Sashe 14
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ka koma can wajenta tunda ta fini mahimmanci a wurin ka"
Maganar da Sumayya tayi ne yasa Mum gane cewa fushin da Sumayya tayi yana da alaka da Muhdeen, ya yin da Muhdeen ya bud'e baki da niyyar magana ta d'aga masa hannunta dake tsiyayar da jini alamar ya dakata tace,
"Bana bukatar jin komai daga gareka, Get out of my room"
Takarasa maganar tana nuna masa 'kofar fita tana kokarin karasawa garesa da niyyar hankad'a sa waje cikin rashin sa'a ta saki wani gigitaccen 'karan azaba ya yin da tataka wani fasasshen kwalbar turaren da ta fasa, zama tayi a wajen ta kasa tafiya ganin hakan ne yasa Muhdeen ya kalli Mum tare da cewa,
"Mum kada a biye mata mu kaita Asibiti ne kawai, Jin hakan yasa Mum tace,
"Okay bari na d'auko mayafina"
Ta fita ta nufi d'akinta don d'aukar mayafin nata ya yin da Sumayya keta sambatu cikin muryar kuka tana fad'in
"Babu inda zan je ka tafi koma wajen wacce ta fini a wajenka meye damuwar ka dani Auren mu saura wata d'aya da sati uku amma ka barni ka tafi wajen wata banza ka manta dani ina ta zaman jiranka"
Muhdeen zuba Mata ido yayi Yana mamakin want irin mahaukacin kishi ne Sumayya take dashi,dahar zata illata kanta akan abunda bata da tabbas akansa zargi ne kawai,bud'e baki yayi tare da cewa'
"Duk abunda kike tunani ba haka bane,kinyi kuskuren fahimta ce da zakiyi hakurin saurara ta da nayi maki bayanin komai"
Dai-dai lokacin da Mum ta shigo d'akin Tana fad'in kada ya biye Mata su tafi kawai,hakan yasa ya d'auke ta kamar wata jaririya kasancewar Bata iya tafiya sakamakon kwalaben da suka shiga cikin 'kafar ta,sai ihu take Tana Kai masa suka a 'kirjin sa Tana fad'in ya ajiye ta Amma Ina baiko sauraren ta har sai da ya bud'e murfin gaban motar ya direta yayin da Mum ta shigo baya 'ko'karin bud'e murfin motar Sumayya tayi Amma Ina ya riga yayi locked din motar ba Halin ta fita horn yayi Mai gadi ya wangale masa 'kofar gate d'in ya fice a guce.
Iya Gaje Mai gyara masu d'aki ne ta shiga dakin Sumayya Don ta gyara 'barnar da tayi,itama tayi mamaki matu'ka 'barnar da tayi ta yau tafi ta kullum yawa ganin jinin dake malale akan tiles d'in d'akin ne yasa ta jinjina Kai tana ta magana ita kad'ai Tana cewa,
"Kai amma wannan yarinyar anya kanta d'aya kuwa? ace mutum ya dinga yin abu kamar na mahaukata? yarinya Sam bata da tarbiyya da sanin yakamata waye zai shigo d'akin nan yace mai hankali tayi wannan aikin?
Tajawa iyayen ta asara,Koda yake su bazasu damu ba ai sun Saba da halin ta kuma su suka d'auka kome taga dama tayi dai-dai ne uwa Babu kwa'bawa uba Babu harara komai tayi sai dai a zuba Mata ido Ina Bata it's komai ba Ana Shirin aurar da ita wallahi Ina tausayawa mijin da zai aure ki."
'Bangaren su Gwaggo kuwa suna Isa 'kofar gidan jabeer kuwa Bayan direban yayi horn Mai gadin ya bu'de masa ya Cinna hancin motar cikin gidan, jabeer dake Shirin fita idonsa ne ya sauka akan kakar tasa mahifiyar Babansa da sauri ya Karasa ya bud'e Mata murfin motar yayi ta jefo kafa kafarta dakyar ta fito rungume ta yayi cikin farin cikin ganin ta yace,
"Uwar gida na sai yau kikaga damar zuwa gidan mijin naki har Ina Shirin zuwa biko"
"Dariya tayi Tana fad'in,
Ai ko kayi biko ba dawowa zanyi ba,Don tunda kayi Mani kishiya ka rage kula dani "
Karasawa yayi gurin Mummy ya gaishe ta cikin girmamawa,ta amsa masa cikin sakin fuska tare da tambayar sa ya Mai jiki,Mufida ma ta gaishe sa daganan suka karasa cikin gidan.
