← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 99

Sashe 49

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mufida ce ta lalubo lambar wayarsa ta kira amma switch off,sau biyar Mufida na kiransa amma the same thing,kallon Inteesar ta yi tare da cewa
"Duka lombobinsa fa a kashe,basa shika Wallahi."
Dafe kai Inteesar ta yi tare da cewa
"To yanzun meye mafita?"
"Bari to na gwada kiran layin yaya Jabeer nasan dukkansu yanzun suna Asibiti dukkansu."
Lamabar Jabeer ta lalubo ta danna masa kira.

Jabeer dake zaune a office d'insa yana duba patient,wayarsa ce take ruri bai kula ba har ta katse,sai da aka sake kira ne ya d'aga tare da cewa
"Mufida ya akayi ne ya mutanen gidan?"
"Yaya Jabeer dama layin yaya Muhdeen ne a kashe,kuma Inteesar ke son magana da shi."
"Okay lafiya dai ko?don ya shiga tiyata ne yanzu."
Kai ta jinjina
" Okya ba damuwa Allah ya bada sa'ar aiki,idan ya fito ka sanar da shi."
"Insha Allah zan sanar da shi."
Daga nan ya katse kiran ya cigaba da abinda ya keyi.

Bayan sun gama magana ne Mufida ta juya ta kalli Inteesar ta ce,
"Gaskiya zan tafi,don mijinki yana d'akin tiyata ,idan ya fito na ce yaya Jabeer ya sanar dashi kinga may be ya kira lambar Gwaggo ya ji dalilin kiransa,yanzun kinsan wayar Gwaggo kinsan bata ajiye waya fili sai cikin kaya ayi ta kira bata sani ba,kinga idan ya Kira sai ki sanar dashi idan ya barki kindai san gidan sai mu had'u a can, amma fa ba dad'ewa zanyi ba zan tafi kitso."
Daga nan ta mik'e tare da musu sallama ta tafi.

Baya awa biyu ne sai ga wayar Gwaggo ta fara ringing,dubawa tayi tare da d'aga kaiwa a kunne.

"Assalamu Alaikum"
Muhdeen da ke zaune a office d'insa ya fara magana
"Barka da gida Gwaggo."
Washe baki tayi tare da cewa
"Muhammadu ya aiki?"
"Alhamdulillah,naji ance kuna nema na ne."
"Eh matarka ce wai mahaifiyar k'awarta Allah ya mata rasuwa,shine Mufida ta biyo mata su tafi tare."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Allah ya jik'anta,ina ita Mufida take?"
"A'a itakam Mufida kam ina zata tsaya jiran matarka,kai da aka ce kana can kana farke cikin cikin mutane ne zata tsaya jiranta?"
"Mufida ta tafi kenan?"
"Eh sai dai ita matar taka ce ake jiran ka fito ka bata izini ta tafi."
"To ban bada izinin ba."
"Ban gane baka bata izini ba,gaisuwar mutuwa ce fa zata."
"Gwaggo ta tsaya tayi masu addu'a a gida,ita k'awar kuma ta kira ta a waya tayi mata ta'aziyya."
Girgiza kai Gwaggo tayi kamar yana ganinta ta ce,
"Haba Muhammadu, Mahaifiyar k'awarta aka ce ta rasu,kuma k'awa ce ta sosai ko lokacin bikinku ta yi k'ok'ari har nan gidan ma ta zo sannan sai ka hanata zuwa?bai kamata ba."
Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya ce
"Shikenan ta sanar da Ishaq Direba ya kaita tayi ta'aziyya ya dawo da ita."
"Yauwa da'n albarka,Allah ya dawo mani da Kai lafiya."
"Ameen ya Allah"
Daga nan ta katse kiran ta kalli Inteesar ta ce
"Ina fatan kinji duk maganar da mukayi."
Kai ta jinjina lamar eh,sannan ta ce
"Nagode Gwaggo bari na d'auko hijabi na na kira Ishaq mu tafi."
"Amma fa kar ki dad'e"
"Insha Allah Gwaggo bazan dad'e ba."
Daga nan ta shiga d'akinta,ba jimawa ta fito rik'e da hijabinta tana sakawa,ta rik'e handbag d'inta ta fice.

