← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 99

Sashe 16

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba d'ayan su suna zaune a dinning room suna dinner Dady, Mummy,Gwaggo,sai Muhdeen,suna zaune kowanen su nacin Abincinsa Amma banda Muhdeen dake jujjuya cokalin ya kasa cin komai,tunanin halin da Sumayya ke ciki yake, Gwaggo ce ta ta'be baki tace,
"Indai tunanine bakama Fara ba yanzun zaka saka 'kafar wando dashi, matu'kar kace wannan mahaukaciya zaka aura,"
Baice Mata komaiba cikin son kawar da zancen yace,
"Mummy Wai har yanzum Mufida bata dawo gida ba?kuma fa har Kiran wayarta nayi nace ta dawo Amma ta kasa dawowa"
Dady ne yayi magana yace,
"Ta kirani ta sanar dani can gidan zata kwana,tayi jinyar Inteesar sai gobe da safe zata dawo tayi Shirin zuwa school, kuma an amince mata"
Shirin Muhdeen yayi Don baiso hakan ba Amma tunda Dady ya amince dole tasa ba yadda za'ayi dole ya hakura sai dai yace,
" In Banda abunta meye na wani kwana a gidan mutane,nifa Sam hankalina baya kwanciya da irin haka"
Gwaggo tayi saurin cewa,
Idan Kai hankalin ka baya kwanciya mu namu Yana kwanciya,tunda tare da Mai cikakken hankali zata kwana,bada Mai cutar kwakwalwa ba ballantana muyi tunanin kada tayi barci mahaukaciyar ta illata muna ita,"
Ta karasa maganar Tana Kai lemu a bakinta, Muhdeen ransa ya 'baci Don yasa magama take fad'a masa a fakaice wato Sumayya ce mahaukaciyar ,Bai gama tunanin da yakeyi ba ya koma jiyo muryarta Tana fad'in,
"Ina tausayawa mijin mahaukaciya"
Take Muhdeen yabar wajen ransa a 'bace don Yana shakkar Dadyn sa ne kada yaha yanayiwa mahifiyar sa rashin kunyar,da badon haka ba da yaayar Mata da amsa.

Kwanci tashi ba wuya a wirin ubangiji,yau su Inteesar da Mufida suka kammala jarabawar su ta kammala secondary School,kuma yau ne ya rage saura sati biyu bikin Muhdeen da sumayya,kuma yaune Muhdeen da Sumayya zasu dawo daga 'kasar Dubai inda sukaje had'a kayan lefen Auren su,don sumayya for ta'ki yadda Wai Muhdeen ko waning nasa ne zai siyo Mata kayan lefe,ta dage dole sai dai suje Dubai ita dashi su siyo kayan lefen acan,haka duk kayan da Muhdeen ya za'bar Mata zatace ita bayyi Mata ba,sai dai ta za'bo wasu kayan daban ,a cewar ta abunda ya burge wani baya burge ta,Koda ta d'auko kaya taga Muhdeen ya yaba kayan zata mayar dashi,akasarij kayan da d'auka duk Basu kwanta masa ba Amma ba yadda zaiyi da ita,Haka suka cika akwatuna goma Sha biyu da kaya hatta sarka da d'an kunne na Gold ita ta za'ba.koda taga ya siyo wasu dogayen rigunan abaya kala daban-daban masu kyau tace Bata son kayan da zasu takura ta,ya nuna Mata cewa 'kannensa ya siyawa Asiya da Mufida Suma ya cika masu Babbar jaka da tsaraba har da Mummy da Gwaggo duk ya masu tsaraba.koda suka dawo yake nuna masu kayan lefe Mummy dai cewa tayi Allah Sanya alkhairi, Gwaggo ne dai tace Allah wadarai da wannan kayan Don Bata ga kayan arziki a wajen ba.

