← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 99

Sashe 60

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To kiyi wankan Ina zuwa"
Fita yayi inda ya koma ya cire zanin gadon da ya 'baci,ya shimfid'a sabo, ya nufi toilet da wannan, koda ya shiga ya same ta ta kammala tana k'ok'arin mik'ewa ya k'ara da sauri zai taimaka mata, sai ta koma da sauri ta zauna tare da sunkuyar da kanta, ya fahimci kunyar ya ganta ba kata take,don haka ya fita ya bata wuri, yana fita ta mik'e a hankali towel da ta gani ne ta d'auka ta d'aura, dak'yar take tafiya tana d'an bud'e k'afa har yanzun bata daina tsiyayar da hawaye ba, a hankali ta bud'e k'ofar ganin yadda take tafiya yasa ya mik'e ya nufi k'ofar toilet d'in d'aukanta yayi kamar jaririya, akan gadon ya ajiye ta ya fita, kai tsaye kitchen ya nufa ya had'a mata tea ya koma bedroom d'in magani ya d'auko ya yazo gefenta ya zauna tare da mik'a mata maganin da tea.

"Kar'bi Kisha zai taimaka maki wajen rage zugin da kike ji."
Maganin ya 'ballo ya bata ya ce,
"Kar'bi kisha ko na baki ruwa ko?"
Kar'ba tayi tare da had'iye maganin sannan ta mik'a masa, matsa mata yayi da ta shanye tea d'in sannan ta kalle shi da idanunta da sukayi jazir suka kumbura ta ce,
"Ka ce zaka kaini wajen Umma na ida..."
Kasa k'arasa maganar tayi don ya mata nauyi a baki, murmushi yayi tare da cewa
"Kinsan yanzun k'arfe biyun dare kuwa? ki bari sai gobe."
Kuka ta saka masa ta ce,
"Amma alk'awari ka d'auka cewa idan na taimaka maka zaka kaini."
"Na sani ai zan kaiki da safe amma yanzun ki kwanta ki bari sai gobe da safe muje."
Kafin tayi magana ne ya d'auke ta ya kwantar da ita tare da ja mata bargo, toilet ya koma sai da ya wanke zanin gadon sannan yayi wanka ya dawo ya haye gadon, cikin bargon ya shige tare da janyo ta a jikinsa ya rungume, k'ok'arin janye jikinta tayi amma bau bata damar hakan ba, hannu yasa ya rage hasken d'akin sannan ya ce,
"Kiyi hak'uri inteesar kada kiyi kuka gobe insha Allah zan kai ki, kinga yanzun dare yayi, amma da zaran kin tashi da safe zamu tafi."
Sauraronsa take har yakai k'arshen zancensa, tunda take da shi bai ta'ba mata magana cikin taushin murya ba sai yau bai ta'ba lalla'ba ta ba sai yau, tana cikin tunani ne taji ya ce,
"Wani asibiti aka kaita?"
"General hospital Mufida ta fad'a mani."
"Kada ki damu zansa a d'auko shi daga can a kawo shi Asibitinmu."
Cikin sanyin murya ta ce,
"To"
Ji tayi yana cewa
"Thank you so much for your help, Allah ya maki albarka hak'ika ke ta daban ce a cikin mata,kin sakani cikin farin ciki da Nisha'i kin jiyar dani dad'in da ban ta'ba jin makamanciyarsa ba a rayuwa ta, ina son ki fad'a mani duk abunda kike so nayi maki shi zan maki, ko mene ne matuk'ar bai da'bawa Addinin musulunci ba, ko na siya maki."
Shiru tayi bata ce komai ba, sumbatarta yayi a goshi sannan ya ce,
"Nagode , idan kinyi tunanin tukuicin da zan baki ki sanar dani, dan kin cancanci haka daga gare ni."
Haka yayi ta surutunsa shi kad'ai har barci ya d'auke ta, shi kuma yana ta tunanin halin da ya kasance da ita a daren yau,yarinyar da ya tsana ya wulak'anta bai d'auke ta a komai ba ashe 'yar baiwa ce murmushi yayi yana kallonta yayin da take jin wani abu na fisgarsa kan yarinyar, shima barcin yayi basu farka ba sai da aka kira sallar asuba farkawa tayi ta jita kwance a jikin mutum ga towel d'in duk ya warware , ta mance ba kaya a jikinta sai ta tashi zaune da sauri ta janyo towel d'in ta d'aura, idanunsa a kanta wani lallausan murmushi taga ya sakar mata wanda bai ta'ba mata irinsa ba,kauda kai tayi don bata ma son ganinsa, kallon mugu take masa mara tausayi.

"Kiyi wanka kiyi sallah bari na d'auko maki wani kaya a d'akinki."
Fita yayi ita kuma ta shiga toilet ta watsa ruwan zafi ta d:auro alwala, bayam tayi fito ya mik'a mata kayan ya shiga toilet d'in, saka kyan tayi tana k'ok'arin saka hijab ya fito jallabiyarsa ya saka ya nufi masallaci.

