← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 99

Sashe 30

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuba masa ido Muhdeen yayi,kafin ya d'aura da cewa
"Haka take duk lokacin da aka 'bata mata rai sai tayi asarar duk abunda ya tari gabanta,amma ban ta'ba tunananin cewa zata iya k'ona kayayyakin lefen nen ba,amma hakan Bai rasa nasaba da cewar kishi ne yasa ta k'ona kayan lefen nata."
"Muhdeen zan baka shawara guda d'aya,shawarar kuma ita ce kada ka ajiye Inteesar a cikin gidannan,don idan har ka had'asu gida guda wata rana wannan mahaukaciyar matar taka zata iya kashe Inteesar ko ma ta illata ta,mafita d'aya ce shine ka raba masu gida,ka Kai Inteesar wancan gidan naka."
Wani kallon irin Wanda ke nuna alamar bazaiyuba muhdeen ya watsawa Jabeer.

"Wani gidan ne zan Kai ta? gidan da na gina da sunan Sumayyata ne zan d'auki waccan kucakar yarinyar na ajiye a ciki?."
Da mamaki Jabeer ke binsa da ido jin kalamansa
"Kamar ya?me kakae nufi ne?"
"Kai nifa wallahi ka daina mani maganar yarinyar nan ba itace a gaba na ba,aure dai an d'aura ko to shikenan tunda haka suka so,amma bazan ta'ba kallon wannan kucakar yarinyar a matsayin mata ba.Yanzun kawai ka sanar dani yadda za'ayi na shawo kan Sumayya."
Tsaki Jabeer yayi cikin jin takaicin maganganun da Muhdeen ya fad'a sannan ya ce,
"Wannan matsalarka ce ni inada abunyi,nabar aiki a asibiti sakamakon kiranka so zan koma patient na jira na,kaima ka shirya dawowa bakin aiki don ayyuka sun mani yawa."
Yana Kai K'arshen zancensa sai ya nufi motarsa ya shige,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa ya fice yabar muhdeen yana mamakin me yasa duk 'yan uwansa suka juya masa baya akan Sumayya.

Wayarsa ce tayi k'ara sunan Mummy ce ya bayyana a kan fuskar wayar,bayan ya d'aga kiran ne ta shaida masa cewa tana buk'atar ganinsa yanzun a gida.Daga nan ta katse wayar shi kuma ya shiga ciki d'akin Sumayya ya nufa still a kulle k'ofar take hakan yasa ya nufi bedroom d'insa key d'in motarsa ya d'auka ya nufi gidan iyayensa.

Koda ya ya isa gidan horn yayi mai gadin gidan ya lek'o ganin motar Muhdeen ne yasa cikin azama ya bud'e masa gate,bayan yayi parking ya fito ne ma'aikatan gidan suka dinga gaishesa amma ko kallonsu baiyi ba hannu kawai ya d'aga masu don ransa yakai k'ololuwa wajen 'baci.

Gwaggo ce da Mummy a falon suna tattaunawa sai Mufida dake zaune kan center carpet,don Mufida ma Bata San da zancen auren ba sai yau.Kuma Mummy ta kwa'beta cewar kada ta fad'i ma Inteesar zancen auren,su manya zasu San yadda zasu fad'a mata cikin hikima don kada ta tashi hankalinta.

Da sallama ya shigo falon gaba d'ayansu suka amsa masa sallamar, inda ya k'araso ya durk'usa ya gaida Mummy
"Ina wuni Mummy"
Cikin sakin fuska ta amsa masa
"Lafiya lau son ya Sumayya take"
Jim ya d'anyi don bazai iya sanar dasu halin da yake ciki da Sumayya ba,cikin sanyin jiki ya ce,
"Tana lafiya lau Mummy"
Ganin yanayin d'an nata da yanayin maganarsa ta fahimci cewa akwai wata matsala don haka ta d'aura da cewa
"Ka sanar da ita zancen auren ne?"
Kai ya jinjina
"Eh na sanar da ita Mummy"
"Masha Allah ina fatan dai ba wata matsala kuma Sumayyar Bata tashi hankalinta ba,duk da nasan kowace mace ce dole zata shiga damuwa kishi kumallon mata ne."
Bazai iya yi wa mahaifiyarsa k'arya ba,kuma bazai iya sanar da ita halin da suke ciki ba.

