← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 99

Sashe 36

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba laifi kuwa gidan ya cika da jama'a musamman 'yan unguwar, an girka abinci kala-kala kowa yaci abunda ransa keso ga soyayyun naman kaji da na sa da aka yanka,'yan matan unguwar ma duk Mufida ta gayyace su, koda aka shigo da Inteesar kai tsaye d'akin Mufida ta nufa don dama duka k'awayensu da wad'anda suka gayyata suna nan cikin d'akin, nan dai suka nuna farin ciki da fatan zaman lafiya mai d'orewa, k'arfe hud'u akayi walima inda aka gayyaci manyan malamai suka zo suka yi wa'azi da jan hankali akan zamantakewa aure da ha
in miji akan matarsa da ha
in mata akan mikinta, da misalin k'arfe shida na yamma aka tashi walimar inda akayi rabon sallaya da hijabai.

Da misalin k'arfe takwas na dare aka d'auki Inteesar aka Fara kaita gidan mijinta, nan aka dinga yaba had'uwar gidan da kuma had'uwar dakinta, dangin Umma ba k'aramin farin ciki suka yi ba ganin yadda iyayen Muhdeen suka narkar da naira wajen yiwa Inteesar kayan d'aki Mama Huraira ma k'anwar Umma taji dad'in ganin yadda gidan 'yar 'yar uwarta, ba yadda Inteesar bata yi da Mufida akan su ta kwana amma sam Mufida ta ce a'a amma zata zo gobe, lokacin da taga jama'a na tafiya kuka sosai tayi dakyar Aunty Abla da Mama Huraira suka lalla'bata ta hak'ura suka tafi.

Gida ya rage ita kad'ai ce a ciki zama tayi tare da tagumi tana tunanin wace irin rayuwa zata yi waye mijinta hawaye ne kawai ke zuba a kan fuskarta kamar an bud'e famfo.

Bangaren Muhdeen kuwa yana zaune a office d'insa kan sofa yayin da idanunsa a lumshe kamar mai barci amma ba barcin yake ba, Jabeer ne ta turo k'ofar ya shigo har lokacin bai bud'e idanunsa ba, Jabeer sallama yayi masa.

"Assalamu Alaikum"
Can k'asan mak'oshi ya amsa, la'b'bansa ne kad'ai zaka kalla ka gane yayi magana.

"Ya kamata ka tashi ka tafi wajen amaryarka k'arfe goma yanzun, tunda ka ce baka buk'atar rakiyar mu ai sai ka tafi Allah ya bada zaman lafiya."
Banza da shi Muhdeen yayi kamar baiji shi ba, dama baisa ran zai amsa masa ba don yasan halinsa, amma duk da haka bai damu ba sake magana yayi yana cewa
"Kasan wallahi idan har baka tashi ka tafi wajen Amaryarka ba sai na kira Dady yanzun nan a waya na fad'a masa cewar kana nan asibiti zaka kwana ba zaka koma gida ba saboda baka son auren da suka yi maka."
Still shiru yayi kamar baiji me ya ke fad'a ba tsawon mintuna biyar bai ce komaiba ran Jabeer ne ya 'baci yana da niyyar yin magana ne wayarsa ta soma ringing dubawa yayi matarsa Maryam ce, dama tana gidansu Mummy wajen taron bikin ganin karfe 10 bai zo ya d'auketa sun tafi gida ba ne yasa ta kiranshi,
aga wayar yayi tare da cewa.

"Hello My dear kinji ni shiru ki?"
Jin muryarta yayi kamar zatayi kuka tana cewa
"Dan Allah ka zo mu tafi gida na gaji ina son na huta pls"
Dariya yayi yana cewa
"Karki damu ganinan zuwa nazo na d'auke ki idan muka tafi gida zan gasa maki jikinki da ruwan d'umi nayi maki tausa zaki ji dad'in barci."
Dariya tayi tare da katse kiran, dubansa ya maida kan Muhdeen ganin baima da niyyar tashi sai ma kishingid'a da yayi ne yasa Jabeer duba wayansa yana lalubar number Dady bugu d'aya a na biyu Dady ya d'aga wayar inda Jabeer yasa speaker na wayar Muhdeen najin Muryar Dady na cewa
"Hello Jabeer ya akayi ne"?

Kafin Jabeer yayi magana cikin zafin nama Muhdeen ya fisge wayar tare da katse kiran, wayoyinsa ya d'auka ya saka a aljihu ya nufi hanyar fita Jabeer yabi bayansa yana k'yalk'yata dariyar mugunta.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi.

K.N.T
Maman Ihsan
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
Page3
Kafin Jabeer ya yi magana cikin zafin nama Muhdeen ya fisge wayar tare da katse kiran, wayoyinsa ya d'auka ya saka a aljihu ya nufi hanyar fita Jabeer ya bi bayansa yana k'yalk'yata dariyar mugunta.saida suka je inda za su rabu ne Muhdeen ya mik'a masa wayarsa kowanne ya shiga motar sa ya kama hanyar fita asibitin.

Jabir gidansu Mummy ya nufa yayin da shi kuma Muhdeen ya nufi gidansa.

Inteesar kuwa tana can d'akinta, k'udunduna saman gado ta had'a Kai da guiwa sai kuka take yi har da sheshshek'a,tana tuna Ummanta da Abbanta.

Horn yayi mai gadin gidan ya lek'a ta k'aramar k'ofa,ganin Mai gidan ne yasa shi saurin wangale gate d'in gidan,cinno hancin motar yayi cikin gidan a parking space yayi parking,ya fito yakai tsawon mintuna goma yana zaune a cikin motar kafin ya fito ya nufi cikin gidan.