A falo suka zauna,shi kuma ya nufi bedroom d'in maryama a kwance ya same ta kamar yadda barta,ya sanar da ita zuwan su Mummy mi'kewa tayi cikin karfin hali Hannunta ya ri'keta suka nufi hanyar falon,Bayan sun Isa falon ganin idanun su Mummy yasa ta zame Hannunta daga nasa,ta karasa ta du'kusa ta gaishe su tare da zama akan center carpet din falon, Gwaggo Dada ce tace,
"Wannan kishiyar tawa da alamu cikin nan na wahalar dake ko?
Uhmm koda yake gwara haka yanzun zaku San irin wahalar da iyayen KU suka Sha akanku ku Kara sanin darajar iyaye ai yanzun ma aka fara wasan"
Jabeer ne da ya 'karaso falon dauke da lemu da ruwa a cikin tray ya ajiye tare da duban Gwaggo yace,
"Waishin dubiya kikazoyi ko kuma kin zo kisamun mata a gaba da maganganun ki need?"
"Ai gaskiya na fad'a mata
Wanda zai hau sama ya taka leda ai baiyi komai ba tukunna, jibi fa yadda take langwa'bewa kamar an tsoma tsumma a cikin ruwa"
Dariya sukayi gaba d'ayan su banda Maryam data kwa'be fuska kamar za ta yi kuka, jabeer ya kalleta yace,
"Kada ki damu Gwaggo haka take da sannu zaki saba da ita"
Umma CE tace,
"Ya jiki Maryam"
Murmushi tayi tare da cewa,
"Da sau'ki Mummy"
"Allah ya 'kara sau'ki"
Cewar Mummy, fira suka d'an ta'ba kafin sukayi masu sallama, Jabir har wajen mota ya rakasu sai da suka fice sannan ya koma cikin gidan.
'Bangaren Muhdeen kuwa suna tafiya a Kan hanyrsu ta zuwa Asibiti Sumayya tayi-tayi ya dakatar da motar Bai kulata ba hakan yasa ta dinga juya sitiyarin motar ta kowane 'bangaren, hakan yasa motar ta ku'buce masa ta dinga tangal-tangal akan titi Mum said salati takeyi ta gama tsorata da lamarin 'yarta, Muhdeen sai 'ko'karin 'kwace Hannunta yakeyi amma abin yaci tura ababen hawa sai kaucewa suke suke suna sauka daga Kan titin, tsawar da Mum ta daka mata ne yasa ta cire hannunta tacigaba da kuka, sannan ya samu yayi control d'in motar parking yayi sannan ya fito Yana bawa jama'ar dake gefen titi suka parking Ha'kuri ya basu, wasu basu kulashi ba wasu kuma suna zaginsa wai bai iya tu'ki ba ya d'auki mota ya hau titi zai kashe al'umma, bai ce dasu komai ba ya shiga motar Kai tsaye ya nufi Asibitin sa.
B'angaren su Gwaggo kuwa daga gidan Jabeer Mummy ta Umarci Direban ta yakai su gidansu Inteesar, Kai tsaye gidan ya nufa dasu, bayan sun gaisa da Umma tayi masu jagora zuwa d'akin Inteesar shigarsu yayi dai-dai da farkawar ta daga d'an gajeren barcin da tayi,Yunwa ce ke kwakular cikin ta yasa ta farka, ganin su Gwaggo da Mummy sannan ga 'kawar ta Mufida yasa ta sakin murmushi,Bayan sunyi sallama ta amsa masu ne suka zauna kan tabarmar dake shimfid'e a d'akin ya yin da sai Mufida ce ta haura kan katifar tare ri'ke hannunta cikin tausayawa tace,
"Sorry my besty ya jikin ki?"
