← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 99

Sashe 55

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsawon mintuna biyu yana tsaye yana tunani idan Jabeer ya sanar da Gwaggo gaskiyar lamarin ya zaiyi, shidai yasan tijarar Gwaggo, duk da cewar matarsa ya ajiye a Hotel ba karuwa ba.

Da haka ya nufi hanyar shiga ta cikin falon,da Sallama ya d'auke a bakinsa ya tura k'ofar, Gwaggo da Jabeer ne suka amsa masa yayin da Inteesar ke kwance a k'afar Gwaggo,tana barci, Duk gashin kanta mai tsayi da bak'i ya bazu ya rufe mata rabin fuskarta, sanye take wata k'aramar riga mara hannu mai kama da singileti pinck colour sai siketa bak'i har k'asa,rigar ya kwanta a jikinta kuma ya kama jikinta,hakan yasa ya bayyana surar k'irjinta,ta kwanta rigingine kanta na saman cinyarsa Gwaggo, ta d'ora hannunta na dama a saman cikinta,barcinta kawai take yi, bayan sun amsa masa sallamar ne ya gaida Gwaggo.

"Barka da yammaci Gwaggo."
Shiru tayi masa kamar bata ji abunda ya ce ba,kauda kanta tayi tana Mai cigaba da kallon T.V da take, gabansa ne ya fad'i kar dai a ce Jabeer ne yayi masa tonon silili, aiko indai haka ne Jabeer bai kyauta masa ba, kuma sai ya ci mutuncinsa, dubansa ya maida ga Jabeer dake zaune shima ya zuba masa ido tare da d'aga
Masa gira d'aya ya dai? kauda kansa yayi daga kallon Jabeer d'in, ya maida zuwa ga Gwaggo ya k'ara cewa
"Ina wuni Gwaggo?"
"Da ban wuni ba zaka ganni?"
Shiru yayi yana kallon Jabeer, yayinda shi kuma Jabeer ke masa murmushi ya ce,
"Da alama kayi mata lafi ne"
"Nayi mata laifi ko kuma kayi mani munafurci ko?"
Sanin inda zancensa ya dosa ne yasa Jabeer shek'ewa da dariya ya ce,
"Kasan baka da gaskiya ne shiyasa ka tsargu kanka, ni ba abunda na sanar da Gwaggo, amma wata k'ila dai zan sanar da ita, ka Fara bincikar laifin da kayi mata tukunna."
Gwaggo ce ta kalli Jabeer ta ce,
"Ka rabu dashi Jabeeru, ba wani bincikar da zaiyi ya sani ai,tunda yasa k'afarsa ya tafi Abuja sau d'aya ya kira mu bayan saukarsa, ga matarsa nan koda sau d'aya bai tambayi halin da take ciki ba."
Sai a lokacin Muhdeen ya kula da irin kayan dake jikin Inteesar, bayan ga Jabeer a wajen zaune sun facing da juna, ransa ne ya 'baci ya fara magana
"Wannan wane irin isakanci ne kuma?"
Da mamaki Gwaggo ta kalle shi tare da nuna shi da yatsa ta ce,
"Kai Muhammadu ka kiyaye ni ka fita a ido na,gidan uwar wa ake isakancin?"
"Haba Gwaggo kema kinsan ko a addinin musulunci wannan ba dai-dai bane, ta yaya matar aure zata tsaya ta kwanta gaban wani namiji da ba muharraminta ba haka,kalli fa ko suturar arziki bata saka ba,ga gashin kanta a waje ki hula bata m saka ba, ga wata 'yar isakar rigar da ko hannu babu."
K'arasawa yayi gabansu ya d'an ja gashin kanta da d'an k'arfi, k'ara ta saki tare da tashi zaune tana mutstsika idanu alamun barcin bai ishera ba,ido ta zubawa Gwaggo don Bata lura da shi ba,tura baki tayi tare da ri'ke kanta ta ce
"Gwaggo akwai zafi."
"Daina Kallo na ga shugaban mugayen nan da yaja maki gashi, saboda mugunta irin taka, dama ina jiran dawowarka ne idan baka sani ba ka sani, tunda ka saka k'afa ka tafi Abuja ka kirani sau d'aya baka sake kira ba, sannan wayar Inteesar da ka amshe ka maida mata da wayarta kaji na fad'a maka."
Dariya Jabeer yayi tare da cewa
"Au dama Abuja ya tafi Gwaggo?"
Kallonsa Gwaggo tayi tare da cewa,
"Ya kake tambaya ta bayan ya ce, daga wajen aiki ne tafiyar ta tashi kuma naga wajen aikinku d'aya, shine baka san ya je Abuja ba?"
Dariya Jabeer yayi
"Wato mutumi na Abuja kaje ko? to me kaje yi ne dan bansan aikin da kaje yi ba,sannan kaga kamar ba Wanda yayi dogon tafiya ba, Abujan ce kuwa ko dai fad'a ne kawai."
Banza da shi yayi dama yasan halin Jabeer da tsokana, kuma yana da tabbacin cewa Jabeer bazai ta'ba tona masa asiri ba, don haka ya maida idonsa ga Inteesar ya ce,
"Saboda tsabar wulak'anci shine kika Sanya wannan banzayen kayan a jikinki ko? sannan kika zo kika tsaya gashin kanki a bud'e kika tsaya a falon Nan bayan kinsan za'a iya yin bak'i a gidan ko?"
"Nifa bansan kowa ya shigo ba ba daga ni sai Gwaggo nayi barci"
Tsawa ya daka Mata
"Zaki je ki sauya kayan ko kuma kisa hijabi ne ko kuma zaki tsaya kina bani labari ne."
Mi'kewa tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya zauna kan kujera, kallonsa Gwaggo tayi ta ce,
"Sai kishin banza da wofi, ka damu da ita ne tunda ka tafi baka iya cewa a bata waya kaji lafiyarta ba?"
Inteesar ta dawo sanye da hijab har k'asa, kallon Jabeer tayi tare da gaishe sa cikin girmamawa.

