← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 99

Sashe 23

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jabeer kuwa akan hanyarsu ta komawa gida ne yake tuna irin kallon da Usman yakeyiwa Inteesar,da yadda yadda dinga sakar Mata murmushi babu abunda ya ke hangowa a cikin idon Usaman kamar tsantsar so da yake Mata.Take sai yaji kishi a cikin zuciyarsa.Kallon Inteesar yayi sannan ya maida hankain sa kan driving d'in da yake yi sannan ya jefa mata tambaya.

"Waye shi?"
Kallonsa tayi cikin rashin gane me yake nufi sanan ta ce,
"Yaya Jabeer me kake magana akai?"
"Raina mani hankali zakiyi?waye kika rabu dashi yanzun zakije gurinsa?"
Ya fad'i maganar cikin d'aga murya kamar Yana fad'a.kallon mamaki take binsa dashi yadda lokaci d'aya yanayinsa ya sauya kamar ba Jabeer d'in da sani d'azun ba.

Cikin sanyin Muryarta ta fara magana
"Shine wanda ya kad'eni da mota."
"Yaushe ya kad'e ki da motar?"
"Sati biyu da suka wuce,lokacin da zamu kai d'inkin bikin nan nida Mufida,naga wani makaho yazo kan titi sai na k'arasa don na taimaka masa ya tsallaka Dai-dai lokacin da motarsa ta kawo kai, shine tsautsayi ya gifta ya kad'eni."
Sake jefa Mata wata tambayar yayi da cewa
"Daga Nan kuma sai akayi Yaya?"
"Shine ya kaini asibiti ya biya kud'in komai sannan ya tafi."
Wani tambayar ya sake yi mata inda ya ce,
"Daga nan baku sake had'uwa ba kenan?"
"Mun sake had'uwa saboda yazo gidanmu bayan ya dawo daga tafiyar da yayi."
"Ya akayi yasan gidan ku?kuma meye dalilin zuwansa."
Tura baku tayi,don zuwa yanzun ta fara gajiya da yawan tambayoyin da ya ke mata ba.cikin k'osawa da tambayoyin sa ta ce,
"Lokacin da yaje asibiti ne ya d'auki wayata ya saka number sa ya kira,to anan ya samu number na shine yake kira na a waya,sau d'aya yazo gidanmu gaishe ni."
Bai sake cewa komai ba ya maida hankain sa kan driving d'in da yakeyi har suka k'araso.

K'ofar gidan a waje yayi parking,da sauri ta riga shi fitowa Shima ya fito,tare suka jera zuwa cikin gidan.

A harabar gidan ya tararda Muhdeen da wasu abokan su zaune kan wasu kujeru suna tattaunawa.Ido suka zubawa Inteesar da Jabeer,wani daga cikinsu mai suna Bashir ne yayi magana ya ce,
"Tsarki ta tabbata ga ubangijin halittu,gaskiya Jabeer ya iya za'ben kyakkyawar mace mai kyawun sura da diri."
Salisu ne yayi dariya tare da cewa
"Ai wannan ba matarsa bace."
Bashir ya sake cewa
"To wace ce ita a wurinsa?kodai budurwarsa ce?"
"Bari ya k'araso ka tambaye shi don banida amsar wannan tambayar taka."
Kai tsaye Inteesar ta nufi cikin gidan, Jabeer kuma ya k'araso wajen su sallama yayi masu tare da mik'awa kowannensu hannu suka gaisa.Muhdeen ne ya kalle shi ya ce,
"Daga ina haka?tun d'azun nake jiran k'arasowarka sai yanzun?"
Murmushi Jabeer yayi ya shafi sumar kansa ya ce,
"Eh daga wajen reception na biya wani waje ne sannan na tafi gidana dawowarmu kenan."
"Kenan tun lokacin kana tare da wannan yarinyar?"
"Eh kana da matsala da hakan ne?"
Ta'be baki Muhdeen yayi tare da kauda kansa gefe.Bashir ne ya washe baki yana cewa,
"Ina ka samo wannan zazzafar yarinyar gaskiya ta had'u ta ko ina,tayi mun."
Jabeer ne ya had'e fusaka domin yasan halin Bashir da neman mata kamar bunsuru.watsawa Bashir mugun kallo yayi tare cewa
"Bari kaji Bashir wannan ba irin matar banzan da ka saba mu'amala dasu bane gara ma ka kama kanka."
Gyara zama Bahir yayi cikin d'aukar maganar da mahimmanci ya ce,
Ai wannan ba irin wad'annan can sauran 'yan matan bane,wannan idan na sameta sunnah zan raya don mace ce ta nunawa sa'a."
Gaba d'ayansu suka saka dariya banda Muhdeen da ko kallonsu bayayi.salisu kuwa harda tafi yayi don bai ta'ba Jin Bashir yayi maganar aure ba,sai dai ya dinga kawo matan banza a guest House d'insa.Sharholiyarsa kawai yake Bai ta'ba maganar aure ba sai da yaga Inteesar yau.

Jabeer ya kalle shi yana cewa
"Baka dace da Inteesar ba kwata-kwata,ai ko da girgiza kurna tafi magarya."
Daga Nan ya tafi ya barsu wajen.

