Sashe 25
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can gidan Mummy kuwa tunda su Inteesar suka idar da sallar asuba su Mufida da Azeeza suka koma suka cigaba da barcinsu, Inteesar kuwa azkar tayi sannan ta mik'e ta nufi kitchen don tasan akwai bak'i a gidan hakan yasa taje don had'a breakfast.Kasancewar tana da zafin nama wajen aiki a cikin k'ank'anin lokaci tayi rabin aikin,don Koda Aunty Maryam k'anwar Dady ta shigo k'araso kitchen d'in k'amshi kawai ke tashi kusan a tare Aunty Maryam ta shigo tare da Mummy.sunji dad'in ganin Inteesar a kitchen tana aiki cikin girmamawa Inteesar ta gaishesu,suma suka amsa mata cikin jindad'i.Lokaci d'aya Inteesar ta shiga ran Aunty Maryam.Had'a hannu sukayi su uku zuwa k'arfe takwas sun gama shirya breakfast kala-kala Inda aka jera wasu a dinning table sauran kuma aka kai d'akunan da Bak'i suka sauka inda Aunty Maryam ta jera wasu a basket tace akai gidan Muhdeen.Mummy ce ta kalli Inteesar ta ce,
"Ina Mufida ce tazo direba ya kaiku,gidan Amarya ku Kai masu breakfast."
Inteesar ta ce,
"Suna can suna barci bari naje na tayar da ita."
Fita tayi daga kitchen d'in Kai tsaye ta nufi da'akin Mufida.koda ta shiga duk suna barci tayar da Mufida tayi ta sanar da ita sak'on Mummy.Yamutse fuska sannan ta sanar da Inteesar cewa bari tayi wanka ta shirya.
"Har sai kinyi wanka?nima fa banyi wankan nan ba dogon Hijab kawai zan saka mu tafi."
"Ke da Zaki iya lullu'be jikinki da hijabi kenan ba Wanda yasan ya kayan jikinki ya ke ba,amma ni da ba hijab zan saka ba fa?haka zan fita a ganni da rigar barci ba."
Daga nan Inteesar ta fita ta sanar da Mummy cewa Mufida zatayi wanka ta shirya in da Mummy ta ce,
"Ba ta yi wanka ba dama?ita da take dad'ewa a bathroom ne zamu tsaya jira?"
Kallon Inteesar tayi tare da cewa,
"Daughter Kinga bari in sanar da Ishaq direba ya kaiki,don nasan har zaku je ku dawo bata gama wanka ba."
Gaban Inteesar ne ya fad'i jin cewa wai ita kad'aice zata je gidan wancan mugun da sassafen nan,domin ita a rayuwarta ba mutumin da ta tsani ganinsa sama da Muhdeen,gashi kuma ba zata iya yiwa Mummy gardama ba ki ta kawo Mata wani uzurin.Bata da za'bi dole haka ta kar'bi basket d'in breakfast hannun Aunty Maryam inda Mummy ta rakata har harabar gidan.Nan ta sanar da Ishaq cewa yakai Inteesar gidan Muhdeen idan ta shiga ya jirata har ta fito kafin su dawo.
Can cikin bacci yaji k'arar k'ofa,a zuciyarsa yace waye haka da sassafe?tashi yayi yabar Sumayya a kwance tana ta barci don ko k'arar k'ofar ita bataji ba.
Falo ya k'araso ya bud'e k'ofar,ganin Inteesar yasa ya murtuk'e fusak kamar Wanda Bai ta'ba dariya ba.Itama 'bangarenta haka ne don ba Wanda ta ysani haninsa a rayuwarta sama da Muhdeen.Cikin sanyin Muryarta ta ce,
"Ina kwana?"
Bai amsa ta ba sai cewa yayi
"Lapiya?"
Bata kula shi ba ta mi'ke masa basket d'in,baice komai ba kar'bi basket d'n tare da shigewa cikin falon ya barta nan tsaye.
Juyawa ta yi don k'arasawa wajen Ishaq koma gida.
******* ********
Har Muhdeen Sumayya suka cika sati d'aya da aure,Kullun sau uku Mummy zata Aiko masu da abinci safe da Rana da dare.Aranar ne kuma ta sanarwa muhdeen za'a daina kawo masu abici,sai dai matarsa ta cigaba da yi masu girki.
Bak'i kowa ya tafi gidan an watse daga Dady, Mummy,sai Mufeeda.Asiya dama tunda akayi biki ta koma Gwaggo ce kad'ai ba ta tafi ba.
: Bangaren ango da ameya kuwa suna shan soyayyarsu son ransu.Abunda ya tayarwa Sumayya hankali shine jin wai zata Fara girki,don ita a rayuwarta ba ta ta'ba shiga kitchen da sunan girki ba don ko ruwan zafi bata ta'ba d'orawa a wuta ba Babu abunda take a gidan iyayenta,komai 'yar aiki ke Mata ko kauda tsinke Bata iya ba.Nan dai ta nunawa Muhdeen cewar ya Nemo masu Mai aiki don ita ba zata iya aikin komai ba,nan ya nuna Mata cewar gsky bazai iya cin abinci wanda 'yar aiki ta girka ba,haka tsarinsu yake ko gidansu Mahaifiyarsa ce ke girka abinci,don haka bazai iya ba gsky.nan hankain Sumayya ya tashi don bata ma san ta Ina zata fara ba kuma Bata San yadda zatayi ba.nan take sanar da ita abokansa ma zasuzo gobe zasu zo suci girkin amarya.Nan dai ta cire d'an kwalin kanta tana goge zufa duk da sanyin A C daga ratsata
Daga Alk'alamin
Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)
09065317995
Love u oll
Comment &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,Idan suna ko hali yazo daya to gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page2
Nan take ya sanar da ita abokansa zasu zo gobe zasu zo su ci girkin amarya.Nan dai ta cire d'an kwalin kanta,tana goge zufa duk da sanyin A C dake ratsata.