'Bangaren Inteesar kuwa kamar yadda tayi alwashi hakan ne ta kasance, bata sake taka 'kafafuwar ta zuwa Gidan su Muhdeen ba ko kafin su gama Exam idan ta shirya zata tsaya kan hanya ta jira har sai Mufida da direban Mummy yazo tabisu ko Mummy da Gwaggo sun kirata zata kirkiri abinda zata fad'a masu da zai hanata har sun gaji sun kyaleta.

Mufice ta kawo Mata Atamfofi da less da material na ankon bikin tace suje wurin tailorn da Mummy ke kai masu d'inki haka kuwa aka yi ta sallami Umma suka wuce wurin Hamza Tailor, bayan sun za'bi irin wanda suke so ne sukayi masa sallama suka tafi, don dama Mummy ce zata tura masa Kud'in,
Har zasu shiga mota inda direba ke jiran su sai Inteesar ta hangi wani makaho ya taho Kan titi da 'yar sandarsa Yana dogarawa ga Mota na zuwa a bayan sa,ba tare da tayi tunanin duna janya ba tahau titin a guje kafin ta ankare bisa tsautsayi sai ji tayi mota ta kad'eta ta Fadi akan titi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta ta shi dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.

Page 1
Ba tare da tayi tunanin duba hanaya ba, kafin ta ankare bisa tsautsayi sai ji tayi mota ta kad'eta ta fad'i kan titin, Mufida dake can gefe ce ta kwalla mata kira.

"INTEESAR!!!"
Ta karaso a guje ya yin da matu'kin motar da ya kad'e Inteesar Shi ma ya karaso direban Mummy sai salati ya ke yi, ya yin da Mufida ke kuka kamar ranta zai fita ganin 'kawarta kwance a sume, rungumeta tayi ya yin da wata mata dake wajen ta d'auko Inteesar d'in ta saka ta bayan motar mutumin da ya kad'eta, jin yana cewa ad'auko ta su tafi asibiti, da sauri Mufida ta shiga bayan motar tare da janyo Inteesar ta rungumeta idonta na zubda hawaye Direban Mummy ne ya shiga gaban motar don baikamata ya barsu su tafi da mutumin da bai sansu ba.

Tafiya kad'an sukayi suka 'karasa wani private hospital dake unguwar, parking yayi tare da fitowa da sauri ya hangi masu wasu ma'aikatan asibitin kiran su yayi sai gasu da hanzari sun d'auko gadon tura marasa lafiya, bayan an kwantar da ita suka wuce da ita ya yin da suka rufa masu baya.

Bayan an shigar da ita d'akin an kwantar da ita bisa gado sai ga doctor da nurses biyu a bayansa, Doctor d'in ne ya umarci su Mufida da su fita su jirasa a waje, fita sukayi Mufida dai har yanzu bata daina kuka ba, saurayin da ya kad'e Inteesar ne ya kalli Mufida yace,
"Ki kwantar da hankalinki ki daina kuka in sha Allah zata samu lafiya"
Kai ta gyada masa ba tare da tayi magana ba, ta nufi kujerun dake wurin ta zauna akan d'aya daga cikin su tare da yin tagumi, Ishaq direban su ne ya kalleta yace,
"To ni bari naje na d'auki mota na tafi na sanar da su Mummy"
Kallaonsa tayi tace,
"To"
Saurayin da ya kad'e Inteesar dai Yana Nan tsaye wayar Sa ya Ciro daga cikin aljihun sa ya lalubo number mahifiyar sa ya shiga Kiran layin.

Wata dittijuwar mata ce Mai kimanin shekaru hamsin tana zaune akan a falon ta, Kan d'aya daga cikin lafiyayyun kujeran dake falon,wayar ta CE to soma ringing dubawa tayi ganin d'anta ne ke Kira yasa ta d'aga da sauri tare da cewa,
"Babana har yanzun baka 'karaso ba?"
Ajiyar zuciya saurayin ya sauke cikin sanyin murya
yace,
"Mummy na samu accident ne"
Zumbur ta mi'ke da sauri Tana fad'in,
"Subhanallahi Babana me ya same ka?

