← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 99

Sashe 2

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Ina jiranki kije ki dauko"
Bayan ta dauko ne suka tafi,Suna tafiya Mufida ta ce,
"kinji gobe Yaya Muhdeen zai dawo ko?"
" Wallahi nayi missing d'insa sosai"
Ta fadi Tana murmushi
Itako Inteesar tunda taji zai dawo kamar taji sak'on mutuwa don har ga Allah bata son dawowar shi saboda ya tsane ta,ba abunda ke hada ta dashi daga yadinga binta da mugun kallo sai kuma ya dinga galla mata harara indai Yana gidan nan bata da sake,ko gaishe shi tayi baya amsa mata sai dai idan akwai idan want wajen mummy ko Dady ko kuma Mufida.idan a gaban Asiya ne Kam baya amsa mata ko kallo bata isheshi ba.dayake Aasiyar ma basu jituwa da Inteesar.

Suka shiga gidan bakin su dauke da sallama.Umma dake cikin daki ne ta amsa masu,shiga sukayi suka gaishe ta.ta amsa masu cikin fara'a.

"Mufida yau kece a gidan namu?"
"Eh Umma naji Inteesar tace 'Dan wake kikayi shine nazo naci."
Cewar Mufida
Umma ta ce
"kema dai kina son 'Dan wake kamar Inteesar."
"To yana can nakai mata d'akin ta Don nasan sai ta dawo taci."
Mikewa sukayi suka fita suka nufi dakinIinteesar,suna shiga Mufida ta zauna kan katifar Inteesar dama d'akin Sai da tagyara shi fes tasa turaren wuta kafin ta tafi gidan Mummy
Plate Inteesar ta dauko ta zuba masu 'Dan waken tasa yaji da man kuli sannan ya yanka kabeji da cucumber da tumatur suka hau ci mufida nata santi,bayan sun kammala sun k'oshi mufita ta kishingid'a ta fara chatting'ita ko Inteesar fita tayi take ta fara Shirin 'Dora masu abincin rana.miyar taushe tayi sannan ta daura tukunyar tuwo,koda ta ahiga d'aki ta tarar mufida ta na barci murmushi tayi sannan ta fita,cikin kankanin lokaci tayi tuwon shinkafa zuwa karfe goma Sha biyu ta kammala komai ta tada mufida tace
"ki tashi har na gama girki gashinan idan zakici"
Mufida cikin yamutse fuska alamun barci bai ishe ta ba ta ce,
" me kika dafa?"
Kallonta Inteesar tayi tace tuw....."
Tun kan ta karasa ta ce
Wallahi bazanci tuwo da rananan ba."
Kasancewar Inteesar ma batajin yunwa kuma dama it ba Mai yawan cin abinci bane.ta ce.

"To tashi mu tafi"
Tare suka fito inda suka shiga sukayiwa Umma sallama suka tafi zuwa gidan su Mufida koda suka k'arasa Kai tsaye Inteesar ta nufi kitchen Don 'Dora abincin Rana.

Washe gari ranar da Muhdeen zai dawo kenan bayan sun gama breakfast mummy tasa Inteesar da mufida Sud'an Kara gyara masa d'aki.dama Shima ya hana ma'aikatan gidan suna shigar masa d'aki.

Koda suka shiga mufida zama tayi kan side drawer'intesar ta zage ta gayra d'akin ta goge ta wanke masa toilet sannan suka fita,dama d'akin Mummy da na su Mufida Maimuna mai aiki ke gyara masu da fallo
Kai tsaye Inteesar ta nufi kitchen Dan taga mummy ta shiga abinci lafiyayyu kala-kala aka shiryar don tarban Muhdeen bayan sun gama sunyi wanka karfe daya na Rana suka nufi airport dan tarban sa, Direban su biyu suka dauki motoci guda biyu inteesar bata so zuwa ba amma da mummy ta matsa mata dole taje, Mummy ta shiga bayan d'ayan motar Inteesar da mufida daya .

Suna Isa jirgin su na sauka,ya fito daga jirgin rik'e da akwatin sa da fara'a suka karasa Mufida ta rungume sa tana masa barka da sauka,bayan ta sake shi ya rungume Mummy tare da cewa
"Imiss you mum"
Murmushi tayi tare da cewa
" miss u to."
Inteesar ce ta kalleshi ta ce,
"Sannu da dawowa ya muhdeen"
"Wani kallo ya mata ganin idon Mummy ne ya sa ya amsa
"Yauwa"
Kai tsaye suka nufi motocin su inda Mufida ta dage sai motar su zai shiga haka akayi kuwa ya zauna gaban motar, da
Yana hada ido da Inteesar ta jikin madubin motar ya watsa mata harara,da sauri ta sunkuyar da Kai k'asa.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u ollFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & written by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.

Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Page0
Yana hada ido da Inteesar ta jikin madubin motar ya watsa mata harara,
Da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,Direba yaja motar suka bar airport d'in suka nufi hanyar gida,yayin da motar da Mummy ta shiga ya rufa masu baya.

Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu gate din gidan.bayan sunyi parking direban ya zagayowa da sauri ya budewa muhdeen mufin motar ya fito,yayin da Direban ya dauko kayan da muhdeen din ya dawo dasu daga cikin boot d'in motar,yayin da Mufida da Inteesar suka fito daga cikin motar,mummy ce ta riko hannun Muhdeen cike da son gudan jinin nata,langwa'bar da Kai yayi alamun gajiya.

