← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 99

Sashe 10

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ne ya ya cigaba da maganar da ya ke yi;
"To idan sun tambaye mu dalilin fasa Auren Mai zamuce masu?meye dalilin da yasa muka fasa?Babu hujjar da zamu basu, sannan yarinyar nan da kika Kira da sunan karuwa bakida hujjar kiranta da sunan Don baki ganta Tana karuwanci ba ko wajen da karuwai suke zuwa, sannan maganar rashin tarbiyya da kika fada bazaki tabbatar da hakan ba don baki zauna da ita ba, sannan Ana sanin mutum ta hanyar zama dashi da aiyukan da mutum yake aikatawa ba ta suturar da yake sakawa ba, ni dai Don Allah na roke Alfarma a wajenki da ki bari ayi bikin nan kada mu zama kananun mutane".

Gwaggo tace
"Shi ke nan tunda haka kace, daga kai har matar ka kun goyi bayansa ai shi ke nan tunda haka kuka gani duk abunda dan ku yake so shi kuke so idon ku ya rufe baku hango abunda nake hangowa a tattare da ita ba shi ke nan ai"
Daga nan ta mike zata bar falon sai ta tsaya bakin kofar ta dawo ta kallesu tace;
"Ba mugun baki nayi ba, amma ku sani akwai ranar da ku da kanku zaku tuna da cewar ni na hana auren saboda akwai abunda na hango, lokacin da zaku gano abunda na hango kuma lokacin kun riga kun makara aikin gama ya riga da ya gama amma lallai sai tazo, Muhammadu ka rubuta ka ajiye duk sai kun yi nadama".

Abba ne ya budi baki yace
"Gwaggo Don Allah ki daina fadin haka Addu'ar ki kadai muke bukata da Sanya alkhairi".

"To shi ke nan ina maku addu'a kowa ne rana, biki kuma Allah ya sanya alkhairi".

Tana gama fadar haka ta sa k'ai ta fice.

Abba ne ya kalli Mummy da Muhdeen yace
"Kada ku damu komai zai tafi dai-dai da yardar Allah".

Mummy dai shiru tayi ta wuce b'angaren dama ba wai Tana son Auren Muhdeen da Sumayya ne ba, Amma ba yadda ta iya tunda ya nace ya ji ya gani ita ya ke so.

Mikewa Muhdeen yayi jin ana kiran sallar magariba, Mummy ma mikewa tayi tabi bayansa ya yin da Dady ya nufi bedroom din sa Don doro Alwala ya nufi masallaci.

Wata Rana bayan Inteesar ta gama yiwa umman ta aiki kamar yadda ta saba.sai ta shigar dakin ta ta kwanta bisa 'yar katifar ta Tana Jin alamun zazza'bi na damunta, wayarta ne tayi ringing ta duna taga sunan Mufida ce ke kira, daga wayar tayi tare da yin sallama.

Mufida dake zaune akan kujera Gwaggo na tsaye akanta Tana Mata fadar cewa me yasa har yanzun Inteesar Bata zo ba kuma Bata Kira ta a waya ba?

Ita wallahi bazata ci Abincin Mummy ba sai dai a Kira Inteesar tazo suyi girki.

Jin Inteesar ta daga wayar ne yasa mufida cewa
"Inteesar Don Allah ki zo ko wannan rigimammiyar zata Bari nasha ruwa".

"Gaky Mufida gaskiya bazan samu zuwa yanzun ba don har na d'an kwanta anjima zan shigo"
Sai ta d'an yi shiru sanin cewar idan har Bata tafi ba Gwaggo zata hana kowa sakat a gidan Nan idan Bata ga Inteesar ba.

"Ko kuma kice mata gani nan zuwa yanzun nan insha Allah"
Daga Nan ta katse kiran ta Mike tsaye tare da daukar wayarta da Hijab dinta, bayan saka Hijab din ta kai tsaye dakin mahaifiyarta nufa, zaune ta sameta bakin gado Tana ninke kayan wankin da Inteesar ta wanke mata.da sallama ta shiga dakin,Umma ta amsa Mata Tana sakin murmushi cikin son d'iyarta d'aya tilo da Allah ya Bata.