Sai k'arfe shida ya dawo,ya tarar da ita tana barci, kitchen ya nufa ya had'a mata breakfast, tea ne da kwai ya soya mata, yana kitchen Sumayya ta shigo, ta bayansa ta rungume shi ta ce
"Gud morning my love"
Kamar bazai amsa ta ba dai ya ce
"Morning"
"Me kaje yi a kitchen zan wuce na hangoka, ina wannan yarinyar take ne da zaka shiga kitchen da kanka?"
,A takaice ya amsa mata da
"Bata d lafiya"
"To nikan ba abunda zan iya yi ko ciwon ajali take ta fito ta had'a Mani breakfast."
Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce
"Saboda baiwarki ce ko?"
Cikin tashin fahimta ta ce
"Wannan ma sun maka yawa muje muci ko?"
Kallon da taga ya mata sai da hanjin cikinta suka kad'a, don bai ta'ba mata irinsa ba, kai tasye d'akinsa ya nufa ya shige.

"Wallahi bazai yiwu ba ai kullun tare muke cin abinci sai yau ka ce a'a? sai na bika.

Kai tasye ta nufi hanyar bedroom nasa .
*KUYI HAK'URI DA WANNAN BA YAWA*
Daga alk'alamin
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love you oll
Comments and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page5
"Wallahi bazai yiwu ba ai kullun tare muke cin abinci, sai yau kace a'a? sai na bika."
Kai tsaye ta nufi hanyar bedroom nasa, turewa tayi taji k'ofar a datse alqmar ya rufe daga ciki, knocking ta fara yi tare da cewa
"Dan Allah kayi hak'uri nasan na 'bata maka rai, ne yasa kake fushi dani."
Yana jinta yayi mata banza,ajiye farantin da ya jero masu breakfast yayi ya zuba mata Ido tana barci amma tana sheshshek'ar kuka, tausayinta ne ya kama shi duk da cewar ya tsani yarinyar baya jin sonta a zuciyarsa amma yanzun baya jin wannan k'iyayyar a yanzun sai ma tausayinta, yana tuna yadda ta dinga kuka tana rok'onsa ya k'yaleta a daren jiya ya tuna sumar da tayi ta daina motsi, shi kansa yasan cewa da badon tana son ya kaita wajen Ummanta ba da bazai same ta cikin sauk'i ba don yasan ba zata batshi ma ya ta'ba jikinta ba ballanta har ya kai ga biyan buk'atarsa da ita, rashin lafiyar da yayi amfani dashi ne ta hanyar nuna mata cewa idan bata barshi ba to baza ta je wurin Ummanta ba.

Jin yadda Sumayya ke dukan k'ofar tana kiransa kuma yasan zata iya tayar da inteesar daga barci yasa ya k'arasa jikin k'ofar ya fara magana.

"Kinga bana son damuwa don Allah ki kyale ni, idan har kuma kika cigaba da takura mani wallahi idan na bud'e k'ofar nan zaki sha mamaki, ina matsayin mijinki ina da buk'atarki kiyi fatali dani ki fita dadaddare kije party ba tare da izinina ba, ki kwana a can saboda rashin sanin darajar aure da kimar mijinki, a k'ullace nake dake ki kiyaye ni ko nayi maki abunda baki ta'ba tsammani ba."
Baki sake take sauraronsa don tunda take dashi bai ta'ba 'daga mata nurya ba sai yau, kuma koda ya buk'ace ta ta hana shi baya fushi da ita da safe zai sake lalla'ba ta don ta yarda dashi, amma yau sai taga baima damu da ita ba, sai maganar banza da yake fad'a mata, tunawa da tayi tasan waye shi da kansa zai dawo yana lalla'ba ta shiyasa ta nufi d'akinta ta kwanta don batayi barci jiya ba.

Yana jin k'arar tafiyarta yayi tsuki,k'arawa yayi jikin gadon tare da zama gefen inteesar,gashin kanta ne da ya zubo ya rufe mata fuska ne ya gyara mata gashin zuwa baya tare da shafa gefen fuskarta, firgigit ta farka ganinsa yana mata murmushi yasa ta ja baya cikin tsoronsa tana girgiza masa kai hawaye na fita daga idanunta.

Murmushi yayi mata tare da cewa
"Kinga ki kwantar da hankalinki ba abunda zan maki,kinji."
Kai kawai take gyad'a masa kamar wata k'adangaruwa, don tsoronsa ne sabo ya dirar mata musamman idan ta tuna azabar da ya jiyar da ita a daren jiya.

"Tashi kiyi brush kiyi breakfast ko?"
"Ni Umma ta nake son gani."
"Nasani kuma can zan kaiki yanzun ki tashi kiyi abunda na ce kiyi sai kiyi wanka mu tafi."
Mik'ewa tayi dak'yar don ji tayi jikinta na mata ciwo, mudammna k'asanta dak'yar take tafiya, kallon yanayin tafiyar mata yayi ya ce,
"A haka zamu tafi kina tafiya a bud'e? duk Wanda ya kalle ki yasan akwai matsala, ko zaki bari naje ni kad'ai ne na duba jikinta zuwa gobe idan kin warke sai mu..."
Bai kai k'arshen zancensa ba ta sakar masa kuka mai tsuma zuciya.

"Kinga ya isa kiyi hak'uri zamu tafi yanzun nan, je kiyi ki fito."
Shiga cikin toilet d'in tayi sabon brush ta bud'e ta fara amfani da shi.
Chapter 60 · 0% Book details