Murmushi mummy tayi tare da cewa ,
"Ka gaji ko"
Kai ya gyad'a mata alamar Eh,hannun shi taja suka nufi kofar shiga part din,yayin da su Mufida suka rufa masu baya,ita dai Inteesar jikin ta duk yayi sanyi kamar an Jefi kaza da gishiri.

Kai tsaye Mummy ta raka shi har part d'insa,har bedroom suka shiga yayin da direban ya ajiye kayan a falon sa.

Mummy ta ce,
" kayi wanka ka fito Muna jiranka muci abinci."
kai ya gyad'a yayin da mummy ta fita taja masa k'ofar ta nufi folo inda ta samu Inteesar da Mufida, itama falon ta zauna fuskar ta dauke da murmushin farin ciki.

Cikin kankanin lokaci Muhdeen ya k'araso falon sanye yake cikin kananun Kaya farin Riga da bakin wando 3 quarter, Mufida ce taja hannunsa tana murmushi suka nufi dinning area din Mummy ma ta Mike tabi bayan su tare da cewa Inteesar ta taso suci abinci.

"Mummy bana Jin yunwa anjima zanci"
Mummy ta dakata tare da juyowa tana kallon ta da mamaki,Don tasan cewa tun suna girki take cewa Tana Jin yunwa amma yanxun kuma tace bazataci ba sai anjima.

"Ina ce yunwa kike ji sannan yanzun kice bazakici abinci ba,taso ko kadan ne kici .

Har ga Allah tana son cin abincin amma kuma tsoron Muhdeen d'in da takeyi ne yasa bazata iya zama dasu taci Abincin ba.mufida ce tace,
"Inteesar Dan Allah ki taso Mana
tana Shirin mikewa ne taji muryar muhdeen Yana cewa
"Ki kyaleta mana tunda tace bazataci ba ko zaki matsa mata dole ne?ba tafiku sanin cikin ta ba?"
Mummy bata Kara cewa komai ba taja hannun Inteesar din suka nufi dinning area din kujera taja mata kuje
ran dake facing d'in Muhdeen ta zaunar da ita kauda kansa yayi bayan ya jefa wata Mata mugun kallo,
Mummy ta shiga bude kulolin abincin ta fara zuba masa nasa.fried rice ne da yaji hanta da Koda,sai kuma farfesun kajin da Inteesar tayi masu,ta zuba masa juice din kwakwa da Madara Wanda Inteesar din ce ta hada.ta kalli Inteesar tace,
"'yata me zaki ci?"
Cikin sanyi ta ce
" ruwa kawai zansha"
Ba tare da mummy tace komai ba ta zuba mata jallop din cuscus ta ajiye mata a gaban ta tare da ajiye mata kofin juice a gaban ta,ta juya ta kalli Mufida ta ce,
"Ke kuma ki tashi ki zuba abunda kike so,
Kulan cuscus d'in a gaban ta.ta zuba a plate ta balle murfin robar ruwa ta zaba a cup Mummy ma nata ta zuba ta fara ci bayan ta zubawa Inteesar farfesun kajin.

Inteesar gaba d'aya ta kasa sakewa taci abinci yadda kowa ya sake yana ci,gabanta sai fad'awa yakeyi musamman irin kallon da Muhdeen ke jifanta dashi.

Shima kansa a cikin zuciyar sa ya rasa gane dalilin da yasa ya tsani yarinyar,shidai wulak'anta mutane ko kuma kyarar mutane ba dabi'ar sa bace, amma baisan dalilin da yasa ya tsani yarinyar ba.Gashi dai Kullun zata baro gidan iyayen ta taxo gidan su tana taya mahifiyar shi aikace-aikacen gida, gashi tana son dangin shi jininta ya had'u da autar su Mufida amma duk lokacin da yarinyar ta shigo gidan sai yaji gaban sa ya fad'i,ga kuma yawan mafarkin da yakeyi da ita kusan kullun,ko sumayya masoyiyar shi da suka kwashe shekaru biyu suna soyayya baya mafarki da ita sai wannan mayyar,sunan da yasa mata kenan mayya.

Yana cin Abincin sa yana tunani kuma gashi yaji dadin abincin sosai don gaskiya Inteesar ba baya bace wajen iya girki.ta kware sosai shiyasa Mummy kullun sai ta jira ta tazo kafin ta d'aura girki,don suna Jin dadin abincin ta sosai.

Mummy ce ta zuba mata ido tana nazartar yanayin ta
"Inteesar lapiya kuwa me yake damun ki?"
Daga kai tayi ta ce
"Lafiya qalau mummy"
"To meyasa bakici abincin kirki ba kinsaka abinci a gaban ki sai jujjuya cokali kikeyi
dakyar taci cokali uku tasha ruwa ta koma falo kan kujera ta zaina,
Mummy dai shiru tayi tare da binta da ido
suka cigaba da cin Abincin su
Muhdeen sai da ya koshi ya Kora da juice din kwakwa sanna ya Mike tare da cewa
"Mummy bari na huta"
"To son a huta gajiya sai ka fito."
Mufida ce ta ce
"Yaya tsaraba ta fa?"
Murmushi yayi tare da cewa
"anjima idan na huta sai na fito maku da tsarabar ku"
Kai tsaye ya nufi hanyar part din sa da sauri Inteesar ta sunkuyar da Kai k'asa Don bata San sake kallon sa,sai da ya wuce sannan ta daga Kai.
Chapter 2 · 0% Book details