"Umma dama zan je gidansu Mufida ne, Gwaggo ce take son wai na je muyi girki tare"
Jinjina Kai Ummu tayi
"To ke da kika ce bakida lafiya kina jin ciwon k'ai da zazza'bi? tunda kin sha magani kamata yayi ki kwanta ki sanar dasu baki Jin dadi"
Ta karasa maganar Tana tausayin 'yarta.

Murmushin karfin hali tayi tare da cewa,
"Umma baki San Halin Tsohuwar Nan ba wallahi idan ban je ba zata addabe su ne musamman Mufida"
"To shi ke nan Allah ya baki lafiya ki gaishesu"
"To za su ji"
Daga nan ta fice ta nufi gidansu Mufida lokaci zuwa lokaci takan zubar da yawu a bakin ta kamar wata mai ciki, dama haka zazza'bin ta yake saboda bakinta ba taste bata iya had'iyar yawu.

Tana isa bakin kofar gidan ta gaida Mallam Ibrahim Mai gadi, sannan ta nufi cikin gidan dai-dai lokacin da ta karasa kan barandan kafin ta shiga falon sai ta juya ta zubar da yuwun bakin ta, kwatsam ta ji ance "keee!" da sauri ta waiga ganin Muhdeen zaune akan kujera Yana kallon yawun da ta watsa masa a Riga.l, cikin kad'uwa ta zaro ido Tana kallonsa kafin ta ankare ya sauke Mata tagwayen maruka biyu, cikin azaba ta kwalla kara wanda ya ja hankalin jama'ar gidan.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne,ban Rubuta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba .Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.

Page1
Cikin azaba ta kwalla Kara Wanda yaja hankalin jama'ar gidan.Mallam Ibrahim Mai gadi da yunusa Mai bawa fulawa ruwa da sauran ma'aikatan gidan cirko-cirko sukayi suna kallon ikon Allah. yayinda Inteesar ke durkushe dade da kuncin ta Muhdeen kuwa na tsaye akanta Yana huci, dai-dai lokacin Mummy da Mufida da Gwaggo suka karaso wajen,ganin Inteesar durkushe Tana kuka yasa Mummy cikin sauri ta karasa tare da mikar da ita tsaye,ganin sawun kumatunta sunyi jajir ga sawun yatsu biyar da Muhdeen ya Mata ne yasa hankain tashi cikin tsananin bacin Rai Mummy ta Fara magana.

"Yanzun son Kaine ka daga hannayen ka akan fuskar yarinyar Nan ka mare ta akan meye?

Yarinyar da ba ruwan ta Mai gudun 'bacin ran mutane zaka mare ta?"
Yana huci ya Fara magana
"Mummy baki ga abunda tayi Mani bane,yawun bakin ta ta watsa Mani a jikin Ka..."
Kafin ya Karasa maganar sa ne Gwaggo tayi saurin cewa,
"To shugaban mugaye na Duniya sai me idan ta watsa maka yuwun bakin ta?ko yawun najasa ne da zaka kama 'yar mutane daga zuwan ta ka Fara dukan ta kamar Allah ya Aiko ka mugu kawai Mai bakar zuciya akan yawu zaka kama 'yar mutane zaka illata.wannan irin mari ai sai ka kurmantawa mutane 'ya ta zama musaka.

Gwaggo ne ta janyo Inteesar daga jikin Mummy ta rungume ta a jikin ta Tana Dan bubbuga bayan ta.Hatta Mufida sai da taji kamar zatayi kuka ganin yanda fuskar Inteesar din ta canja.

