← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 99

Sashe 15

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jikin Mummy ne yayi sanyi ta kasa magana, Gwaggo ce ta dinga fad'a tana cewa,
"Ai dama na fad'a maka wannan ba matar auren ka bace, bata dace dakai ba, ashe bayan rashin tarbiyya da take fama dashi harda ta'bin hankali?

Yanzun da kwananka sun kare da ta kashe ka, ina fatan dai yanzun zaka rabu da ita ka nemi wacce ta dace dakai"
Juyawa tayi ta kalli Mummy da tayi tagumi sannan tace,
"Fatima"
Mummy ta d'ago ta kalleta tare da cewa,
"Na'am Gwaggo"
Gwaggo ta cigaba da cewa,
"Na san cewa ban isa da d'anki ba ya rainani baya d'aukar maganata da mahimmanci, amma ina mai baki shawara cewa idan har kina son rayuwar d'anki da kwanciyar hankalin sa to ki hana sa auren wannan mahaukaciya tun a waje tayi yun'kurin kashe shi ina ga anyi auran ai sai dai ta da'ba masa wuka tace zata kashe shi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
Wannan Kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*
Page1
"Nasan cewa ban isa da d'anki ba ya rainani baya d'aukar maganata da mahimmanci, amma ina mai baki shawara idan har kina son rayuwar d'anki da kwanciyar hankalinsa to ki hana shi auren wannan mahaukaciya, tun a waje tayi yun'kurin kashe shi ina ga anyi auran?

Ai sai dai ta da'ba masa wuka tace zata kashe shi."
Tana kaiwa 'karshen maganarta ta mi'ke ta nufi d'akinta, jikin Mummy ne yayi sanyi, kallan Muhdeen tayi tace,
"Idan ka gama abunda zakayi ka sameni a d'akina"
Bata jira cewarsa ba ta wuce ta nufi d'akinta, jiki a sanyaye shi ma ya nufi part d'insa
Bayan sallar isha'i Mummy tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah tana Addu'o'i, Muhdeen ne yayi knocking yana jiran ta bashi izinin shigowa, bayan ta idar da addu'a ta bashi izinin shigowa, da sallama d'auke a bakinsa ya shiga bayan ya zauna ya kalleta cikin girmamawa yace,
"Barka da dare Mummy"
"Yauwa"
Ta amsa masa a ta'kaice, shiru ya d'an biyo baya karin ta kalle shi ta Fara magana,
"Muhammad"
Jin yadda ta kira sunansa da Muhammad ne yasa ya tattara gaba d'aya hankalinsa da nutsuwarsa akan ta, don yasan bata cika kiran sunan sa kai tsaye ba sai dai ta Kira sa da son, ta cigaba da magana tace,
"Ba na son nayi maka dole akan abunda nake so nafi son na baku dama ku za'bi za'bin ranku akan koma meye matukar hakan bai sa'bawa addinin musulunci ba, musamman akan magamar aure tunda shi aure ba abu bane na wasa kuma ba ni ce zanyi maka zaman auren ba kai da kanka ne shiyasa nafi son kai da zakayi zaman auren ka neme wacce ka ke so take son ka ba tare da anyiwa ko wannen ku dole ba domin d'orewar zaman lapiya da kwanciyar hankalin ko wannen ku, maganar da Gwaggo tayi fa abun dubawa ne, domin jikina yayi sanyi da lamarin yarinyar nan yakamata kayi nazari sosai akan maganar Gwaggo kuma kayi la'akari sosai akan abunda ya faru, naso ace nitsatsiyar yarinya ka samu mai sanin yakamata mai tarbiyya da ri'ko da addini, ba wai Umarni nake baka akai ba shawara ce idan tayi maka idan kuma har yanzu kana nan akan bakanka to shikenan Allah ya tabbatar muna da alkhairi.

Kai ya jinjina dare da cewa,
"Ameen ya rabbi Mummy nagode, ki tayani da addu'a"
Kai ta jinjina Don ta lura da cewa 'Danta yayi nisa sosai akan Son Sumayya baya jin kira, don ta lura laifinta ma baya son ana fad'a, lura da hakan yasa tace,
"Kullum cikin maku Addu'ar nake Allah ya tabbatar maku da abunda yafi zama alkhairi a gareku"
Amsawa yayi da Ameenn kafin ya mi'ke ya nufi 'kofar fita, ya juyo ya kalli Mummy yace,
"Ina Mufida ne tunda na dawo naga alamar bata gidan nan"
Murmushi Mummy tayi tace,
"Ina kuwa zaka ganta tana can tana jinya"
Kallon ta yayi cikin rashin fahimtan inda maganarta ta dosa yace,
"Jinya kuma Mummy?Yaushe ne ta Fara rashin lapiyar ?"
Dariya Mummy tayi
"Ai ba jinyar kanta takeyi ba,jinyar Aminiyarta ce Inteesar,kasan sha'kuwar dake tsakanin su barci ne kawai yake rabasu"
Shiru yad'anyi na lokaci kafin yace,
"Amma duk da haka dare yayi yanzum yakamata ace ta dawo gida"
Wayar sa ya Ciro daga cikin aljihun jallabiyar daya Sanya a jikinsa, Number Mufida ya lalubo my little sister sunan da yayi serving number ta dashi kenan,Danna Mata Kira yayi tare da Kara wayar a kunnen sa,
Mufida dake zaune Ita da Inteesar suna cin tuwon shinkafa da miyar zogale Wanda Umma ta girka,sai Santi take,Don taji dad'in girkin sosai,ita ko Inteesar dakyar taji loma uku Don Bata Jin dad'in komai,Wayar ta CE tayi ringing yasa ta duba ganin sunan Mai Kiran ne yasata sakin Murmushi,My lovely brother shine sunan da tasa masa ,d'agawa tayi tun kafin tayi magana tajiyo muryasa yana cewa,
"Me kikeyi a gidan mutane dai-dai wannan lokacin?yanzun Nan kidawo gida"
Bai jira cewarta ba ya katse Kira Don Bai Bata damara tayi magana ba,kallon Inteesar tayi cikin sanyin murya tace,
"Kinga Yaya Wai ma dawo gida dare yayi,"
Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace,
"Kinji Yaya Wai na dawo gida yanzun dare yayi"
Da sauri Inteesar ta kalle ta tare da cewa,
"Ba kinyi mani al'kawarin cewa tare Dani Zaki kwana ba?"
Shiru tayi ma 'Danyi kafin ta saki murmushi ta kalli Inteesar cikin jinda tace.

