← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 99

Sashe 42

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdulillah"
Dubansa ya maida zuwa ga Mummynsa
"Mummy ina wuni?"
Lafiya lau son kuna lafiya?"
"Lafi..."
Kafin ya gama fad'in lafiya lau Gwaggo ta fara magana
"Ba wani lafiya da kake k'ok'arin cewa,lafiyarce za'a da'auki 'yar mutane a baka da d'an kumarinta a cikin kwanaki takwas naga yarinya ta rame sannan ka ce wa mutane lafiya?to gara ma ka fad'i gaskiya don banga alamar 'yar nan tana cikin kwanciyar hankali ba, Muhammadu kalleni in kalleka nan ba k'aramar yarinya ba ce ni da zaka raina mani hankali nasan k'ugin ciki nasan na gwaiwa wallahi duk wanda yasan 'yar albarka a baya ya kalleta yanzun yasan ba farin ciki da walwala a tare da ita."
Dubanta ta maida kan Dady da Mummy ta ce masu
"Kuma da yake ba tsoron Allah kuke ba bakusan laifin d'anku,har zaku kalli Inteesar ya ce maku suna lafiya ku yarda?"
Girgiza kai Dady ya yi Dan ya Saba da halin mahaifiyarsa,inda Gwaggo ta cigaba da cewa
"Da na ce sai nan da sati d'aya zanzi gidan naku nayi wata d'aya amma yanzun na fasa,jibi zanzo gidan naku dan hankalina ya tashi daga ganinta kasan bata cikin kwanciyar hankali,Amma kuka yi shiru tunda ba 'yarku Asiya bace."
Muhdeen ya tanka Mata
"Wai ke wannan tsohuwar me ke damunki ne haba mana,kince Bata cikin kwanciyar haankali to ki tambayeta idan ina mata wani abun da bata so."
"Me kake ci na baka na zuba? ai ba sai ka fad'a mani ba,da kaina zan tambayeta nasan halin da kuke ciki."
Janye hannun Inteesar ta yi tare da cewa
" kinga tashi mu tafi d'aki kinji 'yar albarka."
'Daga Kai Inteesar ta yi ta kalli Muhdeen ya yinda shi kuma yi mata wani kallo Mai cike da gargad'i karaf kuwa a idanun Gwaggo.

"La'ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi salallahu alaihi wasallam kallon uwar me kake mata haka?wato kada ta fad'a ki?to kada ka damu sai nayi maganinka wallahi da mi kake zancen."
Daga Nan ta ja hannun Inteesar suka shiga d'aki don ta k'udurata niyyar sak ta gano tsakanins,dafe goshi Muhdeen ya yi yana ta addu'ar Allah yasa Inteesar kada ta fad'awa Gwaggo komai,muryar Mummy ce ta dawo dashi tunanin da yake.

"Son maganar Gwaggo fa gaskiya ne nima na gani kuma nasan ba auren aoyayya kuka yi ba,kana can kana k'untawa 'yar mutane da ba ruwanta fa."
Dady ya d'ora da cewa
Muhammad Inteesar amanace awuri ka indan kaci amama amana zata cika.
*LONDON*
Kwance ta ke tana kallon Pics d'in Muhdeen tana kuka,ita kad'ai take magana
"Baby me yasa kayi Mani haka?me yasa aka aura maka wannan tsinanniyar yarinyar ne mun tsaka da cin amarci?kasan irin son da nake bazan iya had'a soyyayar ka da wata 'ya mace ba."
K'arar shigowar sak'one ya shigo tana dubawa ta ga Shila ce bud'ewa yayi taga Muhdeen da Inteesar a gaban motarsa a bakin super market,wani gigitaccen k'ara ta saki Wanda ya ja hankalin Mum nata da Da wayar take kallo tabbas shine tare da Inteesar sun ci ado ya d'aukota a motarsa,jifa ta yi da wayar ta bugata da bango dai-dai lokacin da iyayen nata suka shigo d'akin,numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
DON K'ARIN BAYANI
09065327995
Love u oll
Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page4
Numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa,Mum d'inta ce ta saki kuka tana fad'in
"Shikenan mun shiga uku 'yar da muke da ita k'wara d'aya ce muke neman rasa ta akan d'a namiji."
"Kinga ba kuma Zaki zauna kinayi mana ba,ki kawo mani ruwa."
Fridge d'in da ke cikin d'akin ta nufa ta d'auko robar ruwa ta 'balle murfin ta mik'a masa ya kar'ba ya watsa mata a fuska sau biyu,sai ga ta ta farfad'o da ajiyar zuciya tana cewa.

"Wallahi bazai yuwu ba Ni Muhdeen zai ci amana ta Ina nan ina tunanin yarinyar nan ba sonta ya ke ba ashe yana can tare da ita ya manta dani ko?"
Ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da cewa
"Kada ki damu da kansa zaizo har nan da kansa ya same ki."
Cikin muryar kuka ta fara magana
"Dad wallahi yanzun aka turo Mani pic d'insa ya tafi shopping da wannan matsiyaciyar yarinyar Inteesar,Dad ban ta'ba kisan Kai ba amma Inteesar d'innan matuk'ar tana raye bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba,I will kill her matuk'ar ban kashe ta...

"Shut up kinyi hauka ne ko kuma kishi hauka ne? kada na sake jin wannan maganar ko makamancinta a bakinki,dole ne sai kinyi rayuwa da Muhdeen?