Kwa'be fusaka tayi kamar za ta yi kuka sannan tace,
"Wallahi Yayan ki mugu ne ba yadda ban ro'kesa kara yamun allurannan kum..."
Had'iye sauran maganar tayi sakamakon hararar da Umma ta watsa Mata
Murmushi Mummy tayi tare da cewa
" 'Yata kina tsoron Allura ne haka?
"
Gyada k'ai tayi tare da sunkuyar da k'ai kasa.
Mummy ce ta cigaba da magana tace,
"To yanzun ya ciwon kan naki?"
"Da sau'ki Mummy tunda na tashi barcin nan naji jikin nawa ya d'an mani sau'ki sosai"
Amsar da tabawa Mummy kenan ba tare da ta d'ago Kai ba, don ta lura tunda tayiwa Muhdeen rashin kunyar Nan Umman ta ta canza Mata fuska.
Gwaggo ce tace "to Allah ya baki lafiya yarinyar kirki"
Inteesar ce ta d'auki jakkar Mufida don tasan Bata rabo da kayan za'ki a cikin jakkar ta hakan yasa ta bud'e jakkar ta Ciro biscuit da chocolate ta Faraci
"Dariya Mufida tayi tare da cewa yanzun haka har yanzun bakici komai ba ko?"
Murmushi tayi tace
"Wallahi bakin nawa ne ba taste shiyasa banci komai ba"
Mummy ce tace
"Amma sai da na fad'awa son cewa ya siye maki fruits a hanya, kenan bai siya ba kenan ko?"
Gabanta ne ya fad'i jin tambayar da Mummy tayi mata, don bazata iya fad'awa Mummy irin wula'kancin da ta yi wa d'anta ba.
Waige-waigen tayi inda ta watsawa Muhdeen fruits d'in a jikin sa,taga an gyra wajen tasan aikin Ummanta ne, sunkuyar da k'ai tayi kafin tace,
"Ya siyo Mummy"
Da yake Mummy bata cika bin Kwakkafi ba yasa tayi shiru, don tasan indai Umarni tabawa d'anta Umarni Yana binta koda bayaso.
Fira suka d'an ta'ba kafin sukayi masu sallama suka tafi, amma Mufida tace bazata tafi yanzun ba sai tayi jinyar Aminiyarta.
'Bangarensu Muhdeen kuwa suna isa asibitinsa kujeran keke na d'aura marasa lapiya aka d'orata akai don bata iya tafiya, bayan an shigar da itane ya Fara aikin cire mata kwalaben da suke shiga kafar sai sannu yake ya jero mata amma sai tayi banza dashi kamar Bata jishi ba, cikin kankanin lokaci ya gama mata dressing Mum d'inta na tsaye akansu bayan ya gama Mata duk abunda yakamata yayi Mata ne ya d'auke su ya mayar dasu gida Bayan ya had'a Mata magunguna duk da ta'ki yarda yayi mata allurar da zai rage mata zogi.
Kai tsaye gida ya nufa yanda ya samu Gwaggo da Mummynsa a falo ya gaishe su, ya juya zai wuce part d'insa part d'insa Mummy ta lura da d'an jinin da ya 'bata masa riga cikin kid'ima tace,
"Son Mai ya faru dakaine?"
Cikin son 'boye Mata yace,
"Ba komai Mummy kawai na gaji ne, zan je na d'an yi wanka na huta"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa,
"karya ba d'abi'ar ka bace kada ka Fara yanzun, nasan yanayin ka idan gajiya ke damunka,hakazalika nasan yanayin ka idan akwai
damuwa a tattare dakai,idanunka kad'ai na kalla nasan akwai damuwa a tattare dakai,shin akwai damuwar da d'a zai 'boyewa mahaifiyar sa?"
Shiru yayi cikin sanyin jiki yabasu abunda ya faru Tundaga lokacin da ta ta Umarceni shi yakai Inteesar gida da Kiran da Mufida tayi masa Video calla ta gansa da Inteesar har zuwa haukan da tayi a d'akinta da Wanda tayi suna cikin Motar har suka kusan yin Accident bai 'boye masu komai ba.