A harabar gidan da k'ara ta ke tambayar mai gadi ko ina Ishaq,inda mai gadin ya shaida mata cewa yanzun nan aka kirasa a waya 'yarsa ba lafiya shine ya tafi gidan
Jin hakan yasa ta ce da mai gadin Allah ya bata lafiya,daga nan ta fita zuwa bakin titi ta tsaida mai keke napep ta shiga zuwa gidansu wasila.

Har k'ofar gidansu Wasila mai adaidata sahun ya ajiye ta,bayan ta shiga ne ta gaida mutanen sa ke cikin gidan tayi masu ta'aziya sannan ta nufi falon gidan nan ma cike yake da mata masu kar'bar gaisuwa,bayan ta gaishe su tare da masu ta'aziyya ne ta nufi d'akin Wasila,nan ta samu K'awayensu wad'anda suka gama school tare dasu a d'akin,nan dai suka gaisa ta tayiwa Wasila ta'aziyya da addu'o'i,zama tayi suka cigaba da kar'bar gaisuwa.

Suna nan har aka kira sallar la'asar,nan wasu suka dinga tashi dan gabatar da sallah,dama koda Inteesar bata ga Mufida a gidan ba batayi mamaki ba dan dama Mufida ta ce ba zata dad'e ba zata tari wajen kitso ne.

Bayan ta idar da sallah ne tayi masu sallama dan tafiya gida, kasancewar akwai d'an tazara zuwa bakin titi yasa ta fara tafiya dan neman abun hawa.

Wata jar mota ce ta tsaya a gabanta tare da yi mata horn,ko kallon motar ba tayi ba ballantana tasa waye a ciki,tafiya ta cigaba da yi shima matuk'in motar ya dinga binta a hankali yana danna horn,ganin abin nasa ne taga yayi yawa yasa ta juya ta kalli motar,ba kowa bane illa Usman sai murmushi ya ke sakar mata,da mamaki ta kalle shi tare da furta sunansa
"Usman"
Zaune yake a mazaunin Direba yayin da k'anwasa Khadija ke zaune a gefensa,itama murmushi ta sakarwa Inteesar tare da cewa
"Lallai yaya na yayi gaskiya,muna cikin tafiya ya hangoki ya ke sanar dani cewa kece nace ya za'ayi ya sani tunda baiga fuskarki ba?ya ce to bari mu k'arasa na tabbatar,ashe kuwa kece."
Murmushi Inteesar ta sakar mata tare da cewa
"Nice Khadija da ace ba tare da Usman na ganki ba wallahi bazan gane ki ba."
"Saboda kinsan had'uwa ta dake lokacin da na samu accident ne ina asibiti,tun lokacin bamu sake had'uwa ba."
"Ni kuma duk inda na ganki zan gane ki,saboda pics d'inki da ke wayar yaya na."
Da mamaki Inteesar ta kalli Usma
"Ina ka samu pics d'ina awai wad'anda na d'auke ki a asibiti ba tare da saninki ba da wad'anda na d'auke ki a k'ofar gidanku ranar da na je akan magani zan Kai maki."
Jinjina kai Inteesar ta yi ba tare da ta ce komai ba,jin muryarsa ta yi yana cewa
"Daga ina zuwa Ina?"
"Daga gidan rasuwa zuwa gida"
"To ki shigo nan gaba kad'an zan aje Khadija sai na k'arasa dake gida."
Kai ta girgiza alamun a'a
"Ka barshi kawai zan shiga adaidata sahu."
Nan dai suka matsa mata akan cewa sai ta shiga,dakyar ta amince ta shiga,tafiyar mintuna biyar ya ajiye Khadija a wani shagon saloon inda ya umarci Inteesar ta dawo gaban motar,dan haka ta dawo gaban motar sannan yaja suka tafi.