"Na samu Mana mafita cikin sau'ki,Dady zan Kira na sanar dashi cewa zan kwana tare dake bakida lapiya,nasan bazai hanani ba."
Murmushi Inteesar tayi tace,
"Gaskiya Kam nima nasan cewa bazai hanaki kwana a gidanmu ba"
Wayarta ta d'auka tare da lalubo number Dady,bayn ta Kira number ne ta Kara wayar a kunne bugu biyu ya d'aga tare da cewa
" Assalamu Alaikum"
Mufida tayi murmushi tace,
"Wa'alaika Salam Dady Barka da dare ya aiki?"
"Alhamdulillah yanzun ma insha Allah zan kamo hanyar gida"
Ya 'karasa maganar Yana 'ko'karin kashe Kiran,Jin muryarta Tana magana yasashi dakatawa Yana sauraren ta.

"Dady dama Ina son sanar dakai ne Inteesar ce bata da lapiya Ina gidansu zamu kwana tare da ita ne"
Cikin sauri hankali a d'an tashe yace,
"Subhanallahi me yake damunta?bakuje Asibiti bane?"
Murmushi tayi tare da cewa,
"Kada ka damu Dady da sau'ki,Yaya ya dubata ya Mata allura da magunguna"
Ajiyar zuciya ya sauke yace,
"Okay okay ki bata wayar"
Mi'kawa Inteesar wayar tayi,bayan ta ka'bi wayar ta Kara a kunne.

"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaiki Salam Inteesar ya jikin naki da sau'ki ko?"
"Eh Abba da sau'ki Alhamdulillah"
"To Masha Allah, Allah ya baki lapiya yasa ya zama kaffaran jiki,ki maida hankali wajen Shan magani kinji 'yata Allah yayaye maki,saida safe"
Daganan ya kashe Kiran inda ya shiga bayan motar sa direban sa yaja suka kama hanyar gida.

Mufida tayi murmushi tana kallon kawarta tace,
"Allah sarki yanzun gobe Ni kad'ai zan tafi school,gasky zanyi kewarki sosai Allah dai ya baki lapiya,gashi this time muma Shirin kammala secondary d'in mu zamu zama 'yan matar jami'a"
Dariya ta kece dashi Tana fad'in,
"Wai waya ganmu a jami'a shikenan fa mun zama manyan Mata,Koda yake mum wuce yara tunda a yanzun dukan mu kusa almost 18 years,yanzun cikin kasashen waje wata 'kasa kike son muyi karatun mu a can?"
Murmushi Inteesar tayi tare da cewa,
"Waye ubana dazan tafi kasahen waje karatu? niba 'yar kowa ba bazankai kaina inda Allah baikaini ba ko anan Nigeria ma idan nasamu Abba ya..."
Bata Kai 'karshen zancenta ba tayi shiru ganin irin 'bacin ran da tagani a fuskar Mufida,
Cikin rashin fahimtan fushin nata tace,
"Mufida me ya faru Naga kin canza fuska yanzu-yanzu?"
Tura baki Mufda tayi tace,
"Ba dole na 'bata rai ba tunda kin nuna mun cewa nidake ba Abu d'aya bane,har zakice Wai ke 'yar gidan waye da Zaki karatu waje,bayan kinsan duk abunda Dady da Mummy sukayi Mani zasuyi maki"
Murmushi Inteesar tayi tare da fad'in
"Mufida nasan iyayenki ne suka d'auki nauyin karatuna lokacin da mahaifina ya rasa kud'in da zai biya Mani School fee suka d'aura daga inda ya tsaya,yanzun muna Shirin kammalawa,Banda suturu da sauran ababen bu'kata wannan ma kad'ai ya Isa Allah ya saka da alkhairi,yanzun kina maganar zuwa wata 'kasa ace Nima dani?ke Ni Koda zancigaba da karatuna to anan Nigeria ne kuma a Niger state, IBRAHIM BADAMASI BABAN GIDA(I.B.B.

LAPAI)
Marairace fuska Mufida tayi tace,
"To muje Al-HIKIMA University na Ilori mana"
Shiru Inteesar tayi batare da tace komai ba.
Chapter 15 · 0% Book details