← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 99

Sashe 40

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda ta saba k'arfe hud'u na asuba ta farka,wanka ta tashi ta yi ta d'auro alwala tazo ta yi nafila kamar yadda ta saba,daga nan ta fara karatun al qur'ani kamar yadda ta saba,sai da loacin sallar asuba ta yi sannan ta tashi ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar da sallar ta yi azkar da addu'o'i sannan ta Fara ayyukan gidan kamar yadda aka kafa mata doka.

Da misalin k'arfe goma sha biyu na rana ya fito raga cikin d'akinsa,sanye yake da shadda sky blue sai hula neavy blue da ya sanya a kansa da bak'in takalmi a k'afarsa da tsadaddan agogo dake d'aure a hannunsa,ya biyo ta falon Inteesar zai wuce tana zaune tayi tagumi, Jin takunsa yasa ta d'aga kai ta kalle sa sai da ya k'araso ta durk'usa ta gaishe sa.

"Ina kwana?"
Ko kallonta baiyi ba ballantana ya amsa mata,ta cigaba da cewa.

"Ga breakfast na shirya can na shirya maka."
Nan ma shiru ganin yana k'ok'arin fita ne yasa ta ce,
"Adawo lafiya"
Dakatawa yayi tare da jefa mata mugun kallo.

"Wai ke wace irin mayya ce?kinyi magna d'aya ban amsa maki ba,ba sai ki kyaleni ba?"
Tsuki yaja tare da ficewa,wayarta ce ta soma ringing,duban wayar tayi ganin Mummy ce yasa ta sakin murmushi ta d'aga kiran.

"Assalamu Alaikum"
Daga can 'bangaren Mummy ta ce,
"Wa'alaiki salam Daughter ya hak'uri?"
Murmushi ta yi
"Alhamdulillah Mummy."
"Masha Allah"
'Dan jim ta yi kafin ta d'aura da cewa
"Daughter"
"Na'am Mummy."
"Kuna dai lafiya ko?"
"Lafiya lau Mummy"
"Ki fad'a mani gaskiya naji muryarki wani iri,idan akwai matsala ki sanar dani,kinsan Ni na haife sa idan akwai bunda ya ke maki wanda baki so ki sanar dani."
Sahiru Inteesar ta yi ta kasa magana,ganin kamar akwai want abu da Inteesar ke son 'boyewa yasa Mummy cewa,
"Ina son d'in ya ke"
"Ya fita yanzun nan."
Da zai fita ina ya ce maki zaije?"
"Bai sanar dani ba."
Shiru Mummy ta yi kafin ta ce,
"Ki shirya yanzun nan zan kira shi zai dawo ya d'auke ki,zai kai ki giadanku ki gaida Ummanki sannan ya kawoki gida na."
Cikin jin dad'i Inteesar ta ce,
"To Mummy Nagode sosai sai nazo."
Dagan nan ta kashe wayar ta ajiye a nan kan kujera,sannan ta nufi d'akinta cikin tsananin farin ciki.

Muhdeen kuwa yana tsaka da driving Mummy ta kirasa nayan ya d'aga a cikin bada umarni ta yi magana.

"Son ka koma gida ka je ka d'auko matarka ka tafi da ita ta gaida mahaifiyarta da mahaifinta kaima ka gaishe su,daga nan sai ku taho nan gidan."
Bata jira mai zaice ba ta katse kiran.

Dole ya juya akalar motar don kawa gida,dan yau da kansa ya ke driving ba kullun ya ke fita da Direba ba.

