Sashe 22
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana cikin tunani taga ya d'auki wata hanya daban ,gani yayi yanayinta ya canza alamar Bata yarda dashi ba.Hakan yasa ya Ciro wayarsa bayan yayi parking a gefen titi.Lambar wayar Mummy ya lalubo ya danna mata kira, lolacin Mummy na zaune a d'akinta ita Mahifiyar Jabeer,kiran Jabeer ne ya shigo wayarta kallon Mahifiyar Jabeer d'in tayi ta ce,
"Kinga Jabeer ne ke kira na kodai ya kira lambarki ne bai shiga ba?"
'Daga wayar tayi tare da cewa,
"Hello Jabeer kun iso gida ne?"
Jabir ya Bata amsa da cewa
"A'a Mummy dama lokacin da zamu tafi reception ne naga su Mufida da tagwayen Aunty Maryam, so motar da zasu shiga bai d'aukesu ba hakan yasa nace
wa Inteesar da bata samu wuri a motar ba ta shigo motata.Tunda ango da Amarya zan d'auka kad'a,to yanzun Angon ma a motarsa ya koma sai ni da Inteesar d'in mun kama hanyar dawowa Maryam ta kirani Wai tana son agwaluma,nacewa Inteesar bari na siye na Kai mata tunda munfi kusa da gidana,naga hankalinta bai kwanta ba tana tsoron na cutar da ita ne gashi yanzun magariba tayi ko zakiyi mata magana ko hankainta zai kwanta."
Murmushi Mummy tayi tare da cewa,
"Bata wayar"
Mi'kewa Inteesar wayar yayi tare da sakar Mata Murmushi,amsar wayar tayi ta Kara a kunnenta ta ce,
"Assalamu Alaikum."
Jin muryar Mummy yasa ta sakin murmushi tana cewa
"Ina wuni Mummy?"
"Lafiya lau Inteesar ki kwantar da hankainki Jabeer kamar yaya ne a wajenki,bari ya siye abunda zai siya idan yakai mata sai ku dawo gida kinji?.Abunda yasa baki sanshi ba lokacin da yake zuwa lokacin ki tafi gida shiyasa baki sanshi ba,ki kwantar da hankalinki Jabeer ba mutumin kirki ne.Allahnya kawoku lafiya."
"Ameen"
Inteesar ta amsa tare da kashe Kiran,Mik'awa Jabeer wayar tayi taga ya shagala da kallonta saurin kanye idanunta tayi ta sunkuyar da kanta k'asa.Ajiyar zuciya ya sauke tare da amsar wayar,key yayiwa motar suka d'auki hanya.Bayan yayi parking wajen me agwalumar ya juya ya kalli Inteesar ya ce,
"Kema zakisha agwalumar ne na siye maki."
Cikin sanyin Murya tayi magana
"A'a bana Sha."
Fita yayi yaje ya siyo ya dawo rik'e da leda cike da agwaluma,dan.
Inteesar tayi mamakin yawan agwalumar a zuciyarta tana mamakin yawan agwalumar da mutum d'aya zata sha.Bayan ya tada motar ne sun d'anyi tafiya kad'an sai yayi parking a wani k'ayataccen wajen siyar da abinci.ya kalleta ya ce,
"Bari na d'anyo mana takeaway sai mu k'arasa gida."Ba ta ce komaiba ya fita yaje ya dawo da ledoji biyu a hannunsa,d'aya takeaway ne guda uku d'aya ledar kuma kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe danginsu chocolate da snacks da ice cream da Biscuits ne a cikin.Yana shiga ya tada motar sai gidansa ya nufa,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga da motar,bayan yayi parking ne ya fito ya bud'e mata yayi don ta fito sai ta mak'e kafad'arta alamar bazata fito ba ya k'ura Mata yadda take tura d'an k'aramin bakinta ne ya bashi dariya ce mata yayi
"To shikenan tunda ba zaki fito ba Ni zan shiga ciki kinji ana Kiran sallar magariba ni zan shiga nayi alwala sai naje masallaci na dawo sannan zamu tafi gida.kinsan lokacin sallar magariba gajeren lokaci ne dashi gara ma ki fito.Jin hakan yasa ta fito ,bayan motar ya bud'e ya d'auko ledojin yayi gaba tabi bayansa.
