← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 99

Sashe 24

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama Direban Mummy ne zai kaisu Mufida idan ya dawozai Kai su Mummy.suna Isa harabar gidan wayar Mufida ya fara ruri dubawa tayi taga yaya jabeer ne,d'agawa tayi taji muryarsa yana cewa sun tafi dinner ne? tace suna gida yanzun zasu tafi,ya tamabayeta Inteesar, ta sanar dashi cewa tare zasu tafi ya ce wai Inteesar ta sameshi waje yana cikin motarsa zai wuce da ita dinner d'in.Daga nan ya kashe Mufida ta zubawa wayar idanu Tana mamakin me ya Jabeer yake nufi?baice suzo ya kaisu ba Wai Inteesar tazo wato daga shi sai ita kenan.Kallon Inteesar tayi ta ce,
"Tafiyarmu da ke ba d'aya bane,ya Jabeer Wai kije ya kaiki."
"Babu inda zanje ya kaini sai dai idan tare zai kaimu da ku."
Dariya Mufida tayi tana fad'in
"Ai bada mu ya ce ba ke kad'ai ya ce."
Kauda Kai Inteesar tayi ta dage bazata je ba.Jin shiru yasa ya sake kiran wayar Mufida ta shaida masa yadda sukayi.Sai gashi ya zo da kansa yace da Azeeza da Azeema su shiga motar haka ma Mufida yasa ta shiga daga nan ya ce da Ishaq yaja motar su tafi.Inteesar na gani motar ta fice tsabar takaici kamar tayi kuka.kallonta yayi yana cewa
"Kizo mu tafi lokaci na tafiya fa."
'Dago ido tayi da niyyar ce masa ta fasa zuwa,amma da ta kalli cikin idanunsa sai taji ta kasa masa gardama,haka nan ta bishi har suka fita Murfin motar ya bud'e mata ta shiga,ya rufe sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa.kasancewar haske ne gab d'aya kofar gidan yasa ya zuba Mata ido,domin tasaha kyau har ta gaji.tsawon mintuna biyu taji shiru yasa ta d'ago ta kalleshi,ganin yadda yadda ya zuba Mata ido ne yasa ta d'aga kai ta kalleshi,idanunsa ne suka sark'e cikin na juna da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa murmushi yayi tare da Jan motar yabar wajen.

Akan hanyarsu ta zuwa kuwa du yadda Inteesar taso share Jabeer hakan baiyuwu ba.Domim da ya dinga janta da hira yaga bata tanka masa ba sai ya dinga yi mata tambayoyi yadda dole sai ta dinga amsa masa.shima dama burinsa kawai yayi ta Jin muryarta.A haka suka k'arasa JUSTICE IDRIS LEGBO KUTIGI inda nan ne za'a gabatar da dinner party d'in, a harabar wajen wajen suka tarar da su Mufida suna jiran K'arasowar su Inteesar d'in yayinda Mufida sai d'aukar photo da video take kasancewar gurin haske ne ya gauraye shi tamkar da rana ne.Tana ganin K'arasowar su Inteesar ta maida d'aukar zuwa ga gurin motar yayinda Jabeer ne ya Fara fitowa yayi saurin zagayowa da nufin bud'ewa Inteesar ta fito sai dai kafin ya bud'e Mata tayi saurin bud'ewa ta fito tare suka k'araso wajen ta kalli Mufida tana murmushi ta ce,
"To sarkin d'aukar photo ko dare ma ba zaki bari camera ta huta ba?"
Jabeer dai ya nufi cikin hall d'in inda za'a gudanar da shagalin.

Hall d'in ya cika mak'il da jama'a 'yan uwa da abokan arziki wasu ta hanyar amarya wasu ta hanyar ango.Nan dai amarya da ango suka k'araso cikin shiga ta alfarma sunyi kyau sosai.Wedding goun d'in amaryar irin Mai sirrin hannun nan ne kamar singileti sai jan k'asa rigar take ta bayanta ya sauka yayinda fuskarta ke lullu'be da farin net gaban rigar anyita kamar breezier.Yayinda shi kuma ya saka fararen suit.

Su Hajiya Gwaggo kuwa tana ganin shigar ta Fara salati tana tafa hannu,Aunty Maryam dake zaune gefenta ne ta kalleta tare da tambayarta
"Gwaggo lafiya me ya faru?"
Rik'e ha'barta tayi tana jujjuya Kai tana cewa
"Oh ni,yau naga abunda ya isheni."
Anty Maryam ne ta same tambayar Gwaggo ta ce,
"Wai Gwaggo ne kike ma sallallami haka?"
"Wai ke mairo ke makauniyar ina ce?ki duba wasu 'yan isakan tsinannun rgar da wannan amaryar tasa,duk surar jikinta a bayyane,ki duba gaban rigar harda gidan da mamanta zasu zauna akyi su,gashi sun zauna ciki kowa na ganin shaidar su ga rigar ko hannu Bata dashi.Wani abun takaicin Wai matar aure kenan,tunda d'azu jama'a da yawa sun shida d'aurin auren su.Gab d'aya rayuwar yahdawa suka d'auko.shi kuma da yake mijin hotiho ne da baya kishin matarsa shine ya barta ta fito a haka,ace mutum sam baida kishi kamar Wanda yaci naman alade."
Aunty.

Maryam ce da wasu k'awayen Mummy suka saka dariya.Nan dai aka Fara gudanar da komai cikin tsari inda aka wak'e ango da amarya,aka kira dangin amarya inda suka fito suka cashe sukayiwa ango da amarya lik'i.

