← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 99

Sashe 20

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tattare k'asar rigarta tayi da nufin guduwa,kunsan abu ga dogon mutum ai taku biyu yayi ya isa gare ta, kafin ta ankare ganinsa kawai tayi a gabanta yayi mata dirar mikiya.Hannayenta duka biyu yasa ya murd'e mata hannayenta tare da maidasu baya,hakan yasa ta bud'e baki ta saki k'arar azaba da sauri yasa hannunsa d'aya ya toshe mata bakii, yayin da d'aya hannun yana rik'e hannayenta da ya murd'e.Girgiza kai kawai take yi na azaba yayinda Idanuwanta suke tsiyayar da hawaye.girgiza kai taci gaba da yi idanunta na cigaba da zubar da hawaye.Girgiza masa Kai tacigaba da yi amma ko a jikinsa baiji tausayinta ba.

Suna cikin wannan halin ne Jabeer ya turo k'ofar falon ya shigo,turus ya tsaya yana kallon Muhdeen cikin tsananin mamaki ya ce
"Meye haka?wanna wani irin rashin imani ne?"
K'arasawa yayi ya cire hannun Muhdeen daga rik'on da yayi wa Inteesar.yana sakinta ta zube a wurin ta samu damar fitar da kukan zucin da takey.Jabeer harara ya watsa masa .

"Yanzun meye kake aikatawa haka?

Zaka kama 'yar mutane kana azabtar da ita akan meye?"
"Ba azabtar da ita nayi ba tarbiya nake koya mata."
"Eh k'warai kuwa tarbiyya kake koya mata irin tarbiyuar da kake koyawa Asiya da Mufida,idan Asiya da Mufida sukayiwa laifi haka kake ladabtar dasu?"
Ya k'arasa maganar yayin da yake kallon Muhdeen.

"Ai idan sune basasu yi mani irin abunda yarinyar nan tayi Mani ba ballantana har na d'auki irin wannan hukuncin akan su."
Girgiza kai Jabeer yayi tare da ce wa,
"Duk da bansan me tayi maka ba kuma nansan alak'ar dake tsakanin ku ba,amma da dukkan alamu yarinyar nan bata da rashin tarbiyya ko rashin kunya.Ni nasan halinka fa idan ka d'aurawa mutum karan tsana,wata kila ka kure ta ne shiyasa har takaiga tayi maka haka."
Don't tell me that,how dare you gaban yarinya kana gaya mun maganganu tare da bani laifi?salon ta k'ara raina ni ko?."
Ba tare da Jabeer ya sake wata magana ba ya durk'usa gaban Inteesar dake ta k'ok'arin mik'ar da hannayen ta amma ta kasa,har lokacin kuka take,cikin tausayawa ya kalleta ya ce,
"Sannu ko?"
Kai ta gyad'a masa alamun yauwa ba tare da ta yi magana ba.

"Cikin tausasawa ya ce,
"Me kikayi masa ne?"
Cikin muryar kuk ta fara magana.

"Nidai haka nan kawai ya tsaneni banyi masa laifin komai ba, shiyasa ma nace bazan sake zuwa gidan nan ba sai yayi aure yabar gidan su Mufida suka matsa nazo."
Cikin tausasawa ya girgiza kai.

"Kenan ke k'awar Mufida ce?"
Kai ta jinjina masa alamar eh,da ya ke shi Jabeer baisan Inteesar ba kasancewar duk lokacin da yake zuwa bayan sallar isaha'i ne,kuma lokacin Inteesar ta riga tabar gidan.

"To amma me kikazo yi a d'akin sa?"
"Shi ne ya janyoni wai nazo nayi masa gyaran falo"
Kai Jabeer ya jinjina.

"Okay.yanzun ki tashi ki tafi,sannan ina mai matuk'ar baki hak'uri a madadinsa"
Tashi ta yi dak'yar ta dafa hannayen ta mik'e tsaye, ta nufi hanyar fita ta fice Jabeer yabi ta da kallon tausayi.Gwaggo ne ke zaune a falo su day wasu Mata k'awayen Mummy su uku,ganin Inteesar ta fito daga part d'in Muhdeen idanunta sunyi ja alamun kuka yasa ta mik'e dakyar,ta nufi Inteesar ta ce,
"Subhanallahi 'yar albarka me ya same ki?me kikayi je yi d'akin Muhammadu?me yayi maki?

