← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 99

Sashe 7

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tanimu Dan kasuwa ne,kasuwancin Gwal-gwalai yakeyi daga kasar dubai.amma dai yanxun haka suna zaune a London ita da iyayen nata.sai dai ta sanar dani ta hanyar text message Wai gobe zasu dawo Nigeria."
Kai Abba ya jinjina alamun gamsuwa Sanan yace,
"Zanyi bincike akai,idan yaso sai na Kira Yaya Adam da minina Alh.kabir sai muyi abunda ya dace."
Haka kuwa akayi a cikin sati daya aka saka ranar Auren Muhdeen da sumayya nan da watanni biyu masu zuwa.farin ciki a wurin masoyan guda biyu baya misaltuwa,domin abunda suke buri kenan.

Wata ranar Asabar ne Muhdeen ya sanar da Mummy cewar zai kawo Mata sSumayya ta gaishe a.mummy taji dadin hakan sosai.

Da misalin karfe biyar na yamma sumayya ta gama Shirin ta tsaf da kananun Kaya tasaka saboda dasu ta Saba, mom din ta ce tace ta cire su saboda gidan surukanta zataje tayi shiga na mutunci,zasufi ganin mutuncin ta.dakyar ta yarda ta saka wasu matsatstsun Riga da siket na leshi sun matse ta sosai kamar zatayi numfashi su yage,wayar ta ne tayi ringing Jin ringing din wayar yasa ta sakin murmushi,domin tasan waye ke kiranta ringing d'in sa na musamman ne tasa masada sauri ta daga wayar.

"Hello sweet ganinan fitowa"
Muhdeen dake zaune a motar say Yana jiran ditowar ta ne ya ce,
"Please Baby kiyi shigar mutunci da Kamala,na hanaki saka irin kayayyakin da kike sawa kinki ji ko?"
Tura baki tayi tace,
"To ni fa kasan dasu nasaba."
Muhdeen ya ce,
"Ai zance ya kusan karewa da zaran mumyi aure manyan Kaya da manyan hijabai Zaki dinga sakawa,idan kinda kananun Kaya sai dai idan ni zakiyiwa kwalliya"
Murmushi tayi sannan ta ce
"Ganinan fitowa gashin attached din da akayi Mata Kari ta sake shi baya,tayi daurin Dan kwalin nan da ake cewa ture kaga tsiya,siririn mayafi ta rataya shi a gefen kafad'arta ta tare da rataya handbag dama tayi kwalliya fuska tun daga Kan powder har janbaki ta fesa turarurruka kala uku tasa takalmin ta mai tsini ta dauki wayoyin ta ta rike a hannu.ta nufi kofar fita.Afalo ta samu mahaifiyar ta,sallama tayi Mata ta fice.

A cikin mota ta same shi Yana jiranta,bude murfin motar tayi ta shiga ido ya zuba mata yana kallon ta sai sakin murmushi takeyi ta jujjuya ido takeyi tare da cewa.

"Baby ya kaga shigar manyan kayan nawa?yayi ko?"
Zuba Mata ido yayi tare da cewa
"Ba laifi"
Zuba masa ido tayi
"Cewa zakayi ba laifi?

Bayan Kai da mummy ne kuka ce nasa kayan mutunci Amma ki ka Yana Mani?"
Murmushi yayi tare da cewa
"Sorry my Baby kinyi kyau Amma kike kisaka Koda irin 'dan abayar nan ne da mayafi da mata ke sakawa"
Kallon mamaki tayi masa tace,
"Tab wlh bazan iya kayan wahala ba duk nauyi ya dameni ga zari ba yanda isaka zai shiga ."
Jinjina Kai yayi
Taci gaba da cewa
"Ni bana ma da abayar ballantana nasaka."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Ba damuwa zamu siya a hanya sai ki saka mu karasa gidan"
"Yakamata ka gane zansha wahala idan na saka"
Yace,
"Shikenan mu tafi"
Baiso haka ba amma ba yadda yadda iya,baiso hakan ba.

Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu kofa suka fita,basu same ki Ina ba sai gidan su Muhdeen.Bayan yayi horn mai gadin gidan ya bude masa kofa ne ya shiga yayi parking.

Atare suka bud'e marfin motar suka fito,Tana tafiya cikin takunta na yanga har suka karasa falo,ba kowa sai Mufida dake zaune a Kan kujera ,ganin su ne yasa ta mike cikin farin ciki ta ce
"Sannu da zuwa Aunty Sumayya oyoyo matar Yayan mu"
Sumayya ma murmushi tayi tare da cewa
"Yauwa Mufida ya karatu
"Alhamdulillah"
Kasancewar Sumayya tasan kowa a gidan Muhdeen ya tura Mata photon su tun daga kan Dady da Mummy da Asiya da Mufida duk tasansu a photo.

Inteesar ce ta fito daga dakin Mummy sanye da Hijab ganin Inteesar sai da gaban Sumayya ya fad'i
Inteesar cikin fara'a ta kalle su tare da cewa
"Sannu da zuwa,Ina wuni?"
Yamutse fuska Sumayya tayi tare da cewa
"Wace ce wannan?"
Mufida tace kamar 'yar uwa take a wurin mu kullun Muna nan gidan a tare sunanta Inteesar"
Sumayya ta Kare Mata kallo ganin irin kyawun da Allah ya mata,gata kamar wata balarabiya Fara ce doguwa mai dara-daran idanu,ga hancin ta dogo sai dan karamin pink lips din ta duk da ta saka hijab Amma Ana ganin yala-yalan gashin kanta da ya kwanta luf a goshin ta
take sai taji tsanar Inteesar a cikin zuciyar ta.

Dai-dai lokacin Mummy ta k'araso falon,turus ta tsaya tana karewa summaya kallo,
Cikin wani irin murya ta ce
"Son wannan ce matar da zaka aura?"
Muhdeen ya zamo daga Kan kujera ya durkusa akan center carpet din falon
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love you oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman ihsa)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa
Page0
Muhdeen ya zamo daga Kan kujera,ya durkusa akan center carpet din falon.cikin far gaba ya ce
"Mummy itace, na kawo ta ta gaishe ki."
Jinjina Kai mummy tayi tana karewa Summaya kallo,gani tayi sam bata dace da Rayuwar Dan ta ba,dan daga gani bata samu tarbiyya mai kyau ba do daga gida ba,kallon Karin gashin da akayi mata ne ya zubo har tsakiyar bayan ta ga uban make up har yayi yawa,suturar jikin ta ya bayyana surorin jikin ta a bayyane, girgiza Kai tayi ta karaso ta zauna kan kujera.

Muhdeen idon sa nakan mahaifiyar sa yana karantar yanayin ta.

Sumayya daga yanda take zaune Kan kujera ta gaida mummy ta ce,
"Barka da fitowa mummy"
Cikin sakin fuska Mummy ta ce,
"Yauwa sannu da zuwa"
Sumayya ce daga yanda take zaune Kan kujera ta Kara da cewa,
"Ina wuni Mummy"
Ba yabo ba fallasa
Mummy ta amsa Mata da,
"Lapiya qalau Sumayya,ya mutanen gidan?"
Amsawa tayi da duk suna lafiya
Dai-dai lokacin ne Inteesar da Mufida suka loda Mata kayan ciye-ciye da lemu da ruwa a gaban ta.

Shidai Muhdeen yana zaune a kasa saman carpet,don dama shi idan iyayen say suna zaune a kujera shi yana k'asa a zaune.koda kuwa daga baya suka zo suka tarar da shi akan kujera da zaran su zauna zai sauka kasa.Haka ma sauran kannen sa, Inteesar ma dabi'ar ta ce wannan tun fil'azal.