Inteesar kuwa tana shiga falon ta tarar da Bak'i mata 'yan biki sallama tayi ta gaishe su,sannan ta nufi d'akin Mummy nan ta tarar da Mummy da mahaifiyar Jabeer sai k'awayen Mummy guda uku.Gaishe su tayi sannan ta nufi d'akin Mufida.

Da sallama ta shiga,suka amsa Mata suna tambayarta Ina suka tsaya ne haka?

"Lapiya kika k'i d'aukar Kiran wayar da nake maki?"
Cewar Mufida da ta zubawa Inteesar ido,Sai a lokacin Inteesar ta tuna cewa wayar na a silent take,ciro wayar tayi taga Miss call d'in Mufida har guda 5.

'Bangaren Usman kuwa Koda ya koma gida ransa a jagule yake,
A falo ya tarar da Ammynsa da Khadija suna kallon news,kallo d'aya Ammy tayi masa ta gane akwai abunda ya faru a can.Don ba yadda yadda yadda fita ba kenan,yanayinsa ya sauya,Khadija ce ta kar'bi ledar hannunsa ta ajiye agaban Ammy.don dama ita ce ta kirashi a waya ta ce idan zai dawo ya biya super market yayo mata siyayya kamar yadda yadda saba duk bayan kwna biyu.

"Lapiya kuwa naga yanayinka ya canza?ko akwai abunda ya faru ne?"
Murmushi ya k'ak'alo ya ce,
"Babu komai Ammyna bari na d'an shiga ciki na huta."
Bai jira cewarta ba ya shige ciki tabishi da kallo.

Washe gari ranar juma'a Gidan Alhaji sani ya cika mak'il da jama'a.'Yan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa,aga abinci nan kala-kala sai Wanda mutum yake so zaici ko yasha,komai sunyishi a wadace.

Da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren Muhdeen da Sumayya akan sadaki naira dubu d'ari biyar murna a wajen Muhdeen Ba'a magana.Haka 'bangaren amarya ma hakan take Dan tafi kowa murna.

Da misalin'karfe biyar na yamma aka tafi d'aukar amaeya don kaita d'akin mijinta Dank'arararren gida ne Wanda akashe naira wajen yinsa.Amarya ma iyayenta sunyi bajinta wajen yo mata order lafiyayyun furnitures.Tunda ga Kan kayan d'aki har zuwa kayan kitchen komai masu tsada ne na kece raini, d'akuna guda biyu aka zuba Mata kaya.

Da misalin k'arfe takwas na dare ana ta shirin zuwa dinner wanda za'ayi a JUSTICE IDRIS LEGBO KUTIGI dake daura da Government house a cikin garin Minna.

Mai makeup aka d'auko inda tazo ta tsantsara wa amarya lafiyyen kwalliya.Tayi kyau kam sai baza k'amshi takeyi tana kyalli,k'awayenta su Jummy sai kod'ata suke suna k'ara fasa mata kai.

A can gidansu Mummy kuwa anata shirin zuwa dinner inda nan ma Azeeza ta sake tsantsarawa Inteesar da Mufida kwalliya,sai faman kod'a kyawun da Inteesar tayi sukeyi,har suna cewa ma ai kila tafi amaryar kyawu.Nan ma sai da suka sha fama da ita akan sanya gyale ba yadda ta iya haka ta biye masu ta fasa saka hijabin da ta saba sakawa.Inda kyawunta da kwarjininta suka sake bayyana don ko mace ce ta kalleta sau d'aya sai ta sake kallonta ballantana namiji.

Maman Ihsan ce
09065327995
Comment and share
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing
Zainab Abdullahi
(maman Ihsan)
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page 2
Kyawunta da kwarjininta suka sake bayyana,don ko mace ce ta kalleta sau d'aya sai ta sake kallonta ballantana namiji.

Ajere suka fito daga d'akin inda suka nufi d'akin Mummy.

Da sallama suka shiga d'akin, Mummy ce da Aunty Maryam sai Mummyn Jabeer,amsa musu sallamar sukayi Mummyn Jabeer ce tayi murmushi tare da cewa
"Masha Allahu'yan matana kunyi kyau sosai kamar kune amaren,Allah ya nuna mani ranar aurenku musha biki.Kai kyawawan 'ya'yana kuzo na rungume ku mana."
Ta k'arasa maganar tana bud'e hannayenta alamar suzo ta rungume su.Mufida da Azeema da Azeeza suka k'arasa suka shige jikinta,yayin da Inteesar ta tsaya tsaye inda take Don Bata san Mahaifiyar Jabeer ba sai sai shekaran jiya ta fara ganinta kuma gaisuwa ce kawai ke had'asu.Hakan yasa ita Bata k'arasa ta rungumeta ba,Murmushi ta sakarwa Inteesar ta ce,
"Zo mana 'yata ya kika tsaya can?"
Hakan yasa ta tako cikin sanyin jikinta ta rungumeta hakan yasa Mufida ta ciro wayarta tayi masu selfie su duka kowacce tana dariya.daga nan sukayi masu sallama suka ce zasu tafi dinner,nan Mummy ta ce da su Anty maryam su shirya lokacin fara dinner yayi.
Chapter 23 · 0% Book details