"Yaya Jabeer ina wuni?"
"Lafiya qalau Inteesar, ya hak'uri da rayuwa?"
"Alhamdulillah, yanzun ka shigo ne?"
"Eh hanya ce ta biyo dani nace bari na lek'o mu gaisa."
"Allah sarki mungode, ya Aunty Maryam?"
"Tana lafiya lau"
Murmushi tayi tare da cewa
"Masha Allah"
Mi'kewa tayi ta nufi kitchen ta dawo d'auke da faranti da ruwa da lemu akai, ajiye tayi a gabansu, dama Muhdeen gefen Jabeer ya zauna, bayan ta ajiye ne Jabeer ya d'auki ruwa yasha, sannan ya ce,
"Amarya ai ba ruwa kad'ai ba har da abinci, don shi nafi buk'ata."
Murmushi tayi ta nufi hanyar kitchen, ba jimawa sai gata ta dawo da faranti Babba, anjera food flask da plates da spoon, a gabansu ta ajiye ganin zata bud'e ta zuba yayi saurin cewa
"Barshu kawai hakan ma mungode"
Komawa tayi ta zauna a mazauninta, Jabeer ya bud'e food flask d'in,tuwon shinkafa ne da miyar agushi da ganyen ugun da yaji naman sa, d'iba yayi ya sauka ya zauna Kan center carpet ya Fara ci, kallon Muhdeen yayi tare da cewa,
"Mutumin Abuja ba zaka ci abincin bane? ko kuma Wanda ka ci a Abujan ya ishe ka?"
Ki kallonsa baiyi ba idonsa na kan waya, Gwaggo ce ta ce
"Tun Abinci da ya ci na Abuja ai yakamata ace yaji yunwa tunda doguwar tariya yayi."
Jabeer ya kece da dariya sannan ya ce,
"Ai Gwaggo ba Zaki Gane bane, baki san Abujar da yaje ba wacce kika sani bane wata ce."
Kallon rashin fahimtar inda zancensa ya dosa ta ce,
"Kai Jabeeru Abujar guda nawa ne?"
"Nidai d'aya na sani amma wannan shalelen jikar naki Abujansa ba d'aya bace, wacce yaje shekaranjiya ba wacce kika sani bane wata ce."
"Kai Jabeeru zancen ya Isa haka nan don naga alamar santi kawai kake, saboda dad'in girkin Jika ta da tayi, don kasan ita ta iya girki mai d'an Karen dad'i, bansan girkinta na sanya sambatau marasa kai ba sai akanka, dama waccan solo'biyar matarka bata iya girki ba."
Jinjina Kai yayi
"Shikenan Gwaggo tunda haka kika ce"
Yana gama cin abincinsa ya wanke hannu, ganin Muhdeen baida niyyar cin abincin ne yasa Inteesar ta tattara kayan ta Kai kitchen.

