← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 99

Sashe 61

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shi kuma wayarsa ya d'auka ya kira Jabeer don ya tabbatar an d'auko Umma daga general hospital an kaita asibitinsu, nan Jabeer ya sanar dashi cewa eh yanzun ma zai shiga ya duba ta, sallama suka yi katse kiran,
Janyo farantin yayi ya d'auki k'aramin flask na ruwan zafi ya tsiyaya mata a kofi ya zuba mata milo da madar da suga, dai-dai lokacin da ta fito a hankali ta zauna tana d'an jije le'be, sannubya mata tare da mik'a mata kofin tea girgiza masa kai tayi alamun ba zata sha ba ganin yadda ya had'e fuska yasa ta ka'ba slice bread ya mik'a mata ta da soyayyen k'wan da ya soya.

"Zan shiga nayi wanka, ki tabbatar kin cinye su sannan kije d'akinki kiyi wanka ki shirya mu tafi."
Daga nan ya shige band'akin,jin zasu tafi yasa ta fara shan tea d'in, duk da bata jin dad'in bakinta amma tasan idan bata ci ba zai iya cewa an fasa zuwa, don haka ta tuttura ta bar sauran, tashi tayi ta nufi d'akinta tana tafiya a hankali har ta isa d'akinta, toilet ta shiga ta k'ara gasa jikinta da ruwan zafi sannan tayi wanka, bayan ta fito ne ta sanya riga da siket na atamfa, ba tayi wani kwalliya ba powder kawai ta Shafa a duskarta, sai turaren da ta fesa ta saka hijab har k'asa ta d'auki hand bag d'inta ta saka takalimi, wayarta ta saka a cikin jakkar ta fara takawa a hankali, ganin yanayin tafiyar nata bata iya tafiya yadda ya kamata ne yasa ta cire wannan takalmin da take da tsini, flat shoe ta saka ta fara tafiya a hankali don har yanzun duk da ta k'ara gasa jikinta da ruwan zafi amma har yanzun tana jin zafi a k'asanta musamman idan tana tafiya, lokacin da ta k'araso bakin k'ofar ne ta bud'e ta fita.

'Dakinsa ta nufa da sallama ta shiga cikin sanyin muryarta.

"Assalamu alaikum"
Yana tsaye sanye da shadda sky blue, agogo yake d'aurawa a hannunsa ya amsa da.

"Wa'alaiki salam"
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce,
"Na shirya"
"Me yasa kika shafa turare tunda kinsan fita zakiyi kuma wasu mazan zasu ji k'amshin turaren ya burge su? ko baki san cewa haramun ne matar aure ta saka turare mai k'amshi yayin da zata fita unguwa ba?"
"Na mance ne na fesa"
"To kada ki sake matuk'ar ba kina cikin gida bane."
Da mamaki ta kalle shi tana tambayar zuciyarta me wannan mutumin yake nufi da ita ne, cewa tayi
"Insha Allah bazan sake ba"
Murmushi yayi mata tare da cewa
'Dakyau mar'atu saliha"
Ita dai bata sake magana ba har ya k'araso wajenta, hannayensa biyu ya sa ya zagaye k'ugunta da su, ido ya zuba mata yana kallonta lokaci d'aya yana jin yarinyar har k'asan zuciyarsa, manna ta yayi da jikinsa har k'irjinsu na gogan na juna, narai-narai tayi da ido kamar zatayi kuka ganin hakan yasa ya sake ta ya ce,
"Mu tafi"
Tana gaba yana binta a baya yanyin tafiyar tata ya gani sai a hankali, baiso hakan ba amma ba yadda ya iya tunda ya mata alk'awari zai kaita, idan bai kaita ba gaskiya bai mata adalci ba, da kansa ya bud'e mata murfin motar ta shiga, shima ya zagaya ya zai shiga ne ma'aikatan gidan suka k'araso suna gaishe shi, amsa yayi cikin sakin fuska sannan ya shiga yaja motar suka nufi asibitin.

A can Asibiti kuwa d'akin da aka kwantar da Umman inteesar na musamman ne, don mutum d'aya ne a cikin gadon mara lafiya da goguwar kujera na zaman mutum uku da da fridge sai T.V dake manne a bangon d'akin ga sanyin A.C dake tashi, gaban gadon mara lafiyar akwai kujera da ake ajewa saboda masu jinyar mara lafiya, Mama Huraira k'anwar Umma ce ke zaune a d'aya daga cikin kujeran, don dama ita ce ta kwana da ita take jinyarta, Umma na kwance tana barci k'arin ruwa aka d'aura mata don har ledar tayi rabi, Mufida na zaune akan doguwar kujera tana chatting da wayarta, don ita ce Mummy ta aiko ta kawo masu breakfast.

