rabon da muyi waya?da kullun safiya sai ka kirani idan ka tashi daga barci amma yanzun shiru,kamar ma ka mance da ni ko?"
Ta k'ara sautin kulanta lokacin da takai k'arshen zancen,Wanda har Mum d'inta sai da ta shigo d'akin da sauri Jin kukan Sumayya,bayan shigwarta ne taga waya take da Muhdeen yasa taja tsuki ta fita,don lamarin Sumayya yanzun takaici yake bata.
"Kinga dain kukar nan haka please,ta yaya za'a ce na manta dake?ai idan na manta ki to nima zan iya mance kaina kenan."
Tsagaita kukan tayi ta ce,
"To kwana nawa kenan baka kira ni ba? sai dai ni na Kira ka kuma yadda muke dad'ewa muyi fira yanzun mun daina da mun fara zaka nuna gajiyawarka da ni wallahi hak'uri na ya fara k'arewa,wai yaushe wannan zaman nawa ya k'are?"
"Ya kusa saura sati biyi fah ba nisa mai Happiness."
"Kai a wajenka ne da nisa amma Ni waje na kmar nan da 2 years nake gani,ji nake kamar na janyo ranar tazo yau."
Murmushi yayi tare da cewa
"Ba zaki gane bane wallahi da kinsan halin da nake ciki na rashinki da kin tausaya mani wallahi,hak'urin zaman nake Dan ba yadda zanyi ne amma wallahi I missed you so much."
Sun jima suna fira kafin suka yi sallama
Da misalin k'arfe sha d'aya na dare ne Inteesar tana zaune akan gadonta, Gwaggo na falo tana kallon T.V shi kuma Muhdeen na d'akinsa,tunani take yanzun idan ta kwanta nan Gwaggo na zuwa zata tayar da ita sai taje d'akin Muhdeen dole,ita kuma tsoron zuwa take saboda laifin da tayi masa,tun lokacin da ya dawo ta shige d'akinta ta rufe ya buga bata bud'e ba,tun lokacin bata yarda ta had'u dashi ba sai a dinning table,kuma ta lura da irin kallon da yake mata,alamun yau idan kika shiga hannuna mai k'watarki sai Allah,tasan sarai bazai kyaleta ba yadda yadda taga ransa ya 'baci,bata gama tunaninba sai ga Gwaggo ta shigo da sallama
"Ke 'yar albarka me kike har yanzun baki tafi ba?"
"Wallahi Gwaggo tsoro nake ji."
Bata kI K'arshen maganar ba Gwaggo ta ce
"Sai da fafe Allah tashemu lafiya."
Gabnta na tsananta fad'uwa saboda tsoro,haka ta nufi bakin k'ofar tare da tunani da zullumin abunda zai biyo baya.
*KUYI HAK'URI DA WANNA WAYA TA CE TA SAMU MATSALA*
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Manan ihsa)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.
*JINJINA*
Jinjina ta musamman gare ku masoya na,na yaba kuma nagode da addu'ar da kuke mani Allah yabarmu a tare nayi wannan sharin tukuici ga masoyana na group d'in *INTEESAR* *HAUSA* *NOVEL* *GROUP* Ina jin dad'in comment da addu'o'i da kuke mani I love you lodi-lodi.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page4
___________Gabanta ne ya tsananta fad'uwa saboda tsoro, haka ta nufi bakin k'ofar tare da tunani da zullumin abunda zai biyo baya.
Tsaye tayi a falon kusan mintuna goma, ta rasa yadda zatayi, zuwa can sai ta tuna da d'aya daga cikin d'akunan dake nan cikin falonta, wato d'akin da aka gyara shima aka zuba mata furnitures komai na d'aki, don haka ciki ta shiga tayi kwanciyarta bisa godon bayan ta karkad'e gadon.
Shi kuma Yana can d'akinsa ya gama shirinsa na kwanciya barci, zama yayi Yana jiran shigowarta don yasan tabbas Gwaggo ba zata barta ta kwana a can ba sai ta turo masa ita, sanin hakan ne yasa ya zauna zaman jiranta.
Ganin har k'arfe goma sha biyun dare shiru ne yasa ya fara tunanin anya lafiya kuwa har yanzun bata shigo ba, mi'kewa yayi ya don shi a tunaninsa kila Gwaggo tana falo barci ya d'auketa ne bata san Inteesar na d'aki ba.
Yana zuwa falo yaga ba kowa don haka ya nufi dakin, ganin alamar cewa hasken d'akin a kashe yake alamun sunyi barci, tambayar kansa yayi mene ne dalilin da yasa Gwaggo zata barta ta kwana da ita?gaskiya bata kyauta masa ba haka nan ransa ba dad'i ya koma d'akinsa ya kwanta, duk da cewar ta 'bata masa rai amma hakan bai hana shi jin kewarta ba, ko ba komai yana jin motsin mutum a cikin d'akin.