Jin muryar Mummy yayi ta cigaba da cewa
"Son don Allah ka rarrasheta,ka kwantar mata hankali sosai please."
Kai kawai ya jinjina ya kalli goggo cikin jin haushin auren da tasa akayi masa ne ya kauda Kai ciki-ciki can k'asan mak'oshi yayi maganar ya ce,
"Ina wuni"
Ta'be baki tayi tare da fashewa da dariya tana fad'in
"Yaro man kaza,wato fushi kake dani ko?to kaci gaba gausuwarka ma bana so d'an k'wal uba mai zubin sadaka yalla,nayi maka gata amma ba godiya ko?zanyi maganinka ne daga Kai har wannan matar taka gata nan kamar busashshen cry fish."
Harara ya galla mata ta ta'be baki tana cewa
"Uwarka ka harara gata nan a zaune d'an k'wal uban yaro."
Dai-dai lokacin Dady ya sakko ya K'araso wajensu.zama yayin da Muhdeen ya ce,
"Dady Ina wuni"
"Lafiya lau,sauri nake dama zan fita nace Mummynka ta Kira Mani Kai,kana jina ko?"
Kai ya jinjina
"Eh Dady"
"Abunda nake son na sanar da Kai shine,zancen tarewar Inteesar a ina zaka ajiyeta ne? gida d'aya da Sumayya ko kuma zaka kaita d'ayan gidanka ne?"
"A'a Dady gida d'aya zasu zauna."
Kai Dady ya jinjina tare da fad'in
" Masha Allah"
"Zancen tarewarta kuma Nan da sati d'aya zata tare."
Kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba.

Zancen kayan lefe kuma Ni da kaina zan bada kud'i a had
Kafin yakai k'arshen zancen Gwaggo tayi saurin cewa
"Sani akan me zaka bada kud'in kayan kefe?ai bazai yi wu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta?shi da kansa ya siya,to haka ma Inteesar shi ne da kansa zai siya saboda hakan zaisa ya san mahimmancinta a gare shi."
Daga alkalamin
Maman Ihsan
Don K'arin bayani
09065327995
Love U oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa shi ta kowace siga.

Wannan kagaggen labari banyi tunanin rubutashi shi dan cinzarafi kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku garface ni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.

Page3
"Sani akan me zaka bada kud'in kayan kaya lefe? bazaiyuwu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta ta?shi da kansa ya siyo,to haka ma Inteesar shine da kansa zai siya,saboda hakan zaisa yasan mahimmancinta a gare shi."
Kallon takaici Muhdeen ke yi wa Gwaggo sai da ta Kai K'arshen maganarta sannan ya ce,
"Banda kud'in da zan siya mata wani kayan lefe yanzu,dududu Yaushe nayi auren?sati biyu kenan fa kinsan miliyoyin da na kashe a lokacin auren nan kuwa?banda wani kud'in lefe yanzun keda kika had'a auren sai ki siya mata kayan lefen."
"Dan k'aniyarka ba gata nayi maka ba?"
Bud'e baki yayi da niyyar maida Mata da martani Dady ya daka masa tsawa.

"Kai Muhammad ka shiga hankainka , Mahifiyar tawa ce kake maidawa magana a gabana?"
Sunkuyar da kansa yayi k'asa yayin da Gwaggo ta d'ora da cewa
"A'a Sani ba ruwanka da shi ai wannan tsakanin kaka da jika ne ka kyalemu kawai."
Jinjina kai Dady yayi tare da kallon Muhdeen ya ce,
"To na dai sanar dakai sati mai zuwa Zata tare a gidanka,sannan batun kayan lefe Kai da kanka zaka had'o mata ne ko kuma kud'i zaka bayar?"
Hannu ya saka cikin aljihun wandonsa ya ciro A.T.M card d'insa ya mik'awa Mummy.

