Sashe 9
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nuna ta Gwaggo tayi da yatsa tace
"To ita wannan yarinyar da na gani wallahi na dauka ita ce matar da zai aura, saboda sun dace da juna sosai, wallahi it ace ta dace dashi ba waccan tambad'ad'd'ar karuwar ba.
Mummy ce ta kalle ta tare da cewa,
"Gwaggo wannan fa zargi kikeyi baki da masaniyar cewa karuwa ce, zato kike kuma kin san ance zato zunubi koda ya kasance gask..."
Bata karasa ba Gwaggo ta nuna ta da yatsa tana fad'in
"Ke Fatima a hir dinki ki fita a idona na runtse, idan ba karuwa ba wace ce ita?
Ki nuna uban irin kayan da tasa gaba daya surar jikinta a bayyane suke wannan suturar dake jikinta marabar ta da babu kusan daya ne, hata kirjin ta kusan rabinsa waje suke, ga uban gashin dokin da aka kara mata kamar na sabuwar mahaukaciya ga wani kwalliya dake fuskarta kamar na aljannu".
Mufida ce tayi dariya tare da cewa
"Ke Gwaggo Ina kika taba ganin kwalliya Aljannu"
Harara Gwaggo ta watsa mata tare da cewa,
"Ke kiyi mani shiru ba dake na ke yi ba da uwarki gata nan zaune, da ita nake".
Sannan ta ci gaba da magana tana cewa,
"Yanzu na fahimta wato duk isakanci da suke aikatawa da daurin gindiki suke aikatawa, ni dai bazaku jawo wa dana masifa da bala'i yana zaman zamansa ba".
Murmushin takaici tayi sannan tace,
"To ni meye nawa a ciki me sukayi na daure masu gindi Gwaggo?"
Jinjina kai Gwaggo tayi tare da cewa
"Lallai ma zaki ce me sukayi?
Yanxun ganin idona na gansu nike da juna kamar zasu shige jikin juna kafin yasa ta a mota suka fita.
Allah ya dawo da ubansa wannan kama bata dace da matar da yakamata a aura ba"
INTEESAR ce ta Mike tare da cewa,
"Mummy bari na tafi dama aiki nakeyi nace bari nazo mu gaisa da Gwaggo".
Gwaggo ce tayi saurin janyo hannunta tace "Allah sarki 'yar nan kin tafi bamu gaisa ba?"
Durkusawa tayi cikin girmamawa da sanyin muryarta tace
"Ina wuni?"
Washe washe baki tayi kamar ba ita ta gama sababi ba, tace,
"Lafiya kalau 'yar nan, ya kike?"
"Alhamdulillah", Inteesar ta amsa Mata.
Gwaggo tace
"Masha Allah. ya sunan ki?"
"Sunana Inteesar"
Shiru Gwaggo tayi tare da cewa
"Too wannan sunan naki da wahala wai isitas"
"Ba Inteesar kadai ba hatta Mummy da Mufida sai da sukayi dariya, Mufida harda kwanciya.
Sakin baki Gwaggo tayi tana kallonsu
"To meye nayi na dariya da zaku tasa ni gaba daga nayi magana kamar mahaukaciya".
Mufida ce tace
"Gwaggo ba fa isitas aka ce ba Inteesar"
Tabe baki Gwaggo tayi tace
"Ni kam bazan iya ba"
Daga nan Inteesar ta tafi gida.
Gwaggo ta kalli mufida tace
"Ita wannan yarinyar daga Ina take?" Mufida ce ta bata labarin Inteesar tun daga ranar da direban Mummy ya kade ta da mota har rana irin ta yau.
A b'angaren Muhdeen da SUMAYYA kuwa suna cikin mota duk yadda yayi kokarin rarrashin ta kin sauraren shi tayi a haka har suka isa gida nan ma haka yayi ta bata hak'uri amma ina bata saurare shi ba, dole ya kyaleta idan ta sauka zuwa gobe zai dawo ko zata saurare shi.
