← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 99

Sashe 34

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Muhdeen yabar gidan Asibiti ya koma,Kai tsaye office d'in Jabeer ya nufa yana k'ok'arin knowking ne Jabeer ya murd'a handle d'in k'ofa zai fito,ganin Muhdeen ne yasa ya koma ciki yana k'unshe dariya a bakinsa,zama yayi a sofa dake cikin office d'in Muhdeen ya tsaya tsaye ya zuba masa luhuluhun idanunsa yana kallonsa.Jabeer ne yayi k'ok'arin dakatar da dariyarsa ya ce,
"A mijin kucaka har ka gama kwasan romon amarcin ne?

Dan Allah adai dinga d'aga k'afa kasan sabbin shiga sai a hankali sai ana tausaya masu,duk da nayi mamakin cika bakin da ka dingayi akan Inteesar sai dai abun mamaki a Rana d'aya ka zubar da makamanka,banyi tunanin haka da wuri ba fa nace ashe ashe kucakar yarinyar da ka tsana zatayi maka rana 'Dan iska jarababbe ranar har kana cewa ko Mata sun k'are a duniyar nan ba abunda zakayi da ita,Ashe har matan sun k'are banda labari."
Ya k'arasa maganar yana kecewa da dariya, Muhdeen ransa ne ya gama 'baci kuma shi Mai yawan magana ba gani yayi baida lokacin 'bata lokacinsa a kan Jabeer yasa ya mi'ke ya nufi hanyar fita.Da sauri Jabeer yasha ganansa tare da cewa
"Sorry friend dama na kiraka ne dan na shaida maka kana da patients suna jiranka"
Daga nam Muhdeen yasa Kai ya fice ya bar Jabeer na binsa da kallo.

A yammcin ranar ne Muhdeen ya koma gida dan magana da mahaifinsa,cikin sa'a kuma ya same su dukkansu a falo Dady, Gwaggo,sai kuma Mummy,da sallamarsa ya shigo falon,gaba d'ayansu suka amsa masa nan ya gishe da kowa da kowa harda Gwaggo yau cikin girmamawa ya gaishe da ita yana kwantar da Kai Dan kada tasa Dady ya hana shi zuwa London.Harda yi mata alk'awarin kawo mata magungunan ciwon k'afarta Wanda zata ji dad'i haka ya dinga kamfen a wajen Gwaggo don yasan ba k'aramin aikinta bane tasa Dady ya hana sa tafiya.

"Muhammad ya akayine ance kana ta zuwa nema na bana nan kuma baka sanar dani a waya ba."
Sunkuyar da Kai yayi
"Dady maganar ba Bata waya bace shiyasa."
"To Allah yasa lafiya ina jinka"
"Dady Sumayya ce ta tafi bansan inda ta je ba tun da taji an d'aura aure na da Inteesar ta saka k'afa tabar gidan har yau bansan inda ta tafi ba."
Da mamaki Dady ke kallonsa
"Subahanallahi shine tun tuni baka sanar da kowa ba sai yanzu?Haba Muhammad ai baikamata kayi shiru ba."
"Dady abunda yasa nayi shiru na d'auka zan ganta ne sai na shawo kanta mu cigaba da zamanmu,to gaba d'aya mun zaga garinnan inda nasan cewa tana da k'awa ko dangi ko wani Wanda yake da alak'a da ita amma ko ina bata nan."
Mummy ce ta ce,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,shine na aka tambayeka ka sanar da matarka kace eh."
"Wallahi Mummy na d'auka zan iya shawo matsalar ne,kuma na Kira number Dad da Mum d'inta duk basa shiga."
Dady ne ya ciro wayarsa a aljihu ya Kira number Dad d'in Sumayya Yana ringing baj d'aga ba, har sau uku.Nan dai ya kwantar wa Muhdeen da hankali,ya ce su tafi masallaci kasancewar lokacin sallar magarib tayi.
*WAIWAYE*
A ranar da Sumayya ta k'ona kayan lefenta bayan ta koma d'aki ta Kira Mum d'inta tana kuka ta sanar da ita komai.Ran Mun nata ta ce ta tattara kayanta ta bar gidan wani irin wulak'anci ne zasu bada auren 'yarsu sati biyu da aure a k'ara mata kishiya?bazai yiwu ba.Ta bata shawarar ta tattara kayanta tabar masa gida kada ma ta je wurin da zai nemota ta tafi Hotel washe gari ta jirgi ta taho.Shiyasa da Muhdeen ya gama zaga gidajen duk Wanda yasan Yana da alak'a da Sumayya bai same ta ba.wannan shine abunda ya faru
Bayan Dady da Muhdeen sun tafi Masallaci basu dawo ba sai da aka Kira sallar isha'i.Suna zaune a Dinning table kafin su fara cin abinci Dady ya k'ara gwada Kiran number Dad d'in Sumayya.A wannan karon ya d'aga.Kasancewar wayar a amsa kuwa take yasa dukkansu Gwaggo da Mummy da Muhdeen suna jiyo muryar Dad d'in Sumayya.

