← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 99

Sashe 79

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kai kawai ta gyad'a alamar eh, Mummy ta zuba mata ido tana murmushi ta ce
"Daughter ya dai kamar akwai magana a bakinki ko?"
Sunkuyar da kanta k'asa tayi ta ce,
"Eh Mummy"
"Me ke faruwa?"
Gwaggo ce tayi saurin cewa
"Ki dai kin gaji da zama da mu ne mu maida je d'akin mijinki?"
Tura baki tayi tare da yin narai da Ido kamar zatayi kuka, Mummy ta ce
"Kwantar da hankalinki ba zamu maida ke ba kinji?"
Kai ta jinjina cikin sanyin muryarta ta ce,
"To Mummy"
"Yauwa to ki fad'a mani akwai abunda kike buk'ata ne?"
Kai ta jinjina
"Dama cewa zanyi tunda aka sallamo Umma banje na gaishe ta ba, tunda tana gida muna kusa nake so naje na gaishe ta."
Gwaggo ta ce
"Akan wannan shine kike damuwa? ai uwa ba wasa ba, kuma ai ba nisa bane nan baya ne kije kawai amma dan Allah kada ki sanar da su halin da ake ciki kada hankalinsu ya tashi, kinga Ummanki ba lafiya ne da ita sosai ba, ki nuna mata daga gidan mijinki kika zo kika fara sauka nan sannan kika je gaishe ta."
Kai Inteesar ta jinjina alamr to sannan ta nufi d'akin Mufida, ba jimawa ta fito da hijabinta jar k'asa, sallama tayi masu ta tafi.

Ummanta na zaune tana wankin kayanta, Inteesar ta shigo da sallama, tana hangen Umma ta k'arasa a guje ta rungume ta, Umman nata tayi farin ciki sosai da ganin tilon 'yarta.

"Umma Ina wuni?"
"Lafiya lau wlh"
"Ya jikinki?"
"Jiki Alhamdulillah"
"Mummy tashi na k'arasa wankin"
"Ai na gama "
Inteesar ce ta dinga daukar kayan tana shanyawa akan igiyar shanya, a haka har suka gama.

A can gidan Mummy kuwa Inteesar na barin gidan sai ga Muhdeen yazo, bayan yayi parking ne ya gaisa da ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan.

A falo ya tarar da Gwaggo da Mummy, gaishe su yayi sannan ya durk'usa akan kadarsa ya ce
"Mummy in wuni?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa masa, dubansa Gwaggo tayi tare da kauda kanta taji ya ce,
"Ina wuni Gwaggo"
"Wai yau Kaine ka gaishe ni? banza bata kai zomo kasuwa, abunda kake so na sani saboda matarka ka gaishe ni, kuma ta ba zata koma gidanka ba Dan haka kai kawo mata takardar saki."
Ji yayi kamar an soka masa mashi a kahon zuciyarsa, bazai iya jure maganar Gwaggo ba da haka ya mik'e ya nufi k'ofar fita ba tare da cewa komai ba, a harabar gidan ya had'u da Mufida ya kalle ta ya ce,
."Inteesar tana barci ne?"
Wallah nima yanzun na dawo gidan, kataf suka ju muryar mai gadin yana cewa
"Bata jima da fita ba"
Da sauri ya kalle shi
"What!? ta fita zuwa Ina?"
"Wai zata je gaida Mahaifiyarta da jiki"
Bai Kara cewa komai ba yaja motarsa yabar gida.

Inteesar tana gama shanya kayan Ummanta yaro yayi sallama ya shigo ya ce wai ana sallama da Inteesar, gabnta ne ya fad'i ta ce waye? yaron ya shaida mata cewa wani ne da mota yazo, ta ce ya ke ya sanar bata nan Umma ce ta ce ,
"Saboda me zaki ce haka, bayan kinsan idan ba mijinki ba ai ba Wanda zaizo nemanki, ko dai tare kuka zo ne ya tsasya jiranki waje?"
Rasa ba Umma amsa tayi don bata son ta fahimci halin da take ciki da mijinta, bata gama tunanin ba ta ju Umma na cewa ki tafi ki same shi."
Ba musu ta d'auki hijabi ta nufi k'ofar fita, gabanta ne ya fad'i ganin Usman zaune akan motarsa ya zuba mata ido yana sakar mata murmushi, a zuciyarta ta ce ya akayi yasan tana nan, k'arasawa tayi da niyyar idan ta je ta sanar da shi gaskiya an mata aure da wani.

"Ina wuni?

Murmushi yayi tare da cewa
"Bazan amsa gaishwar ba tsawo kwanki kina wahalar da ni, kullun sai na kira wayarki bata shiga, na kasa hak'uri tsawon lokaci banganki ba zuciyata ta kasa jurewa."
Dai-dai lokacin motar Muhdeen ya k'araso yana parking idanunsa ya sauka akan Inteesar da Usman, ji yayi jinsa da ganinsa sun d'auke na wucen gadi, Usman sai Murmushi yake sakar mata a fusace ya fito daga cikin motar ya nufe su, Inteesar na ganinsa sai da ta tsorata, amma ta daure ya Harare ta ya ce,
"Kina da hankalinki kuwa, kinsan abunda kikayi kuwa"
Kallonsa tayi ta ta'be baki ta ce,
"Waye kai a ina ka sanni?"
Juyawa tayi ta koma cikin gidansu, ya bita da kallon mamaki da al'ajabi, sannan ya kalli Usman ya tuna cewa shine wanda ya ta'ba ganin suna zance da Inteesar kafin tayi aure, kuma shine ya gani ya d'auko Inteesar a mota sunje ubasanjo complex tana zaune gaban motarsa suna sakarwa juna murmushi, rintse idanunsa yayi tare da bud'e su ya kalli Usman ya ce,
"Waye kai?"
Dariyar rainin hankali Usman yayi tare da cewa
"Wanda yazo akeyiwa wannan tambaya ba wanda aka tarar ba"
"Ina mai gargad'i a gare ka ka kiyayi matata."
"Wace ce matarka?

Inteesar kake nufi? to ai naga ita wacce kake Kira matarka bata ma sanka ba bata san kanayi ba, isaka ne ke wahalar da mai kayan Kara."
*Daga alk'alamin*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don k'arin bayani*
09965327995
Love you oll
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne.
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6
"Wace ce matarka?

Inteesar kake nufi? to ai naga ita wacce kake Kira matarka bata ma san kanayi ba, isaka ne ke wahalar da mai kayan Kara."
Muhdeen ne ya fusata ya shak'o wuyar rigar Usman ya ce,
"Ka iya bakinka ka san kuma da wa kake magana, idan baka fita daga harkarta ba zan d'auki mummunar mataki akanta."
Dai-dai lokacin Abban Inteesar ya k'araso K'ofar gidan, ganinsu a hakanan yasa ya k'araso wajensu da sauri
"Subhanallahi Muhammad me ke faruwa ne?"
Sakin wuyar Usman yayi tare da hankad'a shi gefe yana huci kamar wani mayunwacin zaki, Usman ne ya durk'usa ya gaida Abba.
Chapter 79 · 0% Book details