Gwaggo ta dago fuskar ta tare da janyo ta suka nufi kofar falo suna tafiya Tana fadin,
"Kiyi Hakuri kinji yarinyar arziki wannan muguntar da ya maki Allah zai bi maki hakkin ki akan sa, Mufida ce tabi bayan su daga Mummy sai Muhdeen a wajen,zuba masa ido tayi tace,"
"Gsky son ka 'bata Mani Rai sosai akan wannan Hukuncin da ka yanke akan Inteesar ta watsa maka Miyau haba Hukuncin naka yayi tsauri da yawa Don yarinyar Nan bazata ta'ba watsa maka yuwun bakin ta da sanin ta ba na tabbatar Bata lura dakai bane.yanzu idan Asiya ko Mufida ne suka watsa maka yuwun bakin su a bisa kuskure Hukuncin da zaka dauka kenan akan su?"
Girgiza Kai yayi Yana fadin,
To Mummy so fa jini na ne ta Yaya Zaki hada su day wannan kucak..."
Tsawar da ta daka masa ne yasa yayi shiru.

"Kai!

Kai ka fita a idanuna na fada mak,Yadda na dauki Inteesar haka na dauki Asiya da Mufida bana nuna masu Banbanci,haka ma mahaifin KU ya dauke ta komai tare yake masu sai abunda baza'a rasa ba,Hatta Mufida irin shakuwar da sukayi da Inteesar basuyi shi da 'yar uwar ta Asiya ba.kaima haka nake so daga gare ka ka dauke ta kamar kanwa CE a gare ka"
Daga Nan tasa Kai ta shige falon Shima bayan ta yabi .

Gwaggo na zaune akan kujera ta daura Kan Inteesar akan cinyar ta, mufida na zaune tayi tagumi ta zubawa Inteesar ido ganin yanda sawun yatsun yayan nata akan fuskar Inteesar gefen dama da hagu sunyi jajir.

Mummy ta nufi dakin ta Muhdeen ma part din sa ya nufa nufa yayin da Gwaggo tabisa da harara Tana cewa,
"Gaka fari Amma zuciyar ka bakakirin Ga kyawun sura Amma ba kyawun Halayya"
Baibi ta kanta ba ya nufi dakin sa ransa a bace.mummy ce ta karaso falon Hannunta dauke da magani fridge ta nufa ta dauko robar ruwa ta zauna ta balle maganin ba bawa Inteesar tare da Goran ruwa,ba musu ta karba ta hadiye.Ba jimawa bacci ya dauke ta ganin haka yasa mummy tace ma Asiya ta biyo ta kitchen suyi aikin tare.bayan tadiyar su ne Gwaggo ta nufi dakin ta Tana cewa,
"Dan bakin ciki yarinya tazo tayi Mani girkin ta Mai dadi ya Hana ta da muguntar sa"
Muhdeen Yana shiga dakin sa you nufi toilet dinsa kayan ya cire yayi wanka da sabulu Mai kamshi da turaren wanka,ya shirya cikin kananun Kaya jar Riga da bakin wando,Kai tsaye yabar part din sa ya nufi falon ba kowa sai Inteesar dake bacci,Goran ruwa ya bude ya Dan yayyafa Mata ruwa a fuska,a firgice ta farka zatayi masa kuka Dan tsoron sa take ji,daura yatsar sa yayi a bakin sa alamun tayi shiru.

"Shhhshhh"
Hannayen ta ta saka ta toshe bakin ta Tana kokarin hadiye kukan,sannan yace,
"Ki biyoni daki na"
Da sauri ta Ware dara-daran idanun ta Tana kallonsa cikin tsoro da mamaki Tana girgiza masa Kai,daure fuska yayi ba Alamar rahama,da hannu yayi Mata nuni da ta biyo shi.

Haka ta Mike ba musu Tana gaba Yana binta a baya har suka karasa part din sa cogewa tayi a bakin kofar dakin Tana tsoron shiga sanin cewa ba kowa a dakin kuma Ummanta ta Hana ta ke'bewa tare da namijin da ba muharramin ta ba.
Chapter 10 · 0% Book details