← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 99

Sashe 37

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dama ni ce mai aikin da ke zuwa kullun ina gyara gidan lokacin da baki nan,na ji labarin kin dawo ne yasa nayi sammako ko akwai aikin da zan taya ki da shi."
Kafin Inteesar tayi magana ta ji Muhdeen ya fara magana
"Ai ba ita ce matar gidan ba,matar gidan bata dawo ba tukunna,so it's wannan bata buk'atar'yar aiki don ita ma 'yar aikin ce."
Jinjina kai Baaba kande tayi
"To Alhaji zan cigaba da zuwa ina aikin Koda matar gidan bata dawo ba kamar yadda na saba yi a kwanakin baya?"
"Ba buk'ata Koda ta dawo wannan ce 'yar aikin da zata dinga mata aiki,sabida haka aikinki ya k'are,amma kafin nan ina zuwa."
'Dakinsa ya nufa, sai gashi da kud'i kimanin naira dubu d'ari ya mik'a mata amsa tayi tana godiya duk da ta rasa aikin ta tasa ran dogaro dashi amma kud'in zata ja jari dasu.

"Nagode Alhaji Allah ya saka da alkhairi,ya k'ara arziki da wata wadata."
Ficewa tayi tare da yi masu sallama cikin jin dad'i
Kallonsa ya maida ga Inteesar fuskar nan a tsuke,yayinda ita ma ta kallesa cikin girmamawa ta ce,
"Ina kwana?"
Tsuki ya ja tare da cewa
"Na sallami mai aikin gidan nan daga yau ke zaki maye gurbinta,aikin da takeyi naki sai ya ninka na ta,don ita falo da kitchen kawai take shiga ta gyara ke kuma daga yau na kafa maki doka wajibi ne a gare ki bayan falo da kitchen da Zaki dinga sharewa kina gogewa duka bedrooms d'in gidan nan guda takwas, da toilets nasu guda takwas wajibine ko wace rana sai kinbi su d'aya bayan d'aya kin share kin goge su kin wanke ko wane toilet,sannan ina son na ga ko ina na gida na a tsaftace banason k'azanta,sannan ba sau d'aya ba safe da yamma Zaki dinga aikin, idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira."
Shiru tayi tana tunanin uban aikin da wannan bawan Allah ya d'ora Mata,bata gama nazari ba taji muryarsa yana cewa.

"Ki jirani nan Ina zuwa"
"To"
Daga nan ya nufi d'akinsa ba jimawa ya fito hannunsa d'auke da keys ya mik'a mata.

"Kar'bi wad'annan makullayen ki Fara da wancan d'akin"
Ya k'arasa maganar yana nuna mata d'akin Sumayya,daga nan ya koma cikin d'akinsa ya barta nan tsaye,cikin sanyin jiki ta k'arasa cikin falon Sumayya tare da duban saitin da taga ya mata nuna mata, tsayawa tayi tana k'arewa falon kallo a zuciyarayarta ta ce,
"Na fahimci mutumin nan so take kawai ya wahalar dani,ya za'ayi manyan falo guda biyu tare da bedrooms guda takwas ko wanne da toilet da ga kitchen guda biyu kowane falo da dinning romms da table da chairs ko ina sai na shere na goge,kuma safe da yamma harda d'akunan da ba kowa a cikinsu ba datti sukeyi ba tunda ba'a shigarsu amma suma wai safe da yamma."
Goge k'wallan da ya gangaro mata tayi tare da cewa
"Allah ka ka bani hak'urin zama da shi"
Bud'e k'ofar d'akin Sumayya tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama,turus tayi tare da dafe k'irji ganin yadda d'akin duk a hargitse komai kaca-kaca ga kgilasai da aka farfasa da kwalaben turarurruka kala-kala ga suturu duk a yayyage,katifa a gefe pillows a watse mirror a tarwatse photon Sumayya da ta gani a manne a bangon d'akin ne ya tabbatar mata da cewa d'akin Sumayya ne a zahiri tayi magana.

"Oh ni Inteesar mai ya faru da d'akin nan ne kamar anyi girgizan d'aki?ta ya ya zan fara wanna aikin ne?kuma da dukkan alamu d'akin Sumayya ce to ina ita Sumayyar take ne?kuma me ya faru da d'akinta haka?"
Sanin ba Wanda Zai amsa mata tambayarta yasa ta fara tunanin ta Ina zata fara,ganin takalmin dake k'afarta irin masu taushin nan ne idan ta taka kwalba zata iya huda takalmin ta shiga k'afarta yasa ta fita dan canza takalmin da ke k'afarta,ba
Ba jimawa sai ga ta ta canza takalmi ta sanya wani flat shoe da da abunda zata zatayi shara ta zuba,katifar ta fara ja ta jingine da gadon ta kwashe pillows d'in abunda ya bata mamaki shine,kayan suturar da ta gani a k'asa ta fara d'agawa abun da ya bata mamaki shine ganin duka suturar a yayyage ba mamora,har cikin closed d'in ta shiga abun mamaki suturan dake cikin wurin duka a yayyage suke haka ta dinga kattara kayan da kwalaben sai dai wad'anda ta ga robace ba kwalba ba da kuma wada'anda suke a gwangwani ba su fashe ba ta kwashe ta jerasu gaban mirror d'in don ba abunda ya same su.

Tsawon lokaci ta d'auka tana gyara d'akin Sumayya kafin ta kammala,ta shirya d'akin tsaf ta gyara shi ta wanke toilet sannan ta janyo k'ofar ta fito.

