← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 99

Sashe 12

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can fall kuwa bayan angama girki Anjera a Dinning table kowa ya hallara Mummy, Muhdeen da Gwaggo ya yin da Dady ne kadai baya nan.Mufida ce ta fito cikin tashin hankali tana fadin
"Mummy gaba daya na duba ko Ina banga Inteesar ba Ina ta shiga?"
Dai-dai lokacin Inteesar ta fito daga part din Muhdeen dafe da kanta, jin alamar tohuwar mutum yasa suka waiga dukkan su sauka zuba mata ido suna kallonta da mamaki, ya yin da Mummy tayi saurin mikewa ta rike hannunta cikin mamaki tace,
"Daga ina kika fito?Mai ya kaiki part d'in son?"
Mummy ta kara rungume ta tana fad'in
"Subhanallahi jiki yayi zafi, zazza'bi ne ya rufe ta"
Janyo hannunta tayi suka karasa dinning room dinta zaunar da ita kan kujerar dake kusa da ita.Ba yadda Mummy batayi ba akan Inteesar taci abinci taki da kyar tasha lemon da Mummy ta tsiyaya mata a cup, Mummy ta kalli Muhdeen ta ce,
"Son"
D'agowa yayi ya kalleta tare da cewa,
"Na'am"
"Ka d'auko kayan aikin ka sannan ka dauki Inteesar a motarka ka kaita gida kayi Mata treatment din da ya dace kafin ka dawo,sannan kafin KU nufi gidan su ka biya ka siye mata fruit saboda bata ci abinci ba"
Cikin bada umarni tayi maganar, kallonta yayi ganin yanayin fuskar ta ba sauki yasa yace,
"To Mummy yadda kika ce haka za'a yi"
Kallonta ta maida ga Inteesar ta ce,
"Inteesar ga yayanki zai kaiki gida yayi maki abunda ya dace kafin nima na zo"
Kai Inteesar ta gyada ba ya yin da gabanta ya ci gaba da fad'uwa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*
Page1
Kai Inteesar ta gyd'a yayin da gabanta gaba da fad'uwa.

"Uhm wannan marukan da tasha ba dole tayi rashin lapiya ba?

Yanzun haka ba Wanda ya ta'ba Mata wannan Marin,ko uwar ta ubanta nasan bazasu yiwa wannan nitsatsiyar yarinya Marin nan ba Amma Rana tsaka wani katon banza ya more ta."
Gwaggo ce tayi maganar yayin da karasa bayan Inteesar Tana shafa kyakkywar fuskar Inteesar.

Muhdeen ko kallonta baiyi ba yayinda ya Mike ya nafi part dinsa fuskar Nan a muturke.Mufida ce to janyo hannun Inteesar tare da cewa,
"Muje na rakaki mota,idan na dawo daga gidan Yaya Jabeer matar sa Bata da lapiya ne zamuje da Mummy mu gaishe ta,idan muka dawo zan biyo gidan naku Allah ya baki lapiya"
Inteesar tace ,
"Ameen "
yayin da suka nufi hanyar fita,Kai tsaye parking lot suka nufa Inda Mufida ta bude Mata murfin gidan gabar motar.kai Inteesar ta girgiza tare da cewa,
"Baya zan zauna"
Ba musu Mufida ta bude Mata bayan motar ta ahiga,zamanta keda wuya sai ga shi Shima ya karaso hannun sa rike da akwatin magunguna,murfin motar ya bude yashiga ganin Bata gefen sa yasa Kai idon sa baya,ganin ta dukunkune yasa yace Mata.

"Niba direbanki bane ki tashi ki dawo gaba"
Mufida ce tace
"Ya Ina ga kamar zatafi yin Balanced a baya tunda nac...

"
Had'iye sauran maganar tayi ganin irin kallon da yake Mata ne yasa tayi shiru.bude bayan motar tayi ta kama hannun Inteesar Dan ta taimaka ta fito,a hankali ta fito da taimakon Mufida Dan har jiri take ji Yana neman dauke ta.Bayan ta zauna gaban motar ne ya figi motar suka bar gidan.

Sai da ya biya ya siye Mata fruits kamar yadda umma ta Umarce shi.Tundaga Kan lemo,kankana,Apple, Abarba inibi da ayaba sannan ya kama hanyar gidan su Inteesar din kasancewar yasan gidan ya ta'ba Kai Mummy.

Dai-dai lokacin da ya Isa kofar gidan ya juya ya kalli Inteesar,ganin idon ta a lumshe kamar Mai bacci.Dai -dai lokacin ne kuma Kira Sumayya ya shigo wayar Video call ne.daga Kiran yayi ganinta sanye da shaddar da suka shirya sawa sunyi anko su tafi uawan shakatawa.lumshe kyawawan idanun sa yayi tare da bude su yace,
"Mai Baby kinyi kyau sosai"
Murmushi tayi tare da cewa,
"Thanks Amma ya bangan ka da naka a jikin Ka ba?kayi lettin zuwa waje na yakamata ace minti talatin da suka wuce ka iso Amma shiru"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace,
"Ki bani minti talatin zan karaso yanzun Nan insha Allah"
Turn baki tayi sannan tace,
"Kana Ina ne yanzun?"
"Ina kofar gidan su Inteesar"
Rasss Gaban ta ya dadi tace,
"Wace Inteesar"
Saita secreen din wayar yayi dai dai yanda Inteesar ke zaune gefen sa idonta alumshe.

Take Sumayya Gaban Sumayya ya Fadi ganin Inteesar a cikin motar Muhdeen yayin da ita Tana can Tana jiran sa Amma shi Yana can wurin wannan yarinyar.