"Me ka kirani a waya ka sanar dani? cewa d'anka ya saki 'yata ko me?

Kunsan kuma da matar da zaku aura masa kuka bari ya auri 'yata?to Bari kaji 'yata ba zata zauna da kowace kishiya ba.Tun yaushe tabar gidan da yake baku damu da halin da ta shiga ba shiyasa baku Kira ba sai yanzun ko?

Dady ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Alhamdulillah tunda tana wajenku hankalina a tashe yake da naji mijinta wai baisan Ina take ba,dan Allah ka saurareni nayi maka bayani ba yadda kake tunani bane,nasan ranka ya 'baci amma ka fahimcemu."
Dad d'in Sumayya fad'a ya cigaba dayi
"Babu fahimtar da zanyi maku d'anka ya za'bi d'aya ko 'yata ko wacce kuka aura masa."
Daga Nan ya katse kiran wayar.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Domin k'arin bayani
09065327995
*INA BARAR ADDU'ARKU DAN ALLAH KUSA K'AWATA A CIKIN ADDU'ARKU TANA CIKIN DAMUWA ALLAH YA YAYE MATA DAMUWARATA YA KAWO MATA FARIN CIKI A CIKIN RAYUWARTA.DA MA DUKKANIN AL'UMMAR MUSULMI*
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.

Page3
"Babu fahimtar da zanyi maku d'anka ya za'bi d'aya ko'yata ko wacce kuka aura masu"
Ran Gwaggo ne yayi maaifar 'baci da jin kalaman Dad d'in Sumayya,don haka ta ta mi'kawa Dady hannu alamun ya bata wayar,ba musu ya mik'a Mata kamar yadda ta buk'ata.Kar'ba tayi tare da karawa a kunnenta ta fara magana.

"Waye kai da har zaka ce ya za'ba ko 'yar ka ko matar da ya aura?to bari kaji ninan kakarsa wacce ta haifi ubansa kuma ta aura masa Inteesar nace baka Isa ba kayi kad'an.kai da ka kasa ba 'yarka tarbiyya shine..."
Muhdeen ya k'araso gabanta yana had'e hannaye alamun rok'o,a hankali yake mata magana dan kada Dad d'in Sumayya ya jiyo muryarsa.

"Kinga Gwaggo ya kike neman ki 'bata komai ne?don girman Allah ki rufa mani asiri ki lalla'basu ko zata dawo,idan bata dawo ba wallahi akwai matsala ."
Tsawa ta daka masa
"Dalla can rufe mani baki kada Allah yasa ta dawo mana, idan 'yar tasa wata masifa ce ya jik'ata ya shanye."
Hannu Muhdeen ya d'ora akai ganin Gwaggo ta dagula komai.

Dad d'in Sumayya da Mum d'inta kuwa duk suna jin komai dake faruwa ta cikin wayar.