Cikin d'aga murya ta maida ma Dad d'inta da martani
"Yas dole ne!na ce maka dole sai nayi rayiwa da Muhdeen shine mahad'in rayuwa ta bazan ta'ba iya rayuwa babu shi ba da na rasa shi gara a ce na rasa komai a duniyarnan Dad Kai da kanka kayi mani alk'awarin duk abunda nake so a duniyar nan zaka yi mani shi, kuma nima shira ne tunda na tashi naga duk abunda nake so shi kake mani ban ta'ba neman abu na rasa ba duk abunda nake so shi kake so kuma shi kake mani,amma karon farko a rayuwa ta na samu abunda nake son amma yana barazanar su'buce mani."
Mum d'inta ce ta yi ajiyar zuciya sannan ta fara magana
"Tunda haka abun ya kasance da kake cewa ya za'bi d'aya ko'yarka ko wacce suka aura masa kasan dai yana wa iyayensa biyayya bazai ta'ba tsallake maganar iyayensa ya bi na wasu ba kaima kasan da hakan kuma kaji maganganun da kakarsa ta fad'a maka lokacin da ka kira mahaifinsa kake masa magana,indai zaka bi shawara ta tunda basu suka kori Sumayya ba kuma mijinta bai sake ta ba kuma bai wulak'anta ta ba da k'afarta ta bar gidan ta taho nan,to idan zaka bi magana ta ta koma d'akin mijinta tunda ba zata iya rabuwa da shi ba."
"Mum ke da kanki kike fad'in na koma da kaina na zubar da aji na a idonsa da danginsa?da wannan yarinyar da ya aura?."
Fashewa da kuka ta yi fad'aj ikin Dad d'inta tana cewa
"Wallahi Mum ba inda zan koma wato ma na fahimci baki so na baki k'auna ta baki kishi na,tunda har kike son na zauna da kishiya ke me yasa kike zaune ke kad'ai Dad bai k'ara aure ba?ai da Dad ya k'ara aure kika San zafin kishi ba Zaki ce na koma na zauna da kishiya ba."
Da mamaki Mum d'inta ke kallonta
"Sumayya ni kike fad'awa haka?"
Tura baki ta yi tare da cewa
"Ai gaskiya na fad'a kinsan zafin kishin ne?"
Mummy ta yi kanta da niyyar marinta Dad ya daka mata tsawa
"Ke dakata!"
Sumayya k'ara shiga jikin Dad ta yi don ta tsorata da 'bacin ran da ta gani a fuskar Mun nata.

"Kada ki kuskura ki ta'ba mai ita don wallahi kika mareta sai kinyi mamakin abunda zaki maki,k'arya ta fad'a ba gaskiya bane?sabida ance gaskiya d'aci ne da ita,da wanne zata ji da 'bacin ran mijinta ko da naki?kinzo Zaki saka yarinya gaba kamar ba kece kika haifeta ba,ke kanki kin sani bani k'aunar ki 'batawa yarinyar nan rai tun tana k'arama ballantana yanzun da tasan me yakamata tasan dai-dai da akasin haka,da ki ta'bata gwanda ki ta'ba ni,idan kuma kina musu da haka ne to ki ta'bata kisha mamaki."
Mum bata sake cewa komai ba girgiza kai kawai ta yi ta fice ta bar masu d'akin.

A nan k'asa ta kuwa bayan Gwaggo ta ja Inteesar sun shiga d'aki ta zuba mata ido bayan sun zauna ta kalleta ta ce,
"'Yar albarka ki fad'a mani gaskiya ya yanayin zamanki da Muhammadu ya ke?"
Shiru Inteesar ta yi tana nazari kafin ta ce,
"Ba komai Gwaggo muna zaune lafiya"
Kai Gwaggo ta girgiza tare da cewa
"Ba lafiya ba 'yar albarka akwai abunda kike 'boyewa,kina nufin baya cutarki baya zalintarki yana kyautata maki duk wani hakkinki baya tauyewa?"
Shiru Inteesar ta yi ba tare da ta ce komaiba,hakan yasa Gwaggo cewa
"Kiyi mani magana mana abunda yasa kika ji na ce ki fad'a mani ya zamantakewarku ta ke shine kinsan ba auren soyayya kuka yi ba,auren had'i ne kuma bawai yana sonki bane kada ya je ya dinga k'untata maki ba.

"Shiru Inteesar ta yi tana tunanin zamanta da shi Sam baya mata adalci burinshi kawai ya ganta tana wahal,amma Bata son ta zama sanasiyar 'batawansa da iyayensa don matuk'ar ta ce zata sanar da Gwaggo to tabbas zata sanar da su Mummy da Dady kuma zasuyi fushi da shi, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru ta k'udiri niyyar hak'uri da juriyar zama da shi,dan haka kallon Gwaggo ta yi tare da cewa
"Kada kisa tunananin komai a ranki muna zaune lafiya ba abunda kike tunani bane."
"Shine duk kika rame kika lalace?ba komai tunda kink'i fad'a,koma dai mene ne zan gano Allah ya kaimu jibi zanzo na gaishe ku,tashi to muje."
Mik'ewa Inteesar ta yi inda suka nufi falo,zaune suka tarar da su kamar yadda suka barsu, Mummy ce ta zubawa Inteesar ido tana karantar yanayinta,adai zaman da sukayi tare da Inteesar barci ke raba Inteesar da gidanta a tsawon shekaru uku zuwa hud'u kenan amma tabbasa yanayin Inteesar ya canza da ganinta kasan akwai abunda ke damunta.
Chapter 42 · 0% Book details