"Me ya faru ko akwai wata matsala ce?"
Kai ta girgiza tana tunanin ta yadda zata fara,domin kuwa wannan Abu ne mai matuk'ar wahala a gare ta.Bata ta'ba tunananin wannan ranar zata zo ba.Ita da rayuwarta daga taci tasha ta kwanta ba abunda takeyi,Mai mata aiki ce take komai sai da ta tashi barci ta yi wanka tayi kwalliya ta fita Koda zata shigo d'akin sai sai ta tarar an kimtsa mata komai ko kitchen idan ta shiga sai dai idan akwai abunda taje d'auka,sau tari ma tana zaune zata bada umarnin a kawo mata duk abunda ranta keso gashi yanzun mijinta da tayi tunanin zai bi ra'ayinta amma ya ce wai bai yarda da 'yar aiki a gidansa ba.Kukar shagwa'ba ta saka ta ruga a guje ta nufi bedroom d'inta.Shima ya ta shi ya bita a guje kamar sharukhan
Koda ya shiga d'akin kwance ya sameta tayi kwanciyar rubda ciki,janyota yayi jikinsa ya rungume yana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi.Cikin kwantar da murya ya fara magana.
"Haba Baby kukan me kike yi?kinsan na tsani naga kina kuka hankalina tashi ya ke."
Cikin shagwa'ba ta
fara magana
"Haba ya zanyi wallahi bazan iya ba,sai kace jaka?nifa bana aiki a gidanmu kafi kowa sanin ma'aikata ke mana aiki ban iya ba kuma ban saba ba,sannan nayi aure bazan huta ba sai nazo na zama banida banbanci da 'yar aiki?"
Cikin sigar rarrashi ya fara magana
"Kinga ba wai ke zakiyi duka aikin gidan nan ba,girki ne dai bazan iya cin na 'yar aiki ba.kuma ai tunda kika zo gidannan bakiyi aikin komai ba,nine nake yin gyaran d'akunanmu na share na goge na wanke toilet na gyara kitchen,duk da Mummy ke aiko muna da abinci ko wace rana ni nake wanke kwanoni .Aikin komai ban baki ta'ba yi ba,kuma dama ranar Monday zan koma asibiti wajen aiki, kafin ranar zan nemo wacce wacce zata dinga yin aikin Amma iyakar ta dai ta yi wanke-wanke da ta gyara kitchen da falo da d'akinki Amma ban yarda 'yar aiki ta shigar mani d'aki ta gyara ba.Zanyi da kaina kuma ban yarda 'yar aiki ta shiga kitchen ta girka mani abincin da zanci ba sai dai matata,sannan akwai Wanda zai dinga wanki da goga fatan kin fahimta,girki kawai ne aikinki a gidan nan Zaki iya ko?"
Kai ta gyad'a masa alamar Eh.Daga nan salon ya canza aka lula duniyar ma'aurata.
Gidan Jabeer kuwa,Matarsa kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba.Tun ranar da taga ya shigo da Inteesar gidan kuma taga yadda taga Jabeer ya na ta rawar jiki da Inteesar a wurin reception d'in bikin Muhdeen,ta kuma tambayi Mufida wace taga tayi posting a status d'inta ta fito daga Motar Jabeer?sannan washe gari ranar dinner haka taga Jabeer ya d'aukota a motarsa sai wani kallo yake mata mai cike da shauk'i sannan cikin pic d'in ga bugu da k'ari taga photon da Mahaifiyar Jabeer d'in ta rungume Inteesar da su Azeema.Tayi ta sak'a da warwara musamman da ta tambayi Mufida cewar meye dangantaka su da Inteesar ta sanar da ita cewa ba dangantaka sai dai suna mata kallon ita wata sashe ne daga garesu, bata kuma da wata aminiyar da ta wuce Inteesar barci kawai ke rabasu.Nan ta d'aura da cewa wai me yasa da Inteesar zata shiga motar Jabeer ita Mufida bata shiga ba,Mufida ta sanar da ita cewa shi Jabeer d'in ne ya ce su biyu zasu tafi.Har Jabeer d'in ta tsare da tambayoyi ya nuna Mata ba komai a tsakaninsu.
Washe gari ranar da abokan Muhdeen zasu zo, Sumayya na kitchen tana shirya masu girkin tarbar su.Waya ta d'auka ta hau internet don ta samu tasan yadda zata girka masu lafiyayyen jallop.da Farfesun naman kaji.wayar na gabanta tana kallo kuma tana had'a abubuwan girki,a zuciyarta tana ayyana wahalar da akeyi a yayin da ake girki.ta kwashe awa biyar a kitchen tana girka jallop d'in shinkafa da Farfesun kaji.Muhden ne da dawowarsa kenan daga masallaci ya shigo kitchen d'in Jin k'amshi na tashi kitchen d'in sai yanon girkin yakeyi tun baici ba.