← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 99

Sashe 70

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy tana zaune kan sallaya tana azkar na yammaci, tana ta rok'awa Inteesar sauk'i a wajen Allah, bayan ta idar ne tana cire hijabin taji ana knocking a k'ofar bedroom nata, tasan Dady baya gida Mufida na asibiti Gwaggo na barci a d'akinta, mamaki ne ya kamata waye zai shigo har bedroom bak'o dai iya karsa falo,bada izinin shigowa tayi ta zubawa k'ofar idanu, ganin Muhdeen ne yasa ta tamke fuska dan ranta ya 'baci idan ta tuna da abunda yayiwa Inteesar.

"Assalamu alaikum"
Wa'alaika salam"
Ya k'araso ya durk'usa k'asa ya gaishe ta
"Ina wuni Mummy?"
"Lafiya lau"
Shiru yayi na tsawon mintuna biyar ba wanda yayi magana, d'agowa tayi ta kalle shi taga ya sunkuyar da kai kuma yana durk'she be zauna ba, kauda kanta tayi tare da cewa
"Ya dai ina fatan dai lafiya?"
"Lafiya lau Mummy, dama na d'auka tazo nan ne?"
Kallonsa tayi tare da cewa
"Wace ce ta zo nan?"
"Inteesar nake nufi."
"Ce maka tayi nan zata zo? to nidai banganta tazo ba, amma ka shiga d'akin kakarku ka tambaye ta ko tazo nan tana d'akinta kafin ta k'araso nan."
Jinjina kai yayi tare da cewa
"To bari naje na gani ko tana can"
Mik'ewa yayi ta bisa da kallo ya fice don zuwa d'akin Gwaggo.

Gwaggo na zaune a bakin gadonta tana cin goro Muhdeen ya shigo d'akin ba tare da yayi mata sallama ba, kaallon mamaki take masa tare da cewa
"Yau naga ja'irin yaro d'akin kafura ka shigo da ba zakayi mani sallama ba? d'an banza mai suffan yahudu da nasara, ko nayi kama da kaba'ira ce da ba zakayi mani sallama ba."
Bai tanka ta ba ita kuma bata fasa fad'a da take ba, kallonta yayi tare da cewa
"Ba wannan ya kawo ni ba, Ina mata ta take?"
Kallonsa take shek'ek'e take kafin ta ce,
"Ka d'auke ta inda ka ajiye ta."
Kauda kanta tayi ta cigaba da taunan goronta, ganin ta share sa ne yasa ya k'ara mata magana yana cewa
"Bata gida kuma bata wajen Ummanta ba inda nake tunanin zata je da ya wuce nan."
"Kai ka fita a Ido na, ka kiyaye ni na fad'a maka dan tsabar ka raina ni idan uwarka ce zaka shiga mata d'aki haka ne? ko kuma zakayi mata magana haka?

Bansan inda matarka take ba ko ce maka tayi waje na zara zo da zaka titsiye ni da tambayar inda take? wata kila ma ba nisa tayi ba ta koma gida kazo kana damu na, ka fitar mani a d'aki ko yanzun nan na kira ubanka a waya yazo yayi mani iyaka da kai."
"Ank'i a fata daga d'akin naki"
"Haka ka ce?"
"Eh haka na fad'a kuma haka kika ji."
Wayarta ta ciro daga k'asan filo tana cewa
"Yanzun ubanka zai mani katanga da kai."
Tana shirin kiran wayar Dady bayan ta lalaubo number dak'yar tana kashe ido dan bata gane wayar sosai, tana kara wayar a kunnenta.

Cikin zafin nama ya fisge wayar, tare da sakawa a aljihu ya kalle ta ya ce
"In banda masifa da kika saba da shi daga tambaya ina mata ta sai bak'ar magana?"
"Ka bani waya ta kuma kaje can gida matarka nasan tana gida ba inda zata tafi ba saninka."
Jefa mata wayar yayi sannan ya nufi k'ofar fita, jin muryarta yayi tana cewa
"Ka jefi uwarka Fatima amma ba ni Kulu ba"
Har ya tsaya zai bata amsa ya kuma yi ficewarsa ya barta tana ta masifa ita kad'ai.