A can b'angaren Gwaggo kuwa Dady na dawowa ko ruwa bata bari yasha ba, ta Fara basa labarin irin abunda idanunta suka gane mata, ta kara da cewa "sai dai Muhdeen ya fasa Auren Sumayya".
Dady ne ya numfasa yace
"To Gwaggo meye hujjar ki da kike kiranta karuwa? kin ganta a wani wurin ne, ko kuma kallon da kikayi mata yasa kika gane cewa karuwar ce?"
Gyara zamanta tayi akan kujera sannan tace,
"Ahaf na nawa kuma? yarinyar da kayan jikinta kusan tsirara ne ko idonta a tsatstsaye alamun na rashin kunya da rashin sanin darajar mutane, da kake tamabaya ta ko na ganta a wani wurin ne to a cikin gidan ka suke badalar su ganin idona na gansu nanike da juna kamar zasu shige jikin juna, yadda na gansu Allah yasa naga annabin rahama, ko mai gadin gidan nan shaida ne, saboda haka ban yarda ka aurawa danka wannan yarinyar mai kama da busasshen crayfish ba".
Shiru Abba yayi tare da ciro wayarsa number Muhdeen ya lalubo ya kirasa, bugu biyu ya daga.
"Assalamu alaikum"
Daddy yace
"Wa'alaika Salam kana Ina ne?"
Shiru Muhdeen yayi kafin yace
"Ina hanya"
"To idan ka iso ka sameni a falona".
Daga nan ya katse kiran tare da aje wayar.
Muhdeen ne jikinsa yayi sanyi don ya san tabbas wannan kiran bai rasa nasaba da Gwaggo.
*KUYI HAK'URI DA WANNAN*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.
Page 11
_________Cikin sanyin jiki ya fito daga cikin motar kamar wanda aka zarewa lakka a jikinsa.
Kai tsaye part din Dady ya nufa, inda ya tarar da Dadyn da Mummy da kuma Gwaggo, da sallama dauke a bakinsa ya shiga falon, Dady da Mummy ne kadai suka amsa masa sallamar ya yin da Gwaggo ta ta'be baki tare da cewa,
"Ga iya sallama rangada sallama kamar na Allah, ya yin da Allah kadai yasan barnar da ta'asar da yake aikatawa a bayan idon al'umma, ka dai dinga jin tsoron Allah ana tunawa da mutuwa yara sai shegen jarabar tsiya".
Harara ya gallawa Gwaggo tare da Jan tsuki
Cikin daga murya Gwaggo tace,
"Bani kayiwa ba uwarka kayiwa gata nan zaune".
Ta karasa maganar tana nuna Mummy da yatsar ta manuniya.
Ko kallon ta bai yi ba ya karasa gabansu ya zauna kan center carpet din falon, ya kalli Dady yace
" Ina wuni Dady?"
"Lapiya qalau"
Ya amsa
Sai ya kalli Mummy zai bud'e baki ya gaisheta kenan sai ta daga masa hannu alamun dakatarwa.
Sunkuyar da k'ai kasa yayi yana jiran mai zasu ce masa yana fargabar abunda zai biyo baya, tunda Gwaggo tayi masa mugun fahimta kuma Don tun kafin ya bar gidan ya ji sallallami da kalamanta.
Muryar Gwaggon ne ta katse sa daga tunanin da ya ke yi,
"Kada Allah yasa ka gaisheni Mana, wadan da suka haifeka sun gaishe Ni d'an banza mai jajayen kunnuwa".
Shi dai bai tanka Mata ba, saboda idan suna gaban Dady da Mummy bai cika kula ta har ya bata amsa ba.
"Muhammad mai kake aikatawa ne haka?
Wani irin labari naji Gwaggo Tana fada da yasa raina ya sosu, ahe kai mutumin banza ne ban sani ba eye?"
Dago Kai yayi ya kalli mahaifin nasa ya Fara magana kamar haka
"Amma Dady wallah..."