Gwaggo ta cigaba da magana
"Idan ma za'ba zaiyi sai dai ya za'bi za'bin da nayi ma..."
Mum d'in Sumayya ce ta kar'bi wayar daga hannun Dad ta katse kiran cikin 'bacin rai ta fara magana.

Akan me zasu wulak'anta mana 'ya? to bamu gaji da 'yar mu ba?wani iri wulak'anci ne wannan ace aure ko wata d'aya bai kai ba ace anyi mata kishiya,sannan ta dawo gida basu nemeta ba sai yau basu damu da halin da take ciki ba,sannan cin mutunci ne zai biyo baya?wallahi bazai yiwu ba 'yata ba zata zauna da wannan 'yar matsiyatan ba don bata Kai matsayin da 'yata zatayi kishi da ita ba."
Kai tsaye ta nufi d'akin da Sumayyar take ciki,tura k'ofar tayi ta shiga zaune ta sameta rik'e da wayarta tana kallon photon Muhdeen tana kuka.kar'bar wayar tayi daga hannun Sumayya Wanda hakan yasa ta d'ago Kai da sauri ta kalli Mum fusrkata da kwalla.

"Mum Kinga har yanzun bai biyo ni ba ki?yana can ya tare da wannan matsiyaciyar Inteesar d'in wallahi bazai yuwu ba Muhdeen nawa ne ni kad'ai duk maccen da ta ra'besa sai na kasheta ko kuma na illatata,Bata Isa ta mallaki abunda na mallaka ba."
Haka dai tayi ta surutu a cikin tana jifa da pillows d'in dake saman bed d'in, Mum d'inta ce ta rungumeta tana rarrashinta.

Muhdeen kuwa tsabar tsabar takaici da bak'in cikin abunda Gwaggo tayi ne ya ishe sa.Bayan Mum d'in Sumayya ta katse kiran ne ta kalli Gwaggo cikin jin haushinta ya fara magana.

"Wai Gwaggo meye matsalarki dani ne?duk kinbi ki addabi rayuwata,kin hanani samun nutsuwa a rayuwata wai me nayi maki ne?kullun kika tashi magana Zaki ce wai cikin jikokinki kinfi sona da k'aunata ta,amma a ganina ba Wanda kika tsana kamar ni.Kinbar kowa ya auri matar da yake so ya zauna da ita amma Ni tun ranar da na kawo Sumayyar nan a matsayin matar da zan aura kika fara kushe ta Wai bata da tarbiyya,shin ke Zaki zauna da ita da rashin tarbiyar ta ko kuma Ni zan zauna da ita?na aure ta duk da haka bai isheki ba sati biyu da auren mu kika sa aka d'aura mani aure da wata Wai Inteesar to Bari koji bana so Inteesar Sum..."
Kafin yakai k'arshen zancen Dady ya d'aga hannu zai mare shi ne Gwaggo ta daka masa tsawa
"Kai Sani!!"
Dakatawa yayi daga Marin da yayi niyar masa,don a rayuwa Gwaggo ta tsani abunda zai ta'ba Muhdeen tana k'aunarsa fiye da sauran jikokinta,tun yana yaro take masifar ji da shi Bata k'aunar taga an ta'a mata shi.

"Akan me zaka mare sa Sani?"
"Haba Gwaggo kina Jin yadda yake magana dake kamar ..."
"Ba ruwanka da nu yake bada kai ba ku daina shiga lamarina da Muhammadu."
Dallonsa Dady yayi tare da cewa
"Tashi ka tafi gidanka"
Ba tare da ya ce komai ba ya mik'e ya ya fice,gaba d'aya ya rasa me ke masa k'unci kawai yake ji a zuciyarsa,ga rashin Sumayya ga kuma aurennan na Inteesar dan ko kad'an baya Jin soyayyar Inteesar a cikin zuciyarsa.Yayi da ya sanin maganar nan a gaba Gwaggo gashi ta 'bata masa komai har ran Dady ya 'baci shi da yasa ran Dady zai fahimci halin da suke ciki amma ba haka ba.
Chapter 34 · 0% Book details