A can gida kuwa Sumayya da taji yunwa na neman illata, ta sai ta kira Ishaq Direba ta aike sa yayo mata takeaway, tana zaune tana ci ya turo k'ofa ya shigo, dube-dube yake ganin bata falon ne yasa ya nufi d'akinta nan ma bata nan, kallon Sumayya yayi tare da cewa
"Har yanzun Wai bata dawo ba?"
Ta'be baki tayi tare da cewa
"Dama ka daina wahalar da kanka akan nemanta."
Wani banzan kallo ya mata
"Akan me kika ce haka?"
Gani nayi akan me kake wahalar da kanka bayan ta fita bata sanar da kai ba, ka fita harkarta kawai
"Karki sake mani magana makamancin wannan, ke idan zaki fita sanar dani kike yi? ba gara ma ita da ke ba, nasan dai ba zata ta'ba fita gidan nan ba tare da izini na ba, sai dai idan wani abu daban ne, ke tunda na aure ki dai-dai da rana d'aya baki ta'ba bin magana ta ba, ko kibi abunda nake so bakiyi, kina mani biyayya a matsayi na na mijinki wanda mukayi auren soyayya da ita, ita Inteesar ba auren soyayya muka yi ba, hasali ma na tsane ta bana son ganinta, koda aka aura mani ita haka na dinga wahalar da ita da bautar da ita da ayyukan wahala, bana barin ta huta haka zan dinga wahalar da ita ba tausayawa, hakanayyukan da ba sai tayi ba haka zan saka ta yi bana bari ta huta, amma duk da haka tana kallo na a matsayin mijinta bata ta'ba nuna mani 'bacin ranta ba, kwanakin baya Mahaifiyar k'awarta ta rasu Mufida ta biyo mata su tafi, haka tasa Gwaggo ta Kira waya ta har na bada izini sannan ta tafi, shekaranjiya na same ki d'aki kina shirin zuwa oarty, na nuna maki kada ki tafi, ina da buk'atarki haka kikayi fatali da buk'ata na mijinki kika fita ba tare da izinin mijiki ba, ina cikin halin buk'atar mace kika tadi kika barni, Allah da ikonsa sai ya turo mani ita a dai-dai lokacin da ya dace, gashi bata cikin kwanciyar hankali kuma ga mahaifiyarta kwance ba lafiya, a haka na nuna mata buk'ata ta kuma ba gardama ta amince mani saboda tasan girman hakkin mijinta kan wuyanta tasan laifin bijirwa miji masifa ce, amma ke baki San hakan ba, matar da akan rashin lafiyar Umma bata tafi ba sai da ta nemi izini na sannan ta tafi, wani uzurin kuma zaisa ta fita ba izini na."
Kallon mamaki take masa har ya gama maganarsa, sannan ta ce
"Kana nufin ta ta fini kenan ?"
"Kee Sumayya wallahi ki kiyaye ni, a halin yanzun raina a 'bace yake kada ki tunzura ni, dan idan kika tunzura ni zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dadi ba, Dan haka ki kiyaye ni kafin yanzun nan Kisha mamaki, dan zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dad'i ba, karki manta da wannan."
Daga nan ya fice ya barta zuciyarta na tafarfasa, tana mamakin wai yau ita Muhdeen ke fad'awa haka.

Mummy na zaune a d'akinta tana tunanin halin da Inteesar ke ciki, wayarta ce ta fara ringing ganin Mufida ce tasa ta d'aga ta rawar jiki kafin tayi magana Mufida ta ce,
"Mummy Albishirinki."
Murmushin farin ciki tayi ta ce
"Goro ta farfad'o ne?"
Mufida ta kalli Inteesar dake zaune ta jinjina bayanta da filo ta ce,
"Eh Mummy gata nan zaune wallahi na tambaye ta me ya same ta muka same ta kwance cikin jini da kwalabe, tayi mani shiru bata bani amsa ba, amma idan kika zo kila tayi maki magana, duk maganar da nake mata bata ce komai ba kallona kwai take kamar wata kurma."
Shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace,
"Ina Doctor take?"
"Yana office nasa"
"Yasan ta farfad'o?"
"A'a bai sani ba."
"To kiyi sauri ki sanar dashi yanzun nan, nima gani nan zuwa."
Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita.
*Daga alk'alamin*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love you oll
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*SADAUKARWA*
Wannnan shafin naki ne Faty mannir ina jin dad'in comment naki, don haka na sadaukar da wannan shafin a gare ki naki ne, kiyi yadda kike so da shi, sauran members na INTEESAR ma ina godiya da da comments had'i da add'ar da kuke mani Allah yabar k'auna.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6
Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita.

Kici'bis suka yi da Dady wanda shigowarsa kenan daga waje, ganin yadda take sauri yasa ya ce,
"Ina kuma zuwa haka?"
Shiru tayi tana nazari kafin ta ce
"Asibiti"
"Waye kuma baida lafiya"
Jim tayi kafin ta ce,
"Inteesar"
A kid'eme ya kalle tare da cewa
"Subhanallahi me ya same ta?"
A juyar zuciya ta sauke
"Alhji dogon labari ne ba lokaci muje kawai."
Kallon k'ofar d'akin Gwaggo yayi tare da cewa
"Ina Gwaggo"
"Tana d'akinta barci take"
Fita sukayi inda ta umarci Direbanta ya kaisu asibitin da Inteesar take, shiga sukayi bayan motar aka jasu zuwa Asibiti.

Zaune take akan gadon marasa lafiya kanta an nad'e shi da bandeji,Mufida na zaune a gefenta Doctor yana tambayarta yadda take ji ko akwai abunda ke damunta, kai kawai ta girgiza alamar ba komai.
Chapter 70 · 0% Book details