Kana Ina ne?"
"Ba abunda ya sameni wata yarinya ce na kad'e da mota na kawota aaibiti"
Cikin damuwa ta furta kalmar,
"Inalillahi wa'inna ilaihir rajiun,wane asibitin kuke"
"Muna nan asibitin Top medical dake tunga"
Bata 'kara cewa komaiba ta ajiye wayar tare da 'kwalawa autar ta Kira.

Khadija!

Khadija!!

Da sauri matashiyar budurwar ta fito hannunta d'auke da wayar ta,kafin tayi magama matar tace,
"Kiyi sauri yanzun Nan ki fito zamu tafi asibiti yayanki ne ya kad'eta wata yarinya da mota"
Tana kaiwa 'karshen maganarta ta nufi d'akinta,
Ba jimawa tafito dai-dai lokacin da itama Khadija ta fito rataye da handbag hannunta ri'ke da makullin motarta,suka nufi kofar fita.

Inteesar cikin 'kan'kanin lokaci ta farfad'o, kasancewar ba wani rauni taji sosai ba,buguwa ne da 'kujewa tayi,bayan doctor ya fito ya basu damar shiga su ganta kwance suka sameta, Mufida na ganinta ta saki murmushi a guje ta karasa jikin ta fad'a jikin ta ta rungumeta,ganin yadda Inteesar ke cije le'be yasa Usman wato saurayin da ya kad'e Inteesar yace,
"Ki d'an saketa kamar Tana Jin zafin rungumar da kikayi Mata"
Sakinta Mufida tayi tare da zama gefen gadon Tana murmushin ganin jikin Inteesar d'in da sau'ki, Inteesar ce the d'aga idonta ta kalli Usman suna had'a ido ya sakar Mata wani lallausan murmushi,da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,Jin muryarsa tayi yace,
"Sannu ko, ya jikin naki?"
Ba tare da ta d'ago ta kalleshi ba tace,
"Da sau'ki"
Murmushi yayi tare da cewa,
"Allah ya baki lafiya ya kiyaye gaba"
Mufida ce ra amsa da,
"Ameen ya rabbi"
Suna cikin Haka aka turo 'kofar aka turo 'kofar aka shigo d'akin,kusan a tare suka shigo Gwaggo,Mummy,sai Umman Inteesar,suna shigowa sai ga Ammy mahifiyar Usman da 'yarta Khadija ne suka shigo d'akin.

Gwaggo ce ta ri'ke hannunta cikin tausayawa tace,
"'Yar Albarka Garin yaya hakan ta faru?nidai nasan kina da nutsuwa ba laifinki bane,yanzun haka tu'kin ganganci ne direban Nan yayi ways sani ma ko d'an shaye-shaye ne yasha ya bugu Yana neman illata maki illata muna ke,in bandama..."
Bata Kai aya ba Mufida ta Kira sunan ta ganin zatayi 'baran 'barama ga Wanda ya kad'e Inteesar a wajen kuma ba mashayi bane yadda Gwaggon ke fad'a,Hasalima Inteesar ce Mai laifin don itace tahau titin dai-dai motar na kawowa,duk da cewa ita ceton rai tajeyi ganin makaho zai hau titin gashi ba idone dashi ba,dayake tsautsayi akanta yake ba'a kad'e makahon ba ita aka kad'e.

Mufida ce tace
"Haba Gwaggo ki daina yanke Hukuncin abunda bakida masaniya akansa,bakisan yadda Abu ya faru ba ki dinga bincike"
Gwaggo ce ta galla Mata harara tare da cewa,
"Dalla rufewa mutane baki magananniya na'ki nayi bincike,kuma duk Wanda ya kad'e Inteesar sai Allah ya..."
Cikin sauri Usaman yace,
"Mama Don Allah kiyi Ha'kuri nice na kad'eta bisa tsautsayi,kuma ba yadda kike tunani bane Allah ne ya 'kaddaro hakan zata faru ba makawa sai ta faru,KU gafarceni Don Allah"
Gaba d'ayan su zuba masa idanu sukayi suna kallonsa.
Chapter 16 · 0% Book details