← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 99

Sashe 84

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Assalamu alaikum"
Mummy da Sumayya suka amsa mata
"Wa'alaiki salam"
"Mummy ya jikinsa?"
"Jiki da sau
i Mufida"
"Allah ya bashi lafiya."
Suka amsa da Ameen, Mummy ce ta kalle ta ta ce,
"Baki ga Auntynki bace?"
Yamutshe fuska tayi tare da cewa
"Mummy ni banga Aunty na anan ba gaskiya."
Kallon garga
i Mummy tayi mata ba tare da ta ce komai ba, sanin dalilin kallon ne yasa ta kalli Sumayya murya ciki ciki ta ce,
"Ina wuni?"
Itama kanta Sumayya taji zafin abinda Mufida tayi mata, amma sai ta dake ta nuna hakan bai dame ta ba kasancewar a gaban Mummy suke,
"Lafiya lau Mufida ya kike?

Kauda kanta gefe tayi tare da cewa
"Lafiya"
Dan tunda suka je gidan Muhdeen da Gwaggo lokacin Sumayya na Amarya har tayiwa Gwaggo rashin kunya, tun daga wannan lokacin Sumayya ta fice daga zuciyar Mufida, ganin lokacin salla yayi ne yasa Mummy cewa zata tafi tayi sallah, Mufida ma tabi bayanta suka fice, sai a lokacin Sumayya ta samu dama ta kira Jumy take sanar da ita halin da ake ciki na hatsarin Muhdeen, daga can
angaren Jumy ta ce
"Anya
awa ta babu sa hannunki a hatsarin nan kuwa?"
"Na san halinki nasan abunda zaki iya aikatawa ."
"Dariya Sumayya tare da cewa
"Tabbas kinyi gaskiya ba abunda bazan iya aikatawa ba, amma ki sani wannan hatsarin masa ba saka hannuna a ciki, ai kinsan idan in son mutum bazan iya cutar da shi ba matu
ar kuwa kika ga na cutar da mutumin dake
aunata to ha
a ya kainii bango ne wanda hakan shine masalaha."
e baki Jumy tayi tare da cewa
"Ba wata masalaha da sai an halaka wani, nifa nan da kika ganni duk iya shige da isakanci na wallahi bazan iya yin kisan kai ba."
"Hmmm ba'a kaiki bango bane wallahi da ankaiki bango da ba zaki da
i haka ba, sannan lokacin da zaki aikata hakan ma ba zaki sani ba, nayi yun
urin kashe Inteesar a baya ta tsallake rijiya da baya, amma matukar ta kaimu bango to fa wallahi bazata sha ba, don idan raina ya
aci ko zuciyata bana saurara duk abinda yazo gaba na aikata shi nake."
"To ki guji ranar da zakiyi nadama kuwa wanda lokacin nadamar ba zata maki amfani ba."
Maganganun Jumy ba suyi mata ba dan haka ta katse kiran tare da kiran lamabar wayar shila, bugu biyu shila ta
auka suka gaisa zancen da yayiwa Jumy ita tayiwa Shila, sai dai shila tunzura ta ta dingyi akan duk abinda ta ce zata yi, a haka sukayi sallama ta kashe wayar .

Sai da akayi sallar isha'i ne su Mummy suka dawo bayan sunyi sallar isha'i, Sumayya tana nan zaune bata tashi ta je sallah ba.

Da sallma suka shigo
akin ta amsa masu, a tunanin Mummy Sumayya bata je. sallah bane saboda kada a bar Muhdeen a
aki ba kowa dan haka ta kalli Sumayya ta ce,
"Sumayya tunda mun dawo idan zakiyi sallah ki tashi kije kiyi ko."
Dai lokacin Gwaggo da Inteesar ta suka shigo
akin, Sumayya ta mi
e tare da cewa
"Bari na tashi naje nayi sallah to."
Kai Mummy ta jinjina tare da cewa
"To sai kin dawo."
Daga nan ta fice Gwaggo ta raka ta da harara, Mummy tayi magana cikin sigar lallashi ta ce,
"Gwaggo don Allah ki fita harkar yarinyar nan, tunda yanzun dai bata sake wani laifi ba."
Gwaggo ta nuna Mummy da yatsarta manuniya ta ce
"Fatima ki kiyaye ni fa ki fita a ido na na rufe, saboda ba ke tayiwa na mi tayiwa rashin kunya da fitsara, ai idan mayar ya manta ai uwar
a bai ci ta manta ba, kina cewa wai bata sake wani laifin ba sannunki kenan, amma wannan yarinya duk inda kike neman kaba'ira takai."
Ita dai Mummy bata ce komai ba har Gwaggo ta
araci sababinta tayi shiru.