Bayan dangin amarya sun koma ne aka kira dangin ango nan suka fito harda Mummy da su Anty Maryam da k'anwar Dady da Mummyn Jabeer da su Gwaggo da Asiyya da Mufida, Azeema, Azeeza hatta Inteesar sai da Mufida ta janyota Jabeer ma ya fito Nan aka shiga lik'e-lik'en nairori da raye- raye anci ansha sannan aka tashi kowa ya watse.

Da misain karfe goma da rabi na dare ne amarya tana zaune a Kan gado,sanye take da wani less golden yellow Mai ratsin fari a jikinsa doguwar riga ce dakyar k'awayen Mum d'inta suka lalla'bata ta yadda take saka,don ita ba ma'abociya Sanya suturar kirki bane.yayinda k'awayenta su Jumy da shila je zaune a gefenta suna ta mata tsiya suna tsokanarta.

Ango da abokansa ne suka shigo cikin d'akin.Muhdeen Ango Yana sanye da farar shadda da Babbar riga sai k'amshi ke tashi a jikinsa.Salisu na rik'e da ledar kaji da fresh milk a hannunsa,da sallama suka shiga d'akin Su shila ce suka amsa masu.Nan dai akayi siyen baki inda abokan ango suka wuce da k'awayen amarya.Ko rakiya bai masu ba suna ta tsokanarsa suka wuce.haurawa yayi Kan gadon ya yaye mayafin yadda zai ga fuskarta dakyau.Murmush take tayi domin burinta ya cika na auren Muhdeen kullum fatanta kenan tana sonsa sosai.kitchen ya nufa ya d'auko plata da kofuna guda biyu ya k'araso ya bud'e ledar, kaji ne bank'ararru guda biyu sunji gashi Mai kyau kuwa.d'aya ya d'auka yasa a plate d'in ya tsiyaya fresh milk a baki ya dinga bata tana ci tana shan fresh milik d'in har ta k'oshi.ya kwashe kayan ya Kai kitchen sannan ya dawo ya umarceta da ta shiga tayi wanka ta d'auro Alwala suyi sallah daga nan ya fice zuwa d'akinsa.

Zuciyarta cike da farincikin mallakarsa a matsayin mijinta, mi'kewa tayi ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet don yin wanka.Bayan ta fito ta goge jikinta ne da k'aramin towel,ta shafa lotion da turare ta saka riga da wando na barci don dama ta d'auro alwala hijab kawai ta saka ta shimfid'a masu sallaya tana zaman jiransa
Zamanta bada jimawa ba ya shigo sanye da farin jallabiya a jikinsa.Jansu sallah yayi inda sukayi raka'a biyu,bayan sun idar ya dad'e yana masu addu'a kafin suka shafa.Goshinta ya rik'e tare da addu'a kafin suka nad'e sallayar.Zama tayi bakin gado yayimda shi kuma ya haura saman gadon light d'in d'akin ya kashe kafin ya cire jallabiyar jikinsa.

"Bakyajin barci ne kika zauna?ko gadina kike yi?"
Kwanciya tayi daga d'an nesa dashi,janyota yayi zuwa jikinsa kai tausassun le'b'bensa yayi a kan goshinta ya sunbaceta a goshi.Lumshe Idanuwanta tayi sakamakon jin tausasan le'b'bensa a goshinta tsintan kanta tayi cikin wani irin yanayi na nishad'i.Shafar gefen fuskarta yayi har zuwa kan wuyanta a hankali ya fara 'balle boturan gabar rigarta kasa hanashi tayi cikin hikima ya rabta da komai na jikinta tare da sumbatar kowane sashe na jikinta.A hankali yake shafa sassan jikinta tare da yi Mata tafiyar tsuka, wani abu Sumayya takeji tun daga tafin hannunta har tsakiyar kanta,la'b'banta kuwa sai tsotsonsu yake kamar ya samu sweet.A daren dai sai da ya mayar da Sumayya cikakkiyar mace.

Daga Alk'alamin
Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)
09065327995
Love u oll
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta cowace siga.

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa.

Page2
Wani abu Sumayya takeji tun daga tafin hannunta har tsakiyar kanta, la'b'banta kuwa sai tsotsonsu yake kamar ya samu sweet.A daren dai sai da ya mayar da Sumayya cikakkiyar mace.

Bayan awa d'aya ya samu nutsuwa ne ya janyota ya rungume yayinda take ta matsan k'walla.Toilect ya shiga ya had'a mata ruwan wanka sannan ya taimaka mata ta tashi ya kaita toilet inda sukayi wanka.

Shi da kansa ya yaye zanin godon inda ya shimfid'a masu wani.ya janyota jikinsa nan da nan barci ya d'aukesu.

Kiran sallar asuba ya farkar dashi daga barcin da yakeyi.Tashi yayi ya nufi d'akinsa, toilet ya shiga ya sake watsa ruwa ya Sanya jallabiya ya biya ta d'akin Sumayya ya tayar da ita domin tayi sallah.Masallaci ya nufa,sai da aka idar da sallah ya dawo.Kai tsaye d'akinta ya nufa ganinta yayi tana barci da dukkan alamu ma bata tashi tayi sallah ba.Tashita ya sakeyi domin har gari ya fara haske dakyar ta tashi ta shiga toilet,Don bata saba sallar asuba ba ko a gidansu idan tana barci ba'a tashinta idan tana barci ko lokacin sallah ne kuwa,don sallar ma sai taga dama takeyinta idan bata ga dama ba kuwa sai dai Allah ya kar'ba.
Chapter 24 · 0% Book details