"
Murmushin k'arfin hali tayi tare da ce wa,
"Bakomai Gwaggo kada ki damu"
Ta k'arasa maganar tana mai nufar k'ofar kitchen,bayan ta shiga kitchen d'in fridge ta nufa ta d'auko goran robar ruwa tare da tsiyayawa a kofi tasha.Sai da ta k'ara koge fuskar ta inda hawaye ya gangaro da bayan yatsunta sannan ta nufi da'akin Mufida.

Da sallama d'auke a bakinta ta shiga,kallo d'aya Mufida tayi mata da sauri ta mi'ke ta isa gare ta tare da dafa kafad'arta.

"Inteesar lafiya kuwa me ya same ki naga idon ki alamun kinsha kuke?"
Murmushin k'arfin hali tayi tana kallon Mufida ta ce,
"Kada ki damu kaina ne ke Mani ciwo yanzun zan d'an kwanta,idan na tashi zuwa anjima zai sake ni"
Azeeza ce ta ce.

Ikon Allah daga fitar ki zuwa kisha ruwa shiru baki dawo ba sai yanzun kika shigo kanki na ciwo.Dama kina kukan ciwo ne kamar k'aramar yarinya?"
Ta k'arasa maganar cikin yanyin zolaya.Azeema ce ta d'aura da ce wa.

Ni da naga shiru-shiru Bata dawo ba na tambayi Mufida cewa ga Inteesar shiru,take cewa kila ta tsaya wajen mutumiyarta Gwaggo"
Mufida ta girgiza Kai tare da cewa,
"Nidai nasan bakiyin kukan ciwo sai dai idan 'boye mana zakiyi"
Asiya dake tsaye bakin k'kofar hannunta na rik'e da handle d'in k'ofa ce tayi tsuki tare da fad'in
"Amma kuma da naci kuke,tace bakomai ta a tafi a hakan mana haba da Allah.yauwa ni ba wannan ya kawoni ba,wace ce ta d'auki chargern wayata?

Azeeza ta ce
Nice Aunty Asiya na mance da tawa ce,na shiga ban ganki ba shine na d'auko"
Ta k'arasa maganar tana nuna socket d'in da tasaka charging.

"Okay badamuwa idan kin gama ki kawo mani"
Daga nan ta juya ta fice, Inteesar kwanciya tayi akan gadon ta juya masu baya.

'Bangaren Gwaggo kuwa ganin Inteesar ta fito 'bangaren Muhdeen Tana kuka yasa ta nufi 'bangaren nasa.ko sallama batayi ba ta tura k'ofar ta shiga.

"To shugaban mugaye na Africa,uban me kayiwa 'yar mutane ta fito tana kuka?"
Shiru yayi bai kalleta ballantana ya amsa Mata,bada Kai nake magana ba ka yi mani shiru?nasan dai yarinyar nan bazata ta'ba aikata wani abu da zaisa kayi mata azaba ba,sai dai idan kuskure aka samu,haka ranar ka akan ta watsa maka yayu a rashin sani ka kamata kahau yarfa mata maruka kamar Allah ne ya aiko ka,yanzun ma ka kamata kana jibga to a kunnen ubanka d'an banza mai k'irar yahudawa."
Ba tare da ya kalleta ba ya fara magana.

"A halin yanzun Ina cikin farin ciki,saboda haka kada ki ruguza farin mani cikin da nake ciki.karki manta nifa ango ne"
Harararsa tayi ta ce,
Dalla rufe mani baki ina angon yake,sai dai muna angon don ni banga cikakken ango anan ba,wata kila idan zakayi auren da ake kira aure zan ganka cikakken ango Amma yanzun angogo na gani.Dan zaka auri wananna tambad'ad'd'yar yarinyar zaka kira kanka ango.

Take ya murtuk'e fuskar sa don ya tsani a fad'i kalma mara dad'i akan Sumayyarsa.

Zata bud'e baki da niyyar tayi magana,yayi saurin dakatar da ita da fad'in.

"Gwaggo a halin yanzun kin riga da kin 'bata mani rai saboda haka kada ki tunzurani."
Ri'ke baki tayi tana kallosa.

Muhammadu duka na za ka yi ko me?na tunzura kan d'in,ko uwarka da ubanka za su ce kada na tunzura su ballantana kai.?"
Jabeer ne ya k'arasa gaban Gwaggo cikin sigar rarrashi ya fara magana.