Bayan ta dawo ne suka cigaba da firar su sama-sama Jabeer ne da Gwaggo suke fira, Inteesar ta lura da tsarabar da aka ajiye d'auka tayi takai kitchen ta dawo ta zauna, Gwaggo ce ta fara Gyangyad'i, fira suka tsakanin Jabeer da Inteesar,inda ran Muhdeen ya sake 'baci kenan,wato da shi da banza duk d'aya a wajenta ko? tasan yayi tafiya ba sannu da dawowa ba komai,bata gaishe shi ba, bata bashi ruwa ba ballantana abinci sannan ta zauna tana hira da wani a gabansa ko kallonsa ma batayi ba, girgiza Kai yayi sannan ya mik'e ya nufi d'akinsa,Yana Jin muryar Jabeer na cewa a fito lafiya Mutumin Abuja, Bai kula sa ba yayi shigewarsa ciki.

Daga nan Jabeer yayi masu sallama ya ya fice abinsa.

Haka rayuwa tayi ta tafiya, yau alhamis yau ya kama gobe Gwaggo zata tafi, Inteesar ta shiga damuwa sosai har kukanta,Wanda hakan kuwa ki jikin Muhdeen, domin shi so yake ta tafi Sumayya ra dawo gidan,kowa da abunda ke gabansa, Muhdeen na cikin farin ciki Inteesar na cikin bak'in ciki,Wanda Gwaggo duk ta lura da yanayin kowanne a cikinsu, kuma tasan tabbas akwai abunda Muhdeen ke shiryawa da ya matsu tabar gidan sai dai ta kasa gano komai.

Zaune suke a dinning table suna Breakfast, Inteesar gaba d'aya ta kada saka komai a cikinta,tana ta tunanin wahalar da tasha a gidan a hannun Muhdeen, dalilin zuwan Gwaggo gidan ne ta samu 'yanci a cikin gidan, to yanzun gibe Gwaggo zata tafi kenan hakan na nufin zata cigaba da wahala ne kamar yadda yake bautar da ita a baya? ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Gwaggo, Gwaggon ma ita take kallo
"Ke 'yar albarka lafiya kuwa?"
Girgiza kai tayi tare da cewa
"Bakomai Gwaggo"
"Akawai komai"
Sunkuyar da kanta tayi tana juya cokali a cikin kofin tea, Gwaggo ta sake magana ta ce
"Kinga idan akwai wani abu ki sanar dani,Kinga ke amana ce a wurinmu, duk abunda kike buk'ata ki fad'a mani idan ina da halin yi maki shi zan maki, idan kuma banda shi zansa mijinki ya maki idan baifi k'arfinsa ba, amma kada kuce na k'ara kwankin da zanyi a gidan nan."
Marairaice fuska ta yi cikin shagwa'ba ta ce,
"To ai abunda zan nema a wajenki ne kika ce kar na nema."
Dariya tayi
"Dama nasan abunda zaki ce kenan, ki nemi wani abun amma ba wannan ba"
Satar kallon Muhdeen tayi sanna ta fara magana
"To ai banda wayar da zan dinga magana da ke da kuma su Mummy."
Kallon Muhdeen Gwaggo tayi sannan ta ce,
"Kaje ka kawo mata wayarta yanzun nan."
Girgiza Kai yayi sanna ya ce,
"To zan bata."
"Ba haka nake son ji ba, cewa nayi kaje ka kawo mani wayarta, idan kuma ban Isa ba ka fad'a mani yanzun na kira Mahaifiyarka na sanar da ita."
Ba tare da yayi wata magana ya mik'a ya nufi d'akinsa, ba jimawa sai gashi ya dawo da wayar ya mik'awa Gwaggo, amsa tayi ta mi'kawa Inteesar, amsa tayi tana murna tare da godiya.
Chapter 55 · 0% Book details