Take taji wasu zafafan Hawayen kishi suna kwaranya a idanun ta muryar kuka tace,
"Nagode da abunda kayi Mani "
Tana kokarin kashe wayar ne yayi saurin cewa,
"Kinga dakata ki saurare Ni nayi maki bayanin abunda ya daru"
"Want bayanin zakayi Mani?cewa Inteesar tafi Ni mahimmanci a wirin ka ne da yasa ka shanyani kusan awa d'aya Ina jiranka yayin da Kai kake can wajenta"
"Kinga ki tsaya nayi maki bayanin yadda akayi"
Kara fashewa tayi da kuka,Don dama Tana da zafin kishi Bata tsaya sauraren sa ba ta katse kiran.

Juyawa yayi ya kalli Inteesar da ta lumshe ido kamar Mai bacci yayinda duk Tana Jin maganar da suke.

"Fita"
Ya fada Mata a takaice,yayin da Shima ya fito ya rufe marfin motar.da'kyar ta iya bude marfin motar ta fito jiri ne ya d'ebe ta tayi luuu zata fad'i. a guje Muhdeen ya Karasa gare ta ya tare ta ta fad'a jikin sa.

Cikin wata iriyar kasalar da ta dorar masa lokaci guda yace,
"Kiyi a hankali"
Same jikinta tayi ta jingina da motar saboda ganin takeyi komai na jujjuya Mata.

Karasawa yayi bakin kofar gidan tare da yin sallama,Yana Nan tsaye Umma ta fito sanye da Hijab.zubawa kyakkywan saurayin Mai kwarjini da haiba ido, Muhdeen kyautatawa ne ajin farko dogo ne fari fuskar sa zagaye da kwantaccen saje da yayi luf a fuskar sa Gashin kansa ma haka yake kamar ba na bakin fata ba ga madaidaitan idanun sa Mai masu kyau da kwarjini.

Durkusawa yayi cikin girmamawa ya gaida Umma.

"Ina wuni Umma?"
"Lapiya qalau"
Ta amsa masa cikin sakin fuska
'Dan Jim yayi Don ya gane cewa Umma Bata sanshiba yasa yace,
"Dama Inteesar ce bataji dad'i ba shine Mummy tace na na kawo ta nayi treating d'inta kafin su karaso"
Jin haka yasa Umma ta fahimci cewa shine Muhdeen din da ake fadi.nuna mata Inteesar da ta jingina da jikin motar yayi tare da cewa,
"Umma jiri takeji shiyasa nayi sallama Don azo a taimaka Mata"
Da sauri Umma ta karasa ta tallabota tare da had'a ta da jikin ta suka nufi cikin gidan.

Acikin d'akin Inteesar din ta kaita yayin da ta koma tare da bawa Muhdeen izinin shigowa.Har dakin tayi masa jagora hannun sa dauke da akwatin magunguna sai ledar fruit din da ya siya Mata.

Tana kwance akan katifar ta ya kalle ta tare da cewa
"Tashi zaune Kisha fruits din kafin nayi maki allura ,Kinga ba komai a cikinki da kikaci"
Shiru tayi masa tare da tura baki Tana kunkuni
.Umma CE to daka Mata tsawa Tana fadin
"Wai lapiyar ki Yana maki magana kinyi banza dashi ba taimakon ki zaiyi ba"
Hawaye ne ya cika Mata ido tace,
"Umaa kiyi hakuri indai taimako ne daga wurin say bana bukata ya tashi kawai ya tafi"
Umma shiru tayi ta zuba Mata idanu Don ita a tunanin ta allura ce bata so shiyasa take fad'in hakan.

Sake magana yayi a karo na biyu yace,
"Dakin daure kinci wani abun ko kadan ne*
Cikin tsiwar da Bata San Tana da ita ba ta Fara magana Tana fad'in
"Dalla mallam ka tashi ka dauki tarkacen ka bana bukatr ganin ka a rayuwa ta,ko a hanya bana fatan sake had'uwa da Kai.Kuma gidan KU bazan sake zuwa ba idan kaga kafata duk wulakancin da kaga dama kayi Mani Ni na jawowa kaina "
Shiru yayi ya zuba Mata ido Yana mamakin yadda har ta iya bud'e baki tayi masa magana gatsai haka...

Bai karasa tunani da yakeyi ba ya sake Jin murayar ta Tana cewa.

"Ka tashi ka fita bana kaunar ganin ka a rayuwa ta,na tsane ka irin tsanar da ba ta'ba yiwa 'Dan Adam shi ba.Ba zaka sake gani na a gidan KU ba ballantana..."
Bata Kai aya ba taji Umma ta daka Mata tsawa Wanda yasa Inteesar fashewa da kuka Tana fad'in
" Umma Don Allah ya fita wlh idan na kalleshi zuciyata tafasa takeyi"
Numfashi taja alamun maganar ma karfin hali
ne,sannan tace,
"Da ace Kaine likitan da zakayi Mani treatment na samu lapiya gara nayi ta zama da ciwo"
Ledan fruits din da ya siyo ta dauko ta watsa masa su a jikin sa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
Wannan kagaggen labari ne ban Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*
Page1
Ledan fruits d'in da ya siyo ta d'auko ta watsa masa su a jikin sa.

Umma da ranta ya gama 'baci ne ta fita waje,ba jimawa sai gata ta shigo da zabgegiyar bulala,ta nufi Inteesar da niyyar za ga Mata bulalar Amma cikin zafin nama Muhdeen ya shiga tsakani Yana ba wa Ummi hak'uri.
Chapter 12 · 0% Book details