Jabeer ne ya shigo da sallama gaishe da su Mummy da Gwaggo yayi yayinda Mufida ta gaishe sa,zama kusa da Gwaggo ya ce,
"Ke wannan tsohuwar ba zaki tafi gida ki huta ba?"
Kai ta girgiza
"Ina naga tafiya ga miji kwance ko motsi baiyi ba."
"Kada ku damu ina sa ran insha Allahu ya kusa farkawa"
Mummy ce ta kalli Mufida ta ce,
"Ki dubawa yayanki abinci mana"
Mufida ta tashi da niyyar zuba masa abincin yayi saurin cewa
"Am okay"
Dan haka Mufida ta koma ta zauna inda Jabeer ya cigaba da cewa
"Yanzun magana cin abinci Mummy."
Sumayya kuwa tunda ta fita da sunan zatayi sallah sallah ta zauna gefen masallacin, tana tunanin ta ina zata fara, dan ko sallar asuba barayi na ballantana azahar da la'asar, wayarta ta ciro ta kira number Bashir bugu biyu ya
"Hello Sumy ya akayi ya farka ne?"
"Tukunnah dai bai farka ba tukunnah"
"Okay nan zaki kwana Asibitin ne?"
"Wace ni da kwana a Asibitin alhalin wannan fitina miyar tsohuwar na nan ai ba mu zama inuwa
aya, gida zan koma da safe na dawo."
"Okay ko nazo na taya ki kwana ne"
Da sauri ta furta
"What's"
Dariya yayi tare da cewa
"Wai sai na maye gurbinsu tunda baya nan ko?"
"Kasan me kake fa
a kuwa? kazo gida na ka kw
ana bayan ga mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan zasu ganka ka kwana bayan abokinka baya nan? me zasauyi zato?"
a baki yayi tare da cewa
"To ke kizo mana ki same ni idan har ba nan zakai kwana ba ba wanda zai san inda kika kwana, su a nan zasu
auka gida kika je kika kwana su can ma gidan zasu
auka asibiti kika kwana ba wanda zai sani."
Shiru tayi tana nazari kafin ta ce,
"Shikenan sai nayi tunani amma idan kaji ni shiru to ka tabbatar a Asibitin zan kwana tare da mijina."
"Hmm ai naga dole zaki fi bu
atata saboda zanyi maki amfani a daren yau shi kuma fa meye zai tsinana maku?"
"Kaga kada fa ka za
e da yawa dan zaka iya fuskantar tirjiya daga gare ni, kuma duk son da nakeyi maka baikai wanda nake masa ba, i love him more than everything dan haka kada ma kayi tunanin ha
a kanka da shi dan ya fika ta kowace fuska."
"Kada ki nemi gaya mun maganar da zuciyata ba zata iya
auka ba."
Tsuki tayi tare da kashe wayar
Tashi tayi ta je ta jero dalilin da ake binta tun daga asuba har isha'i.

Bayan ta idar ne ta koma
akin ta samu suna cin abinci, Mummy ta kalle ta ta ce,
"Sumayya kin idar da sallar ko?"
"Eh Mummy"
Zama tayi ta fara daddanna wayar ta, Mummy ta kalli Mufida ta ce,
"Ki zubawa Sumayya abinci mana"
"To Mummy"
Daga nan ta janyo Basket d'in da aka jera abincin tare da ciro plate ta zuba mata abincin, ta ha
a mata da ruwan sha, kar
ar tayi don dama yunwa take ji sosai.

Suna gama cin abincin ne Inteesar wacce rabin hankalinta na wajen Muhdeen ta lura da ya fara motsi yana juya kai tare da yamutshe fuska.

Cikin tsananin farin ciki ta ce
"Ya farka"
Gaba
aynsu suka maida hankalinsu ga Muhdeen, gani sukayi yana juya kai amma idanunsa a rufe, da sauri suka
ara da wajen gadon Jabeer ya ri
o hannunsa tare da kiran Sunansa.

"Muhdeen sannu ko"
Ba tare da ya bu
e idanunsa ba ya amsa da yauwa, Sumayya ta ce
"Sannu ya jikinka?"
Ba tare da ya bu
e idanunsa ba ya ce,
"Yauwa"
Sai a lokacin Inteesar tayi magana ta ce,
"Sannu yaya ya jikin?"
Jin saukar muryarta a cikin dodon kunne da yasa ya bu
e idanunsa da sauri dan tabbatar da abinda kunne da ya jiyo masa, idanunsa ne suka sauka akan nata yaga tana sakar masa murmushi, zuba mata ido yayi don tunda yake da ita bata ta
a yi masa murmushi ba sai yau, gani yake kamar ba gaskiya bane mafarki yakeyi dan haka sai ya mi
a hannunsa ya ri
o nata hannun, cikin muryarar da bata fita ya furta
"Inteesar kece?"
Kai kawai ta gya
a masa tana murmushi ba tare da tayi magana ba, sun kai mintuna biyu zuwa uku suna kallon juna suna sakarwa juna murmushi, kowa kallonsu yake yana murmushi sa
anin Sumayya wacce ba
in ciki da takaici duk ya ishe ta, ta gaishe sa amsawa yayi ba tare ba tare da ya ko kalle ta ba, amma daga jin muryar Inteesar ya bu
e ido ba shiri sai kallon juna suke kamar zasu ha
iye junansu,
arin tashi zaune yayi yana cije le
e har lokacin hannunsu na ri
e da juna, Gwaggo ce ta ce,
"Muhammadu ya jikinka?"
Kai ya jinjina tare da cewa
"Da sau
i Gwaggo"
Nan ma Mummy da Mufida suka gaishe su ya amsa masu, Jabeer ne ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo da kofin shafi ya bashi da
yar yasha sannan Jabeer ya bashi magani yasha.
Chapter 84 · 0% Book details