Haka tabi sauran two rooms d'in duk ta gyara kafin sannan ya rage saura d'akinsa, k'wank'wasawa ta yi yana jinta yayi banza da ita, har sau uku amma ko gezau yana zaune kan sofa sai da ya ga dama ya ce,
"Shigo"
Turo k'ofar tayi tare da sallama
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaiki salam"
Tsayawa tayi kanta a k'asa tsawon mintuna goma tana tsaye amma bai ce mata komai ba,tsuki ya yi.

"Dalla malama idan ba za ki yi magana ba ki fita ki ban waje"
Cikin rawar murya ta ce,
"Na gama da sauran d'akunan ne naka ya rage shine na zo na gyara"
K'arar k'ofar falo sukaji alamun suna da bak'o,hakan yasa ya fita don zuwa dubawa.

Kids ya bud'e k'ofar Mufida ya gani d'auke da basket an jira flasks d'in abinci ciki, murmushi ta sakar masa
"Barka da safiya Yaya
Shima murmushin ya sakar Mata
"Yauwa kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah,dama Mummy ce ta ce na kawo maku breakfast"
Yana k'ok'arin kar'bar basket d'n ta ce,
"Yaya gaskiya sai naga besty na zan tafi"
,hanya ya Bata ta shiga ta ajiye basket akan center table.

Okay tana d'akina zauna na kirata"
Zama tayi akan kujerar dake falon tana jiran inteesar.koda ya shiga tana gyara gadon ya sanar da ita cewa ta zo murmushi ta yi cikin jin dad'i ta fito yana biye da ita a baya,Mufida na ganinta ta mik'e ta nufeta a guje ta fad'a jikinta,muryar Muhdeen suka jiyo yana cewa
"Ke Mufida meye haka ki bi mani amarya a hankali fa ka da ki yi mani illa baki San ba na son abinda zai wahalar mani da ita ba?ki barta ta ji da kanta."
Inteesar ce ta bisa da kallon mamaki,bai gama ba ta mamaki ba sai da taga ya sakar murmushi tare da kashe mata ido d'aya.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
Maman Ihsan
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Andullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.

Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, Idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne Mai kashe auren wawa.
*SADAUKARWA*
Wannan shafin naku ne masoyan Inteesar 'yan group d'in INTEESAR HAUSA NOVEL,inajin dad'in comment naku na book d'in nan sunayenku bazai lissafu ba,ina godiya da addu'arku gare ni Allah yabar k'auna.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page3
Inteesar ce ta bisa da kallon mamaki,bai gama bata mamaki ba sai da taga ya sakar Mata murmushi tare da kashe mata ido d'aya,mamaki da Al'ajabi suka hana Inteesar motsi kallonsa kawai take kamar gunki,jan hannunta da Mufida tayi ne ya saka ta sakin murmushi tana cewa.

"Ya dai wannan kallon haka kamar yanzun kika fara ganinsa ba tare kuka kwana a gidan ba,koda yake ba zaki gaji da kallonsa ba don yaya na na musamman ne samun kamarsa sai an tona."
Murmushin yak'e Inteesar tayi tare da cewa
"Yauwa Mufida na manta waya ta a gidanku tun kafin a kaini gidan Hajiya Bilkisu,don kwanakin da nayi gidanta ma duka ba waya a hannuna."
"Okay to Ina kika aje wayar ne?"
"A d'akin Yaya"
Murmushi Mufida ta yi tare da cewa
"To shikenan zan d'auko maki anjima idan zan kawo maku lunch,amma ki daina kiransa da Yaya don yanzun kunzama 5&6 kamata yayi ki canza masa suna na masoya mai dad'i kin gane ko?"
Ta'be baki Inteesar tayi,tare da kallon Muhdeen sai gani tayi ya galla Mata harara sunkuyar da Kai k'asa tayi , Mufida ta cigaba da cewa.

"To Ni zan tafi sai na sake dawowa."
Fuskar tausayi cikin marairaicewa ta ce,
"Mufida tun yanzun zaki tafi ki barni ni kad'ai ki bari ki yini dani mana ko zaki d'ebe Mani kewa, pls aminiya ki tsaya kinji."
Kafin Mufida ta yi magana Muhdeen yayi saurin cewa.

"Kinga Mufida aiko ki akayi kije ki isar da sak'o kince mungode,zaki iya tafiya ki gaida mani Gwaggo da Mummy."
Murmushi tayi tare da kallon Inteesar
"Karki damu my besty zanzo zuwa na musamman na wuni dake kinji."
Murmushi Inteesar ma ta maida mata tare da cewa.

"Shikenan ba damuwa"
Zuba mata ido mufda tayi tana nazartar yanayin Inteesar,don tasan Inteesar farin sani yanayin yanda ta ganta da dukkan alamu tana cikin damuwa,amma sai ta share zancen ta barshi kila saboda auren da aka yi mata ne kuma ba lallai tana son wanda aka aura mata ba kuma gashi Bata saba da shi ba kila shiyasa ta damuwa amma a sannu zata saba da shi.

Sallama ta yi masu daga nan ta fice,dubansa ya maida ga Inteesar fuskarsa a tsuke ya fara magana
"Idan ta zauna a nan gidan uwar me zata yi maki?bari kiji na fad'a maki doka ce bana buk'atar bak'i a cikin gidana,kada ki tara mun k'awayenki bana buk'atar kowace mace tazo mani gida babu wacce zata zo gidan nan da sunan zuwa wajenki,ko wace ce a wajenki kuwa Ina fatan kin gane."
Kai ta jinjina
"To amma me yasa zaka Hana kowa zuwa wajena?kuma ko a gidan kurkuku nake ai baza'a hana a ziyarce ni ba ballantana gidan aure na."
Da mamaki yake kallonta
"Ke!
Chapter 37 · 0% Book details