Duk da cewa part biyu ne gidan amma bawai suna rabe da juna bane,kusan a had'e suke kuma k'ofa d'aya suke da ita dole sai mutum ya bi ta falon Inteesar kafin ka shiga falon Sumayya,kuma ko wane bedroom guda hud'u suke da dasu,kuma kowane bedroom da toilet d'insa a ciki akwai kuma kitchen da dinning area kowanen su.

Turo k'ofar yayi k'amshin turare ne suka tarbe sa,wanda bai ta'ba jinsa ba a gidan,kai ya saka da nufin wucewa part d'in Sumayya sai ya jiyo sheshshek'ar kukan Inteesar,kamar ya wuce sai ya nufi d'akin Inteesar d'in,tura k'ofar d'akin yayi ganinta zaune yayi ta k'udundune ta had'a Kai da gwuiwa sai kuka take kamar ranta zai fita.Bata San ya shigo d'akin ba kukanta kawai take yi kamar ranta zai fita.

"Kukan uwar me kikewa mutane?"
Muryar da taji ya dakai dodon kunnenta ne yasa taji gabanta ya fad'i rass don idan har ba mafarki take ba wannan muryarsa ce don ba zata ta'ba mancewa da wannan muryar ba,azuciyarta take magana
"Kenan wannan mugun mutumin shine mijina?

Kai ina bazai yiwu ba,bashi bane."
'Dago kumburarrun idanunta da tayi ne yasa ta d'aura su akansa ne yasa gabanta yayi mummunar fad'uwa ,tabbasa shine.

"Kallon me kike mani ne?kin zuba Mani ido kamar mayya,ba ke kika ce kina sona ba?"
Kai ta girgiza alamun a'a idanunta na zubar da hawaye ta fara magana.

"A'a ni wallahi bani bace nace ina sonka."
"To kika yarda kika aure ni?kuma amincewa da aure na da kikayi shine kuskure mafi muni da kika tabka a rayuwarki,dan sai kin gwammace dama baki aure ni ba,tukunna wai me yasa baki bijirewa auren ba kika amince duk da kin San ba k'aunarki nake ba?"
Share hawayen fuskarta tayi tare da cewa
Ban san Kai ne mijin da aka aura mani ba sai yanzun,kuma Koda na sani bazan ta'ba bijirewa zancen iyaye na ba,domin duk wanda yake son rayuwarsa tayi albarka bazai ta'ba bijirewa zancen iyayensa ba,neman albarkar iyaye da biyyaya a gare su yasa ban bijirewa zancen auren ba."
"Ko da hakan yana nufin bak'in cikinki ne?"
"Koda hakan yana nufin mutuwa ta ce,bazan ta'ba bijirewa zancen iyaye na na ba."
"Good"
Daga nan yasa Kai ya fice,ita kuma kukanta ta cigaba da yi don bata ta'ba tinanin cewa Muhdeen aka aura mata ba,haka ta cigaba da kukanta a k'udundune har barcin wahala yayi awon gaba da ita.

Shi kuma yana fita d'akinsa da ke cikin falon Sumayya ya nufa kayan jikinsa ya rage ya fad'a toilet Dan yin wanka,
K'arfe uku na dare Inteesar ta farka daga barcin wahala da tayi, toilet ta fad'a tayi wanka da ruwa mai d'umi sannan ta d'auro alwala ta fito man shafawan Hajiya Bilkisu Mai k'amshi ta shafa doguwar riga ta atamfa ta saka ta sanya hijab don yin sallah,nafila raka'a biyu tayi sannan ta fara karatun alqur'ani mai girma,tana zaune har har lokacin sallah ta tashi tayi sallar asuba,bayan ta idar ne ta dinga yin azkar har sai da gari ya waye tayi addu'a sosai akan zaman auren nan tare da rok'on Allah ya k'ara mara hak'urin zama da Muhdeen.

Tashi tayi ta fito daga d'akinta don tsananin yaunwa ke damunta rabon da ta ci abinci tun karin da tayi jiya da safe,da rana bata ci komai ba haka ma dare yayi ba abunda ta saka a cikinta,ba yadda Mufida bata yi da ita ba amma sam tak'i cin abinci dole ta ha'ura ta kyaleta.

Fitowarta falon yayi dai-dai da isowar mai aikin gidan,wato kande wacce take zuwa ki wace safiya tayi share-share da goge-goge,yau tayi sammakon zuwa ne saboda ranar da aka sanar da ita zancen aikin an fad'a mata cewa matar gidan zata dingayiwa aiki da bata ga matar gidan ba sai ta tambayi Ishaq ya sanar da ita cewa tayi tafiya ne,to sai jiya da taji labarin matar gidan zata dawo yasa ta sammakon zuwa,dattijuwa ce mai kimanin shekaru arba'in.

Ganin Inteesar ya sa ta durk'usa da niyyar gaishe ta,kafin ta kai k'asa Inteesar tayi saurin d'ago da ita tana cewa.

"Haba Baaba ai bai kamata ace kin durk'usa mani ba,ni ce ya dace na durk'usa maki,ina kwana?"
Murmushi matar tayi tare da cewa
"Lafiya lau sannu Hajiya."
Inteesar shiru ta yi tana kallon matar ita dai bata santa ba kuma gashi ta daka sammako wajen zuwa gidan,tana cikin wannan tunanin taga matar ta durkusa tana gaida Muhdeen.

"Ina kwana alhaji"
Alamu yayi mata da hannu alamun ta tashi tsaye,ba tare da ya amsa gaisuwar da tayi masa ba, Mi'kewa ta yi.
Chapter 36 · 0% Book details