← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 99

Sashe 54

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dad Mum gobe zan koma gidan miji na"
Da mamaki Dad ya kalle ta
"Akan me zaki koma gidansa? mutumin da tunda kika taho bai saka k'afa yazo ba shine zaki koma gidansa? bayan kinsan cewa danginsa da kakarsa ba k'aunarki suke ba kiyi zamanki an
an, bana son kije inda za'a wulak'anta mani ke alhalin kinfi k'arfin wulak'anci."
Murmushi tayi tare da cewa
"Kada ka damu Dad mijina yana sona, shi kad'ai ma ya ishe ni ban damu da kowa yak'ini ba, sannan wannan kakar tasa ba zamu zauna inuwa d'aya da ita ba, tun farko bata sona, sannan muna tsaka da cin amarcinmu ta sa akayi mani kishiya, hmm bashi ta d'auka tasa nayi nesa da miji na tsawon wata d'aya, yanzun haka tana cikin gidan ita da 'yar lelenta wacce ta aura masa Inteesar take ko wace ce? oho masu amma bazan sauka a gidan ba sai nan da 1 week da zaran ta bar gidan ni kuma zan koma gida na yayin da zan k'untatawa rayuwar Inteesar, wallahi sai tayi nadamar auren miji na."
Sai a lokacin Mum tayi magana ta ce,
"Aure dai sun riga sun masa,kuma suna k'aunarta fiye da ke, saboda haka kada kije ki aikata abunda zaisa kiyi dana sani bada yawu na ba."
"Hmm ita ce da dana sani bani ba sannan kuma kada ma kiyi yawu Mum, don na lura yanzun baki k'aunata kamar kin janza hali ba Mum d'in da na Sani da ba, kuma wallahi da bakinsa ya fad'a mani cewar ba son yarinyar yake ba, ya tsane ta kada na d'auke ta kishiya na d'auka cewa 'yar aiki aka kawo mani,ita zata dinga mani aiki, shine dalilin da yasa na hak'ura na janye k'udiri na akanta, da badon haka ba da sai na illata ta."
Dad ne yayi ajiyar zuciya ya ce
"Yanzun ke kad'ai zaki koma daughter?"
"Lokacin da nazo ni kad'ai nazo ba tare da kowa ba kuma ra'ayin kaina ne, to yanzun ma ni kad'ai zan koma dan ra'ayin kaina."
Tana gama fad'ar haka ta juya ta koma, da ido kawai suka bita don idan ta fad'i magana ba ta sauraron kowa.

Washe gari da safe dukkansu suna Kan dinning table suna breakfast, Muhdeen ne ya kalli Gwaggo tare da cewa
"Gwaggo zan d'anyi wata tafiya ta kwana biyu, so zaku ji shiru baku ganni ba."
Gwaggo ne ta ajiye kofin tea da take sha yayin da Inteesar kuma tayi shiru kamar bata ji ba,inda Gwaggo ta ce,
"Wani gari zaka?"
"Birnin tarayya zanje?"
"To Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, wani lokaci zaka tafi?"
"Yanzun idan na fita zuwa asibiti daga can bazan dawo nan ba,sai bayan kwana biyu na dawo."
"To Allah ya tsare ka ya kaika lafiya ya dawo muna da kai lafiya."
Ameen ta rabbi kaka ta, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce,
"Baki ce komai ba kodai kunyi sallama jiya dadare ne."
Cikin sanyin murya ta ce,
"Allah ya kiyaye hanya"
Ta'be baki yayi don har yau yana jin zafin maganar da tayi masa inda yake ce mata zai mutu ta ce masa idan ya mutu kwanansa ne suka k'are,wato k'iyayyar da take masa har ya kai haka?idan ya tuna zancenta kawai sai yaji ransa ya 'baci.

Gwaggo ce ta katse masa tunani ta hanyar cewa
"Lafiya kuwa ko akwai abunda yake damunka ne?"
"Kai ya girgiza tare da murmushin yak'e yace,
"Bakomai Gwaggo, bari na tafi"
Daga nan ya nufi falo Kan kujera ya d'auki k'aramar jakarsa ya rataya a kafad'arsa,daga nan ya juyo ya kalli Gwaggo da take d'aga masa hannu.

"Ke 'yar albarka ba zaki zi ki raka mijinki ba?"
Bai kula su ba ya nufi hanyar fita, Inteesar tabi bayansa saboda maganar da Gwaggo tayi mata,yayin da Gwaggo ta zauna a kujeran falo.

Yana gaba tana biye dashi a bayansa, yana jin k'arar takun takalminta,bai juyo ba kuma bai tsaya ba, har suka k'arasa wajen motorsa ,yana shiga yayiwa motar key yabarta nan tsaye a wajen ko kallonta bai yi ba.

Ita kuma taji zafin share ta da yayi don haka ta juya ta koma ciki.

A asibiti ma ya sanar da cewa zaiyi tafiya zuwa Abuja,duk da cewar Jabeer d'an uwansa ne kuma amininsa bazai iya fad'a masa gaskiyar inda zai je ba, shiyasa Koda Jabeer ya tambaye shi ya ce Dady ne ya aike sa.

Bayan yabar asibiti hotel ya je ya kama masu d'aki na tsawon kwanaki bakwai, shida Sumayyarsa,isowarta kawai yake jira yaje Airport ya d'auko ta.

Da misalin k'arfe d'aya na rana bayan ya idar da salla ne ya nufi Airport d'auko ta.