"Ga shinan duk abunda kuka siye sai ku cire ku biya tunda kinsan pin d'in."
Amsar A.T.M card d'in tayi tare da sa masa albarka.Dady ya mik'e don dama Shirin fita yayi,daga nan yayi masu sallama ya fita.Mummy ce ta ce,
"Bari na shiga ciki na d'auko waya ta na kira Aunty Abla ta shirya gobe zamu je mu had'o kayan lefen."
Daga nan Mummy ta mi'ke ta nufi d'akinta,Gwaggo ce ta kalle Mufida ta ce,
"Ke 'yar nan tashi ki d'auko Mani magani na nasha don anjima zamuje mu d'auko Inteesar"
Cikin zumud'i Mufda ta Fara magana
"Gwaggo anjima za'a d'aukota?"
"K'warai kuwa anjima za'a d'aukota mu kawota gidannan idan sati d'ayan yazo sai a kaita gidan mijinta."
Cikin farin ciki ta nufi d'akin Gwaggo yayin da Muhdeen ya mik'e ya fice, Gwaggo na ce masa
"Asauka lafiya"
Ko kallonta baiyi ba ya daka Kai ya fice.

Inteesar ce zaune a gaban Abba da Umma a tsakar gidansu,Abba ya kalleta cikin nutsuwa ya ce,
"Inteesar"
Jin yadda yadda Kira sunanta cikin wata irin murya yasa ta zuba mada ido tana jiran Mai zaice.

"Kiyi hak'uri na yanke shawara akanki ba tare da na tuntu'be ki ba,banyi shawara dake ba naji r'ayinki ba kiyi hak'u..."
Idonta ne ya ciko da k'walla cikin rawar murya ta fara magana
"Abba don Allah ka daina bani hak'uri akan koma meye,nice ya kamata na baka hak'uri ba Kai ba,duk shawar ko hukuncin da ka ga ya dace ka yanke akaina dai-dai ne Abba.Ni Mai biyayya a gare ka na ka daina bani hak'uri idan kana bani hak'uri ji nake kamar ban cika 'ya Mai biyayya a gare ka ba."
Shiru yayi cikin alfahari da 'yar tasa ya fara magama
"Na aurar da ke"
Da sauri ta d'aga ido tana kallonsa da mamaki,ganin irin kallon mamamkin da takeasa ne ya sashi fad'in
"Kiyi hak'uri"
Sunkuyar da kanta tayi k'asa hawayen da suka taru mata ne suka samu nasarar zubowa,cikin rawar murya ta ce,
"To Abba "
Hawaye ne suka cika idanun Umma Don bata ta'ba kowa wa a ranta cewa Nan kusa zata rabu da 'yarta tilo ba,Amma gashi k'addara tasa lokaci guda ba zato ba tsammani zasu rabu ba,ita da ganinta sai ranar da tazo gaishesu.Abba ya cigaba da cewa
"Ki kasance Mai biyayya ga mijinki yi nayi bari na bari duk abunda ya umarce ki da kiyi masa to kiyi masa matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba.sannan ki zauna lafiya da abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wacce take gaba dake,ki zama mai kauda kai akan al'amarin mijinki da abokiyar zamanki,kiji kik'i ji ki gani kik'i gani ki zama Mai kyautatawa ga kowa mijinki da danginsa da kowa da kowa.Ki zama Mai nutsuwa da kamun kai a duk inda kike,ki girmama mijinki kibi shi sau da k'afa kindai ga irin zaman da mukeyi da Mahifiyarki a cikin gidan nan kiyi koyi da ita."
Nan dai ya cigaba da Mata nasiha masu ratsa jiki Umma ma ta d'aura da nata, Inteesar dai kanta a sunkuye yake sai kuka da takeyi.Ganin kukan nata yayi yawa ne yasa Abba ya Umarce ta da ta tashi ta shiga d'akinta.
Chapter 30 · 0% Book details