Koda ya koma gidan bata nan a falo don haka ya nufi d'akinta,ita kuma lokacin ta fito daga wanka kenan tana d'aure da towel iya rabin cinyarta ya rufe gashin kanta da suka jike da ruwa kafad'arta,tana goge suman kanta dai-dai lokacin da ya shigo d'akin da niyyar yi mata masifa,mutuwar tsaye yayi lokacin da yayi arba da ita,tundaga k'asan k'afarta ya fara kallon zara zaran yatsun k'afarta da suka sha zanen filawowi masu kyau,a hankali yake d'aga k'wayar idonsa har zuwa santala santalan cinyoyinta farare masu kyalli da d'aukar ido,surar jikinta masu Jan hankali ya ke kallo gashin ya zubawa ido kamar na wata ba'indiya hand dryer ta d'auko ta kunna ta fara busar da gashin kanta,bayan ta gama ne ta fara k'ok'arin zare towel d'in da ta d'auka ne ta hango shi tsaye ta cikin mirror,cikin zafin nama ta maida towel d'in ta d'aura tare da janyo dogon hijabinta ya saka,ta'be baki ya yi ya fara magana cikin muryarsa da ta sark'e ya ce
" ki same ni a mota."
Daga nan ya saka Kai ya fice daga d'akin,ita kuma ajiyar zuciya ta sauke tare da hanzarin shiryawa.

Yana fitowa falo wayarta dake saman kujera ta Fara ringing,kallon wayar ya yi yaga sunan wanda ya Kira ta,Usaman shine sunar da ya bayyana akan wayar,bai kula ba ya fice abinsa.

Yana zaune cikin motarsa ya na jiranta, danne-danne ya ke a wayarsa,ta k'araso sanye take da abaya kalar lemon green ta sa hula ba'ki a ciki kafin ta yafa gyalen,ta yi simple makeup tana ri'ke da posanta da wayarta a hannunta,bak'in takalmi flat shoe ta saka,abayar na d'aya daga cikin kayan da ya siya lokacin da suka tafi Dubai da Sumayya had'o lefe inda kayan suka burgesa ya za'besu ita kuma Sumayya ta ce bata son kayan duk abunda ya burge wani baya burgeta,shi kuma sai ya kawo wa k'annensa Asiya da Mufida Mummy ta cirewa Inteesar wasu daga ciki,son shi dama kayan sun masa.

Bud'e murfin motar tayi ta shiga tare da masa sallama,a zuciyarsa ya amsa sallamar,zama tayi ba tare da tayi magana ba,shiru yayi har tsawon mintuna goma bai ja motar sun tafi ba kuma bai ce komai ba,ganin bai da niyyar tafiya ne ya sa ta ce,
"Yaya na gama."
Shiru ya d'anyi kafin ya fara magana.

"Dama kina da baki shine kika zauna mani shiru a mota kamar kurma?"
Yaui maganar ba tare da ya kalle ta ba,zuba masa idanu ta yi tana mamaki wani irin mutum ne shi wannan?sai da fa ta masa sallama Bai amsa ba amma wai ya na cewa kamar kurma,shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

"Bari kiji na fad'a maki wani abu d'aya,idan muka je gidanku ko gidanmu aka tambaye ki yanayin zamanmu kika kuskura ki ka sanar dasu halin da muke ciki da ke wallahi sai na lahira ya fi ki jin dad'i,ki nuna masu ba komai a tsakaninmu muna zaune lafiya cikin jindad'i,kuma bari kiji wannan d'ari d'arin da kike Dani ki ajiyeshi tun yanzun kuma a nan ki saki jikinki dani sosai ki nuna masu ba wata matsala a tsakaninmu,ki nuna muna jin dad'i da k'aunar juna,bari na fad'a maki meye ma sunanki?"
Kallonsa tayi tare da cewa
" sunana Inteesar"
Jinjina Kai ya yi tare da cewa
" koma dai wace ce na fad'a maki wallahi kika kuskura suka tambayarka kika sanar dasu zaman da muke yi dake,iya ka dai sai dai suyi mani fad'a,ke kuma idan muka dawo gidan nan Ni kad'ai nasan hukuncin da zan yanke maki,idan kunne ya ji jiki ya tsira,ina fatan kin gane?"
Kai ta jinjina tare da cewa
"Eh na gane"
"Good,sannan magana ta k'arshe naji Gwaggo wai zata zo nan gidan tayi 1 month to da zaran ta maki zancen ki nuna mata cewar ba sai tazo ba tunda kinzo ta ganki."
Da sauri ta kalleshi,dan Allah ya sani ba zata iya fad'awa Gwaggo haka ba,amma sai ta amsa masa da kawai.

