Sashe 65
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Anya ma akwai maganin anan?bari na kira a kawo mani na baki, Kiran waya yayi ya fad'i sunan magungunan da za'a kawo masa, Mufida ce ta ce
"Yaya banga Inteesar ba"
Tana cikin bedroom barci take, karaf kuwa Inteesar taji maganar Mufida bata ma san tare da su Mummy take ba, da sauri ta diro daga kan gadon ta mane cewa kanta ba d'an kwali rigarta duk ta cukuikuye gashin kanta a yamutse zif d'in rigar ma a zuge take, haka ta k'araso wajensu ganin irin kallon da suke mata na zargi musamman Mufida da ke watsa mata kallon gargad'i,tunawa tayi da yadda ta fito sannan ta kalli fuskar Muhdeen taga shatin jan bakinta a bakinsa sai ta kwa'be fuska cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka, Mufida ta ce
"Ina nan ina ta jiranki ke miji dad'i kinzo kin tare a office nasa ko?
Wato bakiji magana ta ba to kije ke kika sani duk abunda ya biyo baya."
Mummy ce ta kalle ta ta ce
"Me ke faruwa Mufida?"
Kallon Muhdeen Mufida tayi tare da cewa
"Komai ma ya faru."
*Wash hannuna ya gaji*
*Daga alk'alamin*
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don k'arin bayani*
09065327995
Love you oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page5
Kallon Muhdeen Mufida tayi tare da cewa
"Komai ma ya faru."
Kallon rashin fahimta Mummy tayi mata tare da cewa
"Ina komai ya faru me kike nufi?"
Kafin Mufida ta bud'e baki tayi magana Jabeer ya shigo office d'in a gigice wata nurse na biye da shi a baya, hannun Muhdeen ya janyo tare da cewa
"Pls kazo da sauri an kawo Emergency ne, suna buk'atar taimakon gaggawa."
Fita office d'in sukayi cikin hanzari, yayinda Mummy ke cewa
"Allah ya basu lafiya ya tashi kafad'arsu."
Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen, idanun Mufida na kan inteesar kafin ta maida dubanta ga Gwaggo ta ce,
"Kinga anyi masa kira gaggawa, gashi yamma tayi yakamata mu tafi tunda bamu San lokacin dawoarsa ba."
Dai-dai lokacin da wata ta shigo da leda da magungunan Gwaggo a ciki Mufida ce ta kar'ba tare da mik'ewa Gwaggo
"Kinga magungunaki an kawo."
Kar'ba Gwaggo tayi tare da kallon Inteesar ta ce
"Ke kuma abunda ya kawo ki kenan ko?
Ko kunya bakiji wai kinzo duba jikin Mahaifiyarki kenan ko? cikakken mintuna talatin bakiyi ba tare da mahaifiyarki taki, da kika kwanan biyu baki gane ta ba ko?amma shi mijin da kullun kina ganinsa kullun tare kuke kwana amma a asibitin ma ba zakuyi hak'uri ba saboda tsabar jaraba irin..."
Kuka inteesar ta sake tare da nufar Gwaggo zata fad'a jikinta ne ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ta ce,
"A'a ni kada ki k'araso waje na ki shafa mani najasa nasan ko wankan tsarki ma bakiyi ba."
Jin kalaman bakin Gwaggo yasa Inteesar komawa jikin Mummy,rungume Mummy tayi tare da saka kuka, Mummy ma rungume ta tayi tare da d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, tana shafa sumar kanta ta ce,
"Kema kinsan halin Gwaggo ba tun yau ba, haka take kada maganarta ya dame ki."
"Wallahi Mummy ba haka bane ba abuda mukayi."
"Ba komai ba sai kin rantse ba koda ma kunyi ba laifi kika aikata ba mijinki ne."
Tafa hannu Gwaggo tayi tare da cewa
"Yau ni kuluwa naga abun mamaki, 'yar albarka yaushe kika zama haka da rantsuwar k'arya? ko makaho ya kalle ki yasan da walakin goro a miya."
Mummy ce ta kalli Gwaggo ta ce,
"Kinga Gwaggo don Allah kibarta haka nan baki ga yadda taji bane, ai ba komai zakiyi magana aka..."
Kafin takai k'arshen maganar da zatayi Gwaggo ta ce,
"Dalla ni rufe mani bak, dan na fad'i gaskiya zaki ce me yasa?