"Me yasa kullun na kira wayarki bata shiga,tun ranar da muna cikin magana kika katse kiran ban sake samumki ba."
Tasao ta sanar da shi ita matar aure ne a yanzun amma kuma wannan ai ba aure bane,tunda da zarar matarsa ta dawo zai sake ta,don haka ta yi shiru ta ce
"Bana da waya ne."
"Okay badamuwa mun kusa k'arasawa Ubasanjo complex sai mu shiga ki za'bi kalar wayar da kike so."
Da sauri ta kalle shi
"Dan Allah ka rufa mani asiri,yanzun idan ka siye mani waya me zance idan na koma gida?"
Dariya ya yi
"Kedai akwai matsoraciya to meye a ciki?nifa so nake su san da ni fa,duk da sun sanni amma ina son susan cewa aurenki nake so."
"Naji amma duk da haka ba yanzun ba,kaga yamma ta yi ina sauri na koma gida."
Dariya yayi yare da cewa
"Kinfi son ki zauna kurma ko?"
Da mamaki ta kalle shi
"Kamar ya kurma?"
"Eh mana ai duk mutumin da bashida waya kurma ne."
Dariya ya bata sosai har saida dimful d'inta suka lotsa fararen hak'oranta suka bayyana.

Muhdeen dake tsaye daga tsallakensu gaban access bank yana magana da wani,kamar ance ya juyo kwatsam idanunsa suka sauka kan Inteesar da Usman,tana zaune a gaban motarsa sai dariya take masa harda hak'oranta,want abu ne yaki kamar mashi ya soki zuciyrsa,tunda ya ke bata ta'ba masa dariya ba ko da ita da Gwaggo take dariya da ta ganshi zata had'iye dariyar,amma gata zaune gaban motar wani k'ato tana masa dariya,ransa yakai k'ololuwar 'baci,garan gadan ya nufi tsallakowa titin cikin zafin rai da k'unar zuciya.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Comment &,shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.

Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.
*JINJINA*
Jinjina ta musamman gare ku masoya na, na yaba kuma nagode da addu'ar da kuke mani Allah yabarmu a tare nayi wannan shafin tukuici ga masoya na na group d'in *INTEESAR HAUSA NOVEL* ina jin dad'in comment da addu'o'i da kuke mani i love you lodi-lodi.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page4
Ransa yakai k'ololuwar 'baci gadan gadan ya nufi tsallakowa titin cikin zafin rai da k'unar zuciya,cikin rashin sa'a ga cunkoson ababen hawa sunyi yawa, kasancewar yamma ne kowa na kiciniyar komawa gida.

Kamar ance ta kalli gefenta can ta hangoshi duskarnan tasa a murtuk'e,kuma idonsa na kanta,gaban ta ne ya fad'i dan har sai da hanjin cikinta suka kad'a, cikin tashin hankali ta dubi Usman ta ce,
"Dan Allah mubar wajennan yanzun nan"
Da mamaki ya kalleta
"Lafiya?"
"Ba lafiya kaidai mubar nan yanzun nan"
Cikin sauri ya tara motar suna barin wajen sai ga Muhdeen ya tsallako,kad'an ya rage bai same su ba,cizon yatsarsa yayi cikin takaici da k'unar,don da ya same ta baisan iya abunda zai mata b.

Komawa yayi wajen mutumin da suke magana ya kallesa ya ce,
"Kaga zamu yi magana a waya."
Bai jira cewarsa ba kawai ya shiga motarsa ya tafi,mutumin na masa magana yana tamabayarsa ko lafiya amma ina bai saurare shi ba ya ja motar ya yi tafiyrsa.

Inteesar suna tafiya akan titi sai azalzalar Usman take kan yayi sauri,da taga yabi hanyar gidansu ta ce a'a ba gida zata ba,tayi masa kwatancen inda zai kaita.
Chapter 49 · 0% Book details