Turo k'ofar akayi aka shigao tare da sallama, inteesar ce da Muhdeen, Mufida tana ganin aminiyarta a guje ta tashi ta nufe ta tare da rungume ta ta mak'alk'ale ta, janyo inteesar tayi da k'arfi don su shiga cikin d'akin su zauna kan kujera, kasancewar inteesar bata iya tafiya da k'arfi yasa ta d'an wash tare da cije baki ta coge wuri d'aya, ganin hakan yasa Muhdeen dakawa k'anwar tasa tsawa.

"Ke mahaukaciyar ina ce haka? kin d'auka yadda kike biri-biri haka kowa yake? ba zaki bita a hankali ba?"
Cikin shagwa'ba yasa ta ce,
"Haba yaya me nayi na hauka kuma daga na tarbe ta? sai ka fara fad'a?

"To haka ake tarbar mutum a garinku? baki san bata da lafiya bane?"
Inteesar ce ta k'arasa gaban k'anwar Ummanta cikin girmamawa ta gaishe ta, Mama Hure ta amsa mata cikin fara'a, Muhdeen ma ya k'araso ya durk'usa ya gaida Mama Hure tare da mata ya mai jiki, ta masa masa da cewa da sauk'i, duba ruwan da aka d'aura mata yayi tare da duba magungunan da yaga an ajiye a sama durowar da ke gefen gado, kallon Mama Hure yayi tare da cewa zai d'an fita kafin ta tashi sai su gaisa.

"Mufida ya su Mummy da Gwaggo"
Kauda kanta tayi tare da tura baki, ya gane nufinta tayi fushi ne fad'ar da ya mata ne don haka ya ce,
"My lovely sis ya kika kyale ni ne?"
"Ba kaine ba yanzun ka daina so na"
Dariya yayi yaja hannunta suka fita, ita dai inteesar zama tayi ta zubawa Ummanta ido tayi tana tausaya mata ganin yadda ra rame.

Tana nan zaune sai ga Mummyn Muhdeen da Gwaggo sunzo, mik'ewa tayi
da niyyar zuwa ta taro Gwaggo sai taji bazata iya ba saboda yanayin tafiyarta, bayan sun k'araso ne ta durk'usa ta gaishe su, Mummyn Muhdeen ta ce,
"Daughter ya kike fatan kina lafiya"
Sunkuyar da kai tayi ta ce ,
"Alhamdulillah"
Gwaggo ce ta mik'ar da ita tsaye ta ce,
"Tashi 'yar albarka, ya Kuna lafiya ina jikan nawa?"
Kafin ta yi magana ne Muhdeen ya shigo rik'e da hannun Mufuda yana cewa
"Gani nan kaka ta ya kike?"
Fuskarsa d'auke da tsantsar farin ciki, musamman da yaga Gwaggo ya tuna cewa ita ce silar aurensa da inteesar, ada haushin Gwaggo yake kan ta aura masa inteesar amma a yanzun yasan gata tayi masa, ta aura masa irin maccen da yake mafarkin samu, gashi tasan darajar miji bata masa gardama, murmushi yayi Gwaggo ta zuba masa ido ta ce,
"Kai kuma fara'ar me kake ne?"
Ba tare da ya ce komai ba ya durk'usa ya gaida Mahaukaciyarsa.

"Mummy ina kwana?"
Lafiya qalau son ya iyali da aiki?"
"Alhamdulillah"
Umma ce ta bud'e idanunta tare da kallonsu d'aya bayan d'aya, Inteesar ta k'arasa gabanta ta ce,
"Umma ya jikinki?"
Murmushi tayi tare da rik'e hannun inteesar ta ce,
"Naji sauk'i"
"Umma wallahi hankali na ya tashi sosai da naji baki da lafiya"
Murmushi tayi
"Ki kwantar da hankalinki naji sauk'i"
Muhdeen ne ya durk'usa ya gaida Umma ta amsa masa cikin sakin fuska tare da masa godiya, don an fad'a mata shine yasa a dawo da ita nan.
Chapter 61 · 0% Book details