Akan hanyarsu ta zuwa Hotel ne yana Driving ya d'an juyo ya kalleta
"Ya su Dad da Mum duk suna lafiya?"
Murmushi tayi tare da cewa
"Lafiya lau suke suna gaishe ka"
"Shine kika tafi kika nisanta kanki da ni ba tare da kinyi tunanin halin da zan shiga ba ko"
Yamutse fuska tayi
"Baby mubar maganar nan kawai, dan wallahi zaka sa na tuno da abunda nake k'ok'arin cire shi a Raina."
"To shikenan tunda bakiso na bari"
Hirarsu suke har suka k'arasa Hotel d'in, inda sukayi order na abincin da suke so, ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya ta zauna gefensa, kallonta yayi tare da cewa
"Banga kinyi sallah ba?

Kada dai kice mani fashin sallah kike ki sakani cikin wani hali."
Dariya tayi sannan ta ce
"Ba fashin sallah da nake."
Murmushi yayi tare da cewa
"Alhamdulillah, to banga kin tashi kinyi sallah ba."
Yamutse fuska tayi
"Sai anjima zan had'a da la'asar nayi gaba d'aya."
Dafe goshinsa yayi
"Sumayya wai har yanzun baki daina jinkirta sallah ba?"
"Shikenan bari na tashi nayi"
Mi'kewa tayi ta nufi toilet don d'auro alwala,binta da ido kawai yayi ya ce,
Allah ya shirya
Tsawon kwanaki biyu yana tare da Sumayya,idan ba lokacin sallah ba ba abunda ke fitar dashi daga Hotel d'in, kullun sai yayi waya da Gwaggo da su Mummy ba Wanda yasan ba Abuja yake ba,kowa ya d'auka yana Abuja, a ranar ne kuma Sumayya ta ce ta gaji da zaman Hotel d'in,tana son su d'an fita, haka kuwa akayi suka fita suka d'an shak'ata, a kan hanyarsu ta komawa Hotel d'inne dai-dai kwanar da zasu shiga Jabeer yazo wucewa ya hanto Muhdeen da mace a gaban Motarsa,da mamaki ya tsaya yana kallonsa har suka shige,sannan yaja motarsa ya wuce cike da mamaki.

Bayan ya koma gida yana zaune a falo ya ciro wayarsa layin Muhdeen ya kira, Muhdeen da yake zaune a kujera Sumayya tayi folo da cinyarsa wayarsa ta soma ruri dubawa yayi tare da d'aga wayar.

"Hello Jabeer ya akayi ne?"
Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa
"Kana ina ne?"
"Ya kake tambaya ta bayan kasan na tafi Abuja"
"Me kaje yi a Abuja?"
"Saunawa zan sanar dakai Dady ya saka ni wani aiki"
"Shi aikin baida suna ne ko kuma na kira Dady na tambaye shi wani aiki kake masa, nasan dai bazai 'boye mani ba."
Cikin d'aga murya Muhdeen ya ce,
"Bai shafeka ba, kada ka shiga hurumin da ba naka ba"
"Bansan yaushe ka zama haka ba, amma bari yanzun nan naje gidanka na d'auko Gwaggo sannan na biya na d'auko Mummy sai na kawo su ka fad'a masu aikin da kakeyiwa Dady wanda su bazasu iya sani ba."
"Ka kawo su Ina?"
"Safara Hotel, inda ka ajiye mace da sunan kana Abuja."
A zabure mi'ke tsaye Sumayya dake kwance saman cinyarsa har ta fad'i.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09055327995
Loveu oll
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.

Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page5
A zabure ya mi'ke tsaye, Sumayya dake kwance saman cinyarsa har ta fad'i.

"Look Jabeer ba yadda kake tunani bane, kasan waye ni bazan ta'ba aikata abunda ya kaucewa shari'a ba, duk abunda kaga nayi to bai kauce, hanya ba."
"To wace ce ka ajiye a Hotel tsawon kwanaki biyu?"
"Mata ta ce"
"Wace matarka.?"
"Sumayya ce,kasan akwai takun sak'a tsakaninta da Gwaggo kuma zamansu waje d'aya akwai matsala, hakan yasa na ajiye ta anan har zuwa ranar da Gwaggo zata bar gidan."
Ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa
"Idan 'bera nada sata daddawa nada wari, haka zalika idan anbi ta 'barawo abi ta mabi sawu."
"Kaga ba wani zancen Hausa zaka tsaya kana mani ba, maganar gaskiya Gwaggo ta tsanar mani mata ne kawai,ba gaire ba dalili."
"Itama matar taka harda halinta yasa aka tsane ta, kaima kasan matarka nada matsala."
"Ni banga matsalarta ba, kaga sai anjima."
Daga nan ya katse kiran, don baya son Sumayya taji maganar da sukeyi.

Washe garin ranar ne ya sanar da Sumayya cewa zai koma gidansa, don dama kwana biyu ya ce zai yi, kullun da safe kafin ya tafi Asibiti zai je, ya duba ta, kafin ya tafi Asibiti, kuma idan ya tashi kafin yaje gida zai biyo wajenta.

Haka dai ta hak'ura badon ranta yaso ba, shi kuma ya nufi gidansa akan hanya ya tsaya harda 'yar tsaraba ya siye ya tafi dasu gidan, a harabar gidan yaga motar Jabeer yayi parking a gefe, sai da gabanasa ya fad'i don kada Jabeer dai abunda ya ce zaiyi shi yake k'ok'arin yi, don ga motarsa nan a gidan hakan na nufin yazo d'aukar Gwaggo ne ya kaita Hotel inda yake tare da Sumayya? tambayar mai gadin gidan yayi yaushe Jabeer yazo gidan? ya sanar da shi cewa yanzun.

'Daya daga cikin ma'aikatan gidan ya kira, yasa shi ya d'auki ledojin tsarabar da ya dawo dasu,fruit ne da kayan ciye-ciye danginsu chocolate cake da snacks.
Chapter 54 · 0% Book details