Sashe 53
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da asuba ya ya farka a k'urarren lokaci, don har za'a tayar da sallah hakan yasa alwala kawai yayi ya tafi masallaci,
Ita kuwa wanka tayi ta d'auro alwala tazo ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne tayi azkar kamar yadda ta saba, tana gamawa kuma sai ta tashi ta nufi d'akinta da sallama ta shiga Kallo d'aya Gwaggo tayi mata ta Gane cewa tasha kuka, ganin yadda idanunta suka kumbura sukayi jazir, duk'awa tayi
"Ina kwana Gwaggo?"
Bata amsa mata ba sai ido da ta zuba mata, ita Kam Inteesar batayi tunanin Gwaggo zata fahimci kukan da tayi ba.
"Dukanki yayi ne naga alamar kinsha kuka?,
Kai ta girgiza
"Banyi kuka ba Gwaggo,barcin da na tashi ne"
"Ni zaki rainawa haankali?nasan idon kuka nasa na barci, idan akwai abunda yake maki da baki so ki sanar dani dan Allah."
"Ba komai Gwaggo, hanaki yayi ki fad'a ko?zaizo ya same ni ina nan ina jiransa, tunda ke amana ce."
Gabanta ne ya fad'i tana Allah yasa kada ya sanar da Gwaggo idan ta tambaye shi, mi'kewa tayi ta cire hijabin ta Ciro wani kaya zata sauya,idanun Gwaggo ne ya sauka akan rigar da Muhdeen ya yaga gabanta, da mamaki ta kalli rigar amma sai tayi shiru kawai, Dan tasan Inteesar ba zata fad'a mata ba ko ta tambaye ta,
Yana kwance a d'akinsa Yana waya da Sumayya, inda yake cewa
"Kinga kibar wannan maganar kawai kizo gobe."
"Ya zan zauna gida d'aya da wannan tsohuwar why not ba zaka bari ta tafi ba."
"Kinga idan har kina sona kuma da gaske kinyi missing d'ina to ki bar London ki dawo gobe."
"Ok zan dawo zuwa jibi"
Acikin zuciyarta Tana mamakin shi da yace ta bari Gwaggo ta tafi yanzu ya canza magana, ta'be baki tayi dan bata san dalilinsa ba.
Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page4
A cikin zuciyarta tana mamakin shi da ya ce ta bari Gwaggo ta tafi yanzu ya canza magana, ta'be baki tayi dan bata san dalilinsa ba.
Da misalin k'arfe goma na safe Inteesar ta gama duk ayyukan ta da zata yi na cikin gidan,d'akinsa ya rage kuma yana ciki ba zata iya shiga ba,hatta breakfast ta shirya masu ta jera a dinning table,ta sanar da Gwaggo cewa ta kammala amma Gwaggo Bata tashi ba,yau 'yan fad'a da take yi na rashin breakfast da wuri bata yi ba.
Wanka Inteesar tayi ta shirya cikin riga da siket na atamfa, d'inkin ya mata kyau kuma ya bayyana kyawun surarta da Allah ya mata, powder kawai ta shafa bayan ta shafa mai sai turare mai dad'in k'amshi.
Gwaggo ce da kanta yau taje d'akin Muhdeen don kiransa,samunsa tayi yana waya dan haka ya sallami wanda suke wayan da shi.
"Barka da safiya Gwaggo"
"Yauwa barka dai kaga na shigo maka d'akinku kai tsaye ko?to naga ita tana can ne nasan kai kad'ai ne shiyasa."
Ido ya zuba ba tare da ya ce komai ba,cigaba da magana ta yi
"Nace lafiya dai ko?"
Da mamaki ya kalleta don bai fahimci tambayar da take masa ba,ji yayi ta cigaba da cewa
"Naga alamar jiya akwai matsala tsakaninka da 'yar albarka."
Ido ya zuba mata yana nazari,kafin ya fara tambayarsa kansa cewa kodai Gwaggo la'be take masu ne?Kai ya girgiza Dan yasan da ace taji ba ruwanta da 'boye zata yi magana ne.
"Naga da ta shigo yau da safe gaban rigarta a yage take,kamar tayi kokawa da kura kaima ga shi na ganka kamar wanda ya tashi daga jinya,shin bata baka hakkinka na aure ne ko kuwa dai tana iya k'ok'arinta kaine jarabarka tayi yawa bata iya d'aukar nauyinka?"
Wani irin kallo ya watsawa Gwaggo wanda ita ma bata san ma'anarsa ba,don ita ba ruwanta da kunya ko wani 'boye-'boye,kauda kansa yayi gefe.
"Mtsww matsala ta da kai kenan,idan ana tambayarka kana wani kauda kai saboda mishkilanci,inda Jabeer ya fika kenan da shi na tambaya da yanzun ya bani amsa,amma kai k'aton banza dakai k'aramar yarinya ka kasa yadda zaka shawo kanta,kalli yadda ka koma a dare d'aya lusari kawai, sai Kai ta zama a haka tunda ba zaka fad'a mani damuwarba ballantana na shawo maka kanta, idan kaga dama ka tashi kayi kalaci."