"Allah ya huci zuciyarki Gwaggo kiyi hak'uri ki tafi kada ki biyewa Muhdeen don Allah kinsan halinsa."
"Halinsa na banza ba,yanzun ka fad'a mani gaskiya me yayiwa yarinyar nan?"don nasan ba abunda zatayi masa bak'ar zuciyarsa ce da mugun halinsa ne kawai."
Ahljiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa,
Gwaggo idan har nace ga abunda tayi masa nayi k'arya,nadai zo na tarar ya murd'e mata hannaye ya lan'kwasa mata su baya tare da toshe Mata baki wallahi iya abunda na sani kenan."
Jinjina Kai tayi
"To Allah yayi maka Albarka ya sauke matar ka lafiya ta Haifa maka d'anka namiji, mai sanin darajar mutane da neman albarka irinka."
Murmushi yayi tare da cewa,
"Ameen Gwaggo."
"Ni banma tambayeka ya jikin matar taka ba ko?anya ma zata iya zuwa bikin nan kuwa?"
Girgiza kai Jabeer yayi yana dariya ya ce,
"Ba zata iya zuwa ba Gwaggo saboda cikin nan yana wahalar da ita."
Kai ta jinjina tare da ake tambayar sa.

"Cikin nan nata wata nawa ne?"
"Wata biyar kenan Gwaggo"
"Auren KU watanni biyar kenan ko"
Kai ta jinjina tana dariya ta ce,
"Dakyau namijin gaske,ashe dai jikan nawa ba rago bane,aure wata biyar ciki ma wata biyar lokacin da kukayi watanni tara da aure lokacin cikinta watanni tara sai haihuwa kenan.

Wato baka da wasa kana jefa k'wallo kenan ta shige raga lallai yaron nan ka cika namiji ba lusari bane kai.Ai dam..."
Muhdeen ne ya katseta ta hanyar cewa.

Ba'a irin wad'annan maganganun a gaba na,don na dad'e da sanin cewa baki san alkunya ba."
Kallon shek'ek'e Gwaggo tayi masa ta ce,
"Ubanwa yace dole sai ka saurare mu ka fita mana."
"Kuzo har cikin d'aki na sannan ku ce na fita? ai ba zamanin mulkin mallaka muke ciki ba.Koda yake dama ke nasan haka kike shine ma da ya biye maki."
Juyawa yayi ya kalli Jabeer ya nuna sa da hannu ya ce,
"Kai baka san waye Gwaggo ba ko? shiyasa har take tambayarka sirrin gidanka kake fad'a mata,sai ta dinga terere da sirrin gidan ka.Idan ka biye Mata cewa zatayi ka fad'a mata me ya faru a first night d'in ku,kaga jata ku tafi can d'akinta ku karasa zancen ku ba'a nan ba."
ya k'arasa maganar yana shigewa bedroom.Ta bishi da harara tana cewa,
"Ai sai dai ka shiga ciki,kuma saura kuma naga naka k'wazon jarumi ne ko kuma lusari."
Daga Nan ta fice daga d'akin tana sababi,Kai tsaye d'akin Mufida ta nufa nufa ganin Inteesar kwance tana barci yasa ta fita ko gaisuwar da su Azeema suke mata Bata amsa ba ta fice.

Washe gari gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arziki ana ta shagulan biki.inda kowa yake cin abincin da ransa yake so yasa abunda ransa ke so.

Da misalin karfe hud'u na yamma ana ta Shirin zuwa reception kowa ya saka ankon material d'in da aka fitar saboda reception d'in kowacce tana shiga mitoci ana waucewa dasu.Su Inteesar kuwa suna cikin d'akin Mufida su hud'u.

Mufida, Inteesar,Azeema da Azeeza.Sunci anko inda Azeeza ta tsantsara masu kwalliya sunyi matuk'ar kyawu sosai sai shek'i da k'amshi suke inda suka inda suka dinga fama da Inteesar akan ta dage lallai dole sai ta saka hijabi ita kuma ta dage,dakyar suka shawo kanta ta har ta amince zata saka gyalen.Gashi kayan sun bayyana tsantsar kyawun surar jikinta kowacce ta d'auki wayarta da posa d'inta suka fito.
Chapter 20 · 0% Book details