Kunna motar ya yi tare da yin horn inda mai gadi ya wangale masa gate ya bar gidan.

Suna tafiya a gefen ya yi kwana ya tsaya a gaban wani tafkeken super market,yana gama parking yana k'ok'arin fita daga motar yaji an k'wank'wasa gilashin motar, sauke gilashin ya yi sai yaga shila k'awar Sumayya ri'ke da waya a hannunta, murmushi ta sakar masu tare da cewa
"Barka da warhaka amarya da ango."
"Shila kece ya kike?"
Kallon Inteesar ta yi tare da watsa mata harara sannan ta ce,
"Amarya ta ango ya cin amarci?"
Inteesar ta kalleta tare gaishe ta
"Ina wuni?"
"Lafiya lau ya kike"
"Alhamdulillah"
Harara ta watsa mata a fakaice tare da cewa
"Da alama amarya tasa an mance da Sumayya ko?"
Ajiya zuciya ya sauke
"Ba haka bane shila abun ne ya fi k'arfina ba yadda na iya ne,kuma ita da iyayenta sun d'auki zafi Amma na da few days komai zai dai daita."
Jinjina kai tare da yi masu sallama ta bar wajen,shi kuma fitowa ya yi ba tare da ya kalli Inteesar ba ya fita daga motar.

Bayan wani mintuna sai sai ji tayi ana zuba kaya a but d'in motar,karin aka rufe ya zagayo ya zauna ya ja motar suka bar harabar wajen.

Bai tsaya ki ina ba sai k'ofar gidansu Inteesar,ganin ya yi parking k'ofar gidansu ya sa ta sakin murmushi mai sauti,Wanda har sai da ya kuyo ya kalleta,cikin farin ciki tayi yun'kurin bad'e motar amma sa taji ya yi lock d'In motar,juyawa ta yi da niyyar masa magana sai ta ga ya had'e fuska ba annuri a fuskarsa,hakan yasa ta turo baki ta cigaba da zama cikin motar,sai da kwashe mintuna bakwai kafin ya ce,
"Ki shiga ki sanar da su tare muke."
Bayan ya yi unlock d'in motar,fita tayi ta nufi cikin gidan,tun a zauren gidan take kwalawa Ummanta Kira.

Umma!

Umma!!

Umma!!!"
Da sauri ta fito daga d'aki jin muryar tilor 'yarta,A guje Inteesar ta k'arasa jikin Ummanta ta rungumeta sai hawaye kawai ke fita daga idanunta
"Ummana nayi kewarki sosai,ta kwantar da kanta a kafad'ar Ummanta hawaye kawai ke tsiyaya daga idanunta,kusan mintuna uku suna a haka kafin Umman nata ta janyeta daga jikinta tare da Jan hannunta suka shiga cikin d'akin,Kan gadonta Ummanta ta zaunar da ita,zuba mata ido tayi ganin duk ta rame da alama bata cikin kwanciyar hankali,alamu sun nuna haka amma ko mene ne zata nemi Jin ta baki 'yarta, tasan halin da take ciki,don sanin cewa ba auren aoyayya bane na had'i ne.

"Umma ina kwana?"
"Lafiya lau Inteesar ya kike?"
"Alhamdulillah Umma"
"Ya mijin mai gidan naki?"
Sai a lokacin Inteesar ta tuna cewa yana waje.

"Umma muna tare ya ce nazo na sanar dake kafin ya shigo."
"In banda abunki shine da kika shigo baki sanar dani ba?"
"Farin cikin ganinki ne yasa na mance da shi,ina Abba ya tafi kasuwa ko?"
Murmushi Umma ta yi tare da cewa
Yana kasuwa amma idan zaki dad'e ne har zai dawo ya tarar dake,ki je ki shigo da mijin naki ko?"
Mi'kewa Inteesar tayi ta fice daga d'akin duk wanda ya kalli fuskarta yasan tana cikin farin ciki.

Yana zaune a cikin motarsa ya d'an kishingid'a,idanunsa a lumshe kamar mai barci,sallama ta yi masa a zuciyarsa ya amsa har sau uku tana masa magana amma shiru bai amsa ba.
Chapter 40 · 0% Book details