Daga nan ta fice daga dak'in, binta kawai yayi da kallo har ta fice bai tanka mata ba.
A falo ta samu Inteesar zaune akan kujera, ta tsaya tsaye a kanta ta fara magana.
"Ke kuma na dawo kanki, me aka kawo ki kiyi a gidannan?
Cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ta ce,
"Kiyi hak'uri Gwaggo ban gane inda zancenki ya dosa ba."
"Zaki ce haka mana, to bari kiji ba'a kawo ki nan gidan da kici kisha ki kwanta ba, don idan dan abinci ne gidan iyayenki kina ci, idan sha ne a gidan iyayenki kina sha haka sutura ma, ko ba haka ba?"
"Hakane"
"To wani abu ne wanda ya zama bak'o a wajenki dole sai a gidan miji ake yinsa?"
Shiru tayi tana nazari kafin ta ce,
"Wallahi ni Gwaggo bansan inda zancenki ya dosa ba, ban gane me kike nufi ba."
"Dan k'aniyarka baki san hakkin miji akan matarsa ba?
Ko baki san ki biyawa mijinki buk'atarsa ba ne? kin fi son ki kwana cikin tsinuwar mala'ikun Allah? to bari kiji duk ranar da na sake ganin makamancin hakan ya faru dake da mijinki wallahi ranar zaki ga 'bacin raina, daga nan bata sake magana ba ta nufi dinning area, Inteesar mi'kewa tayi cikin sanyin jiki ta bi bayanta, zuba mata nata tayi dai-dai lokacin Muhdeen ya k'araso, k'amshin turarensa ne ya sanar da ita k'arasowarsa, zama yayi d'aya daga cikin kujerun dinning d'in yayin da ita kuma ta zuba masa nasa, k'ok'arin barin wajen tayi sai taji muryar Gwaggo tana cewa
"Ina zaki je baki ci komai ba?"
Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba ta ce,
"Bana jin yunwa"
"Shikenen ke kika sani, idan ma fad'a da na maki ne kike fushi dani, ban damu ba kuma matuk'ar baki sauya ba to ba ruwa na dake."
Daga nan Inteesar d'akunsa ta nufa dan gyara masa,dama irin wannan lokacin take jira, idan baya ciki ta shiga ta gyara har ta fito ma bai sani ba.
A daren ranar ma haka Gwaggo ta sanya Inteesar ta shirya cikin wasu kayan barci masu kyau, har da k'ara ja mata kunne akan kar ta sake gudun mijinta, ita dai Inteesar bata ce komai ba sai da safe tayiwa Gwaggon ta fita.
Tsayawa tayi a falo tana ta sak'e-sak'e matuk'ar ta ce zata tafi d'akinsa ba makawa sai yayi abunda ya ce zaiyi da ita, ita kuma bata k'aunar haka ta faru da ita,don haka ta ce ba zata tafi d'akin ba ballantana ace ya cutar da ita, d'akin da ta kwana shekaranjiya nan ta tafi ta kwanta.
Shima a 'bangarensa bayan ya gama shirinsa na kwanciya barci zama yayi a bakin gadon ba abunda yake sai tunanin yarinyar nan, ya kasa gane gaskiya shin son ta yake ko me? shidai a iya saninsa ya tsani yarinyar ada ko son ganinta baya yi, amma a yanzun baya jin tsanarta a cikin zuciyarsa kamar yadda yake ji ada, kuma shi haryanzun baya jin yana sonta, sai dai abu d'aya ne yake basa mamaki wanda kuma ya kasa gane dalili, shine a duk lokacin da ya kad'aice shi da ita a cikin d'aki d'aya sai yaji gaba d'aya sha'awar kasancewarsa da yarinyar yake ji,ko kallonta yayi sai yaji wani yanayi na buk'atuwa musamman idan ya kalli wani sashe na jikinta sai yaji feelings ya taso masa, ga Sumayya matarsa da sukayi auren soyayya da ita Sumayya idan zata kwanta tsirara a gabansa zai iya tsallake ta ya wuce ba tare da yaji wani abu dangane da haka ba, amma idan Inteesar ce ko yaya ya kalli wani sashe na jikinta sai ya rasa nutsuwarsa,koda Gwaggo ke turo ta d'akinsa baida niyyar ta'ba koda yatsarta, amma da zaran ya ganta sai ta nemi wargaza masa lissafi, shiyasa ba ya iya hak'uri sai ya ta'ba ta, idan kuma ba haka ba shine yake shan wahala don sai ya kwana yana ciwon mara, shiyasa ya fad'a mata duk ranar da ta shigo masa d'aki sai ya biya buk'ararsa.
Kwanciya yayi yana ta juyi shi kad'ai, zuciyarsa sai tunaninta yake,a wannan lokacin ita Kam ta dad'e da barci.
*LONDON*
Dad da Mum d'inta suna zaune a falo, ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya k'erere akansu.