A falo sula tarar da Maryam kwance kan doguwar, kujera tayi rigingine ta d'aura hannunta akan cikinta.Jin muryarsa yasa ta mi'kewa zaune don dama agwalumar take jira tasha.
Jin sallamar muryar mace yasa ta d'aga kai ta kalli Inteesar,gabanta ne ya fad'i saboda yanzun ta sauka a online kuma tagani a status Mufida ta d'ora videon reception d'in da sukayi taga inda Jabeer ya fito daga gaban motarsa ya zagayo ya bud'ewa Inteesar ta fito daga gaban motar sa yana kallonta yana murmushi.Tare suka shiga wurin tana gaba yana binta a baya.Har tayiwa Mufida reply da cewa wace ce nan tare da miji na?Mufida bata amsa Mata ba don ta sauka online.Zaubawa Inteesar ido tayi tana tunanin meye tsakaninta da mijinta da tun d'azu suke tare har yanzun ya kawo Mata ita cikin gida.
Murmushin yak'e tayi tare da cewa,
" sannun ku da zuwa"
Inteesar ce ta gaishe ta,ta amsa mata fusaka a sake ba yabo ba fallasa.Jabeer ya ajiye lesojin ka center carpet dake tsakiyar falon,ya kalli Maryam ya ce,
"Madam ya jikinki?"
Murmushi tayi tare da cewa
"Da sau'ki."
Ledar agwalumar ya d'auka ya ce,
"Bari naje na wanko maki su kafin ki Fara shansu hakanan."
Kichen ya nufa da agwalumar don wankewa, Maryam ta kalli Inteesar ta ce,
"Zauna mana baiwar Allah kinyi tsaye."
Inteesar tayi murmushi ta zauna Kan kujerar dake kallon Maryam,zauba Mata ido Maryam tayi tana kallon tsantsar kyawu irin na Inteesar kamar wata balarabiya,sai taji wani abu ya d'arsu a zuciyarta ta kasa gane kishi take da Inteesar ko meye?gashi dai yarinyar ta burgeta amma meye had'inta da mijinta?ta sake duba wayarta taga yanda Jabeer ya fito motarsa ya zagayo ya bud'ewa Inteesar sai kallonta yake Yana sakin murmushi.Jin ya dawo ne yasa ta ajiye wayar ta fara shan agwalumar.kallon Inteesar yayi yace bari nayi sallah sai na maidake gida ko?"
Ya maida dubansa ga Maryam ya ce
" ta shiga ciki tayi sallah ga takeaway nan idan ta idar da sallah taci abinci zan maidata gida."
Daga Nan ya fice Maryam ta zubawa Inteesar ido kafin ta mi'ke dakyar tana yamutse fuska ta ce,
"Zo mu shiga ciki."
Ba musu Inteesar tabi bayanta har bedroom d'inta ta nuna Mata k'ofar toilet ta shiga ta d'auro alwala,Koda ta fito Maryam ta shimfid'a Mata sallaya ta aje mata hijab.Bayan ta Fara sallah sannan Maryam ta shiga ta d'auro alwala tana tafiya tana d'an dafa bango don jiri takeji.
Bayan sun idar da sallah,Maryam tace da Inteesar taje taci abinci kafin ya dawo,tace ita ba zataci abinci ba ta k'oshi.Shiru-shiru Jabeer bai dawo ba Inteesar ta kagara sai da har aka Kira sallar isha'i suka idar sannan ya dawo.A falo ya tarar dasu ganin yadda yadda ajiye ledar takeaway haka ya same shi ya ce,
"Me yasa bakici komai ba?"
Mik'ewa tayi tare da d'aukar posan ta ta ce,
"Na k'oshi,ka kaini gida kawai."
Yadda tayi maganar ne ya burgeshi ya zuba Mata ido yana murmushi,Maryam ta lura da hakan sai tayi gyaran muryar da yasa ya kauda idonsa akan Inteesar ya maida kan Maryam.alama ya mata Wai meye?Kai ta girgiza ta kauda kanta gefe,hakan yasa yacewa Inteesar ta zo su tafi.Sallama tayiwa Maryam suka fice.