Yarinyar da tazo dubiya na uwarta ko mintuna talatin batayi ba amma ta tare ta k'unshe a cikin ofishin miji sama da awa uku, tun lokacin da suka dawo sallar azahar fa gashi yanzun k'arfe biyar suna nanik'arki juna, 'yar k'aramar yarinya da ita sai jaraba, ni nasanta ko da naje gidansu nayi wata d'aya akwai ranar da na aike ta ta Kira mijinta muyi Karin kumallo tare, tunda ta shiga bata fito ba har yunwa taci ta cinye ni, sannan suka fito yamutsai yamutsai da ita, tunda yanzun an masa Kiran gaggawa ai sai ki koma wajen Ummanki kafin ya dawo."
"Gwaggo nifa ba da son raina na
biyo shi ba, cewa yayi yayi mije naci abinci da nak'i zuwa Mama ce tasa na biyo shi, kuma shi ya rufe office d'in da key ya hanani fita."
Rarrashinta Mummy tayi har ta daina kukan sannan ta shaida mata cewa ta shiga toilet ta watsa ruwa ta kimtsa jikinta ta koma wajen Umma, idan ya dawo sai su tafi gida, sallama sukayi suka tafi suka barta.
Bak'in ciki da takaici ne suka ishe ta,ga yunwa da ya addabe ta duk ta rasa yadda zatayi gaban dressing mirror ta tsaya ta gyara dogon sumanta tare da tufke shi, rigarta ta gyara zamansa ta rufe zif d'in rigar tayi bra d'inta da ya ya yaga gida biyu ta kalla d'agawa tayi taga ba yadda za'ayi ya moru, tsuki tayi tare da d'aukar hijabinta ta saka, ficewa tayi daga office d'in ta nufi hanyar da zara sada ta da d'akin da aka kwantar da Ummanta.
Tura k'ofar tayi ta shiga da sallama Abbanta da Mama Huraira ta gani sai Ummanta da ke kwance amma ba barci take ba, koda idanunta ya sauka akan Abbanta farin ciki ne ya lullu'be ta, dama tunda tayi aure bata k'ara ganin Abbanta ba, saboda ranar da suka je Muhdeen cewa yayi ya bata mintuna talatin ta gaishe su ta fito,hakan yasa bata ga Abbanta ba sai yanzun a asibiti.
Cikin farin ciki ta k'arasa gabansa tare da fad'awa jikinsa ta kwantar da kanta a kafad'arsa ta ce,
"Abba na nayi kewarka wallahi sosai."
Murmushi yayi tare da d'aga ta ya ce
"Kina lafiya?"
"Lafiya lau Abba na."
"Masha Allah ko na kira wayarki bata shiga ko kin canza layi ne?"
Tunawa tayi da tun ranar da Muhdeen ya kar'be mata waya bai bata ba, sai da Gwaggo ta amsar mata ranar da zata tafi, gashi yau ma ya amshe bata san ranar da zai sake bata.
"Abba wayar ce bansan inda ta shiga ba amma da zaran na nemo ta zan dinga Kira muna gaisawa."
Durk'usawa tayi ta gaishe da Abban nata ya amsa mata cikin so da k'aunar tilon 'yarsa, sannan ta k'ara gaida k'anwar Ummanta wato Mama Huraira, sannan ta k'arasa gaban gadon Umman nata ta durk'usa tare da rik'e hannun Ummanta ta ce
"Umma ya jikinki?"
Murmushi tayi tare da gyad'a kai almar da sauk'i, Mama Huraira ta kalle ta ta ce,
"Tun d'azu da naga shiru baki dawo ba sai na d'auka ko dai kun tafi gida ne."
Sunkuyar da kanta k'asa tayi tare da cewa
"A'a Mama ."
Tayi maganar a tak'aice tare da zama gefen gadon,fira suka dinga yi har sai da aka kira sallar magariba Abba ya tashi ya tafi masallacin, da ke cikin asibitin, kasancewar yanzun ba mutane a d'akin yasa Inteesar ta shiga toilet da ke cikin d'akin ta d'auro alwala ta fito ta shimfid'a sallaya tayi sallah, bayan ta idar ne Mama Huraira ta shiga ta d'auro tazo ta gabatar da sallar, bayan ta idar ta taimaka wa Umma ta rik'e ta sosai suka nufi band'aki ta taimaka mata tayi alwala suka fito ta saka hijab tayi sallah daga zaune.
Bayan sunyi sallar isha'i ne Mama Huraira ta janyo Basket d'in da ke da sauran Abinci da Mummy ta kawo masu, Abba ta zubawa sannan sauran da ya rage ta ce da Inteesar ta d'iba ta ci, ganin abincin ba wani yawa ne da shi ba kuma ga Mama Huraira bata ci ba yasa ta ce ta k'oshi dan yinwar cikinta ma tun yana damunta har taji ta daina jinsa.