Dakatar da shi Dady yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yace,
"Kai ma kasani Gwaggo ba za ta yi karya ba, idan har bata ganku ba ba za ta fada ba".
Gwaggo tace
"Da karyatani za ka yi? mutumin banza da idona na ganka manne da kuna ka rungume ta kana sumbatarta Amma zaka karyatani, to uwarka ka karyata bani ba".
Muhdeen da ransa ya gama baci da abunda tsohuwar ke fada ya kalli Dady cikin rawar murya yace,
"Dady Don Allah ka bani dama nayi magana kafin ka yanke hukuncin da zaka yanke.
Zuba masa ido yayi na d'an lokaci, domin shi ma kansa yasan irin tarbiyar da su ka yi wa 'ya'yansu ba tarbiyar banza ba ne, sannan baya jin d'an nasa zai aikata kazamar dabi'a, ga gefe daya kuma ya san Gwaggo mahaifiyarsa ce ba za ta yi masa
arya ba, cikin sanyin murya yace,
"Ina Jinka Muhammad Fadi abunda kake son fada",
Muhdeen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ba wa Dady labarin duk abunda ya faru tun daga kiran da Gwaggo tayi masa Yana office tace kar na dawo gida sai yazo Mata da matar da zai aura, da yadda ya d'auko ta da irin cin mutunci da Gwaggo tayi mata.
Shiru yayi kafin ya cigaba da fadin,
Kuma Dady wallahi tunda nake a rayuwata ban taba rike koda hannun wata mace wacce ba muharrama ta bace, ko ita Sumayya da Gwaggo take magana akan ta na rungume ta yanayi ne yasa haka, ganin irin kukan da takeyi na d'aukota har gida na kawo ta anci mata mutunci har da Mata kazafin karuwanci, gashi ranta ya 'baci ta fita tana kuka taki ta saurareni ne sai na d'an rungumeta da sigar Rarrashi kamar yadda kasan Ina rarrashin Asiya da Sumayya idan suna kuka ina son na rarrashesu to hakan ne ya faru tsakanina da ita, kuma maganar cewa na sumbaceta ba sumbatar ta nayi ba rarrashinta nakeyi ta hanyar fada mata kalamai masu sanyaya rai a cikin kunnenta, wallahi Abba ban taba sunbatarta ba".
Shiru Abba yayi Don ya fahimci Dan nasa, cikin sanyin murya Abba yace
"To shi ke nan naji Amma ka kiyaye kada makamancin wannan ya sake faruwa".
Jinjina k'ai yayi tare da cewa "insha Allah"
Mummy dai shiru tayi don bata da ta cewa.
Dady ne ya kalli Gwaggo yace "to me kike son ayi yanzun?".
Gyara dan kwalin ta tayi sannan tace,
"Ni dai ban yarda ya auri wannan tambad'ad'd'yar yarinyar ba ehe, sai dai ya nemo 'yar mutunci yo wannan wace tarbiyya zata ba yaran da zasu Haifa?
Don ko ita tana bukatar tarbiyya".
Wani irin kallo Muhdeen yayi wa Gwaggo, ya bude baki da nufin zai maida mata martanin maganarta, Mummy ce ta yi masa kallo mai cike da gargadi hakan yasa yayi shiru ba tare da ya furta kalaman da yayi niyyar fada ba.
Dady ne yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli Gwaggo cikin girmamawa ya Fara magana
"Yanzun haka Gwaggo idan kika ce fasa Auren nan bayan ni da Yaya Adam da Aminaina mu ka je har gidan iyayen yarinyar nan muka nema masa Aurenta, sun girmamamu da mutuntawa suna muna kallon dattako da kamala, suka dauki 'yarsu suka bawa d'anmu anyi komai an saka rana nan da watanni biyu masu zuwa sannan yanzun muje muce mun fasa aurawa d'anmu 'yarsu munyi masu adalci kenan?".
Gwaggo dai ta'be baki tayi tare da cewa;
"Uhum".