Akan hanyarsu yayi parking dai-dai wani super market.kallonsa tayi ya kauda Kai tare da fita don kar ma ta tambaye shi,bud'e mata yayi tare da cewa
"Fito"
Kallon mamaki tayi masa tare da cewa
" me zamuyi anan kuma?"
"Turare zan siya"
Ya Bata amsa a ta'kaice,ta koma jefa masa wata tambayar ta ce,
"To ka maidani gida idan ka dawo ka siya,ko kuma kaje ka siya Ina jiranka a mota."
Kallonta yayi yana cewa
"Idan baki fito kin rakani ba bazamu bar nan wajen ba ko zamu kwana ne kuwa."
Jin hakan yasa ta fito suka jera dab da zasu shiga taji an Kira sunanta,gabanta ne ya fad'i jin muryar Wanda ya kirata.Juyawa tayi da sauri ganinsa tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu ya zuba Mata ido.
*DON K'ARIN BAYANI*
09065327995Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba.Idan suna ko hali yazo d'aya,to you gafarceni bada niyyar yin gakan nayi ba arashi mai kashe auran Wawa.
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guii sarrafa mani shi ta kowace siga.
Page 2
Juyawa tayi da sauri ganinsa tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu ya zuba mata ido.
A hankali ta furta sunansa
"Usman"
Murmushi ya sakar mata tare da yi Mata alama da tazo,kallon Jabeer tayi taga ita yake kallo ita da Usman.Cikin sanyin Murya ta ce,
"Yaya Jabeer don Allah ina d'an zuwa 2 minutes."
Kai kawai ya d'aga ba tare da yace Mata komai ba,take kuma fara'ar dake d'auke a fuskarsa suka gushe.Dai-dai lokacin ne wayar Jabeer ya soma ruri,ganin sunan Mummy ce ya saka shi sakin murmushi ya d'aga kiran.Jin muryar Mummy na cewa Ina suk tsaya da basu dawo ba haryanzun?
Inteesar kuwa har ta kusan k'arasawa kusa da Usman Jabeer ya kira Sunanta,juyowa tayi ta kalleshi.Cikin bada Umarni yace ta dawo,ganin fuskasa ba wasa yasa ta juya ta koma wajensa,tana k'arasawa ya ce,
"Mummy ta kira waya, ki wuce mu tafi."
Kai tsaye inda yayi parking ya nufa tana biye dashi, bud'e mata yayi ta shiga sannan Shima ya zagaya ya shige.Sauke glass d'in motar yayi tare da kallon Usman yaga idanunsa nakan su,jan motar yayi suka bar wajen super market d'inda basu shiga ba kenan.Usman bin motar yayi da kallo har ta 'bacewa ganinsa,a ransa yana jin babu dad'i, zuciyarsa cike da tarin tambayoyi,shin waye wannan dake tare da Inteesar?
Ita da lokacin da ya ce zaizo gidansu ta hanashi ta ce wai ba'a barinta ta tsaya da saurayi,sai da yayi Mata dabarar cewa maganinta ne doctor ya ce a bata sannan ta yarda ta bari yazo gidansu.
Kuma iya saninsa bata da wani yaya ita kad'aice a wajen iyayenta ballantana ace shi yayanta ne, yarinyar da Bata tsayawa da saurayi me zaisa a irin wannan lokacin wani saurayi ya kawota shopping?.Haka ya dinga yiwa kansa tarin tambayoyi sanin bashida mai bashi amsane yasa jin zuciyarsa jin ba dad'i musamman idan ya tuna cewa Inteesar zata k'araso wajensa kenan wannan saurayin ya kirata dan kada tayi magana da shi.Ita kuma sai ta biye masa ta tafi ta barshi,Take ransa ya kuma 'baci haka yaja motarsa ya bar wajen,dama ya gama abunda zaiyi yana shirin tafiya ne yaga Inteesar ta fito daga Motar Jabeer.