Sumayya ruwa kawai tasha Wanda mufida ta kawo tata,kayan ciye-ciyen da Inteesar ta kawo mata kuwa ko kallon su batayi ba ballantana ta taba.
don haka kawai sai taji kishin yarinyar musamman yanda taga Allah yayi mata sura Mai kyau gata Tana zaune a gidan su Muhdeen,kuma tasan dole zai dinga yawan ganin ta.sai tsanar Inteesar ya sake nunkuwa a cikin zuciyar summaya,don tasan tafita komai,abu d'aya zata fita dashi shinec tsayi Don sumayya doguwa ce tafi Inteesar tsayi.bayan nan ba abunda zata n mata,ko hasken fata ma idan Kika kalli Inteesar da sumayya zaki ga Sumayyar ta fita hasken fata.don ita tana karawa da mai maisa hasken fata shiyasa farin nata ya zarce na inteesar.amma da badon mai ba Inteesar tafita hasken fata
Ido ta zubawa Inteesar sai taji k'irjin ta na dukan uku-uku,ta juya ta kalli Muhdeen dake zaune kasa s
aman carpet tace,
"Baby mu tafi ko"?

Kallon juna sukayi mufida da Inteesar yayinda mufida dariyar da take 'boyewa ne ya kufce mata.

Ganin kowa ita yake kallo yasa taja hannun Inteesar suka shige dakin ta da sauri.

Mummy ce ta kalli sumayya ta ce,
"Tun yanzun gashi komai baki ci ba?"
Yamutse fuska Sumayya tayi yayinda ta kalli kayan ciye-ciyen da Inteesar ta ajiye Mata tare da cewa
"Mummy am okay"
Mummy ce ta Mike tare da cewa
"Ina zuwa"
Kai tsaye dakin ta ta nufa,ba jimawa ta fito dauke da Leda a hannun ta.d'an kunne da sarka ce sai Turarruka a ciki.

Karasawa tayi ta mikawa Summaya karba tayi tare da yin godiya mata sallama suka fita ita da muhdeen
Mummy k'arasawa tayi d'akinta zuciyar ta cike da sake-sake ,tana ganin Sam batayi sa'ar suruka ba,ta dad'e tunanin hakan lokutan da take ganin pics d'in ta da Mufida ta nuna mata wasu ka ganta ba dankwali sai tulun Karin gashin wasu ba suturu.

Kirki gasu nan dai da sauran su.

Tumawa tayi da maganar da Dady yayi mata na cewar tayi masu fatan alkhairi kawai kada tayi tunanin komai,hakan yasa a cikin xuciyar ta tace Allah ya Sanya alkhairi.

A bangaren Muhdeen da Sumayya kuwa suna tafiya a mota ne sumayyay ta kalle shi tare da cewa,
"Baby na Wai meye alakarku da yarinyar nan ne?"
Ba tare da ya kalle ta ba idanun sa nakan tuk'in da yakeyi ya ce ,
"Wata yarinya kenan?"
Yamutse fuska tayi ta ce,
"Wadda suka shiga daki da Mufida,Mai sanye da Hijabin nan Mana"
"Okay Inteesar kike nufi ko?"
"Eh"
Ta amsa masa a takaice
Dan Jim yayi kafin yace
"Bamu da wata dangantaka ta jini da ita"
Gaban ta ne ya tsananta bugawa,ta kalle shi tare da cewa
"To zaman me takeyi a gidan ku?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Nima kaina ba son zaman yarinyar nan nakeyi ba,hakanan kawai naji na tsane ta a cikin zuciya ta,wallahi bana kaunar zaman ta agidan nan.ke intakaice maki Zaki zance ban taba Jin tsanar wani mahaluki a duniyar nan kamar yadda na tsani ganin yarinyar nan ba.

Sumayya wani irin murmushi tayi wanda sai da hak'oranta suka bayyana,cikin jin dad'in kalaman sa ta ce
"Ai da kasa an Kore ta a gidan"
Da sauri ya kalle ta tare da cewa
"Ke!
Chapter 7 · 0% Book details