Sashe 63
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
INTEESAR!!!"
Jin shiru ne yasa tayi kwafa ta nufi kitchen d'in a fusace, tana shiga tayi turus tayi ganin kitchen d'in wayam ba alamar ma anyi girki, ranta a 'bace ta furta
"Lallai ma yarinyar nan wuyanta ya isa yanka, ubanwa ta ajiye da zai mata aikin da bata yi ba? lallai yau zanyiwa yarinyar nan wulak'ancin da ban ta'ba yi mata ba."
Kai tsaye ta nufi part d'in Inteesar, dan zuwa d'akinta, da k'afarta ta bankawa k'ofar duka, k'ofar ta bud'e ta shiga ciki tare da cewa
"Ke 'yar matsiyata ubanwa za..."
Dakatawa tayi da maganar da tayi niyar yi sakamakon ganin k'awatuwar d'akin inteesar d'in, kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara shigowa d'akin, ganin furniture's masu tsada da aka zuba mata ga d'akin yasha gyara sosai komai na d'akin abun sha'awa ne, ta'be baki tayi tare da cewa
"Ina wannan ba iyayenta bane suka sayi mata wannan kayan d'akin, don ba suda kud'in siye mata su, bayan naji ance uban nata dankali yake siyarwa bazai iya siyen ko kwatankwacin kayan nan ba sai dai idan iyayen Muhdeen da suka had'a auren ne suka siye mata, ganin ba kowa yasa ta k'arasa bakin k'ofar toilet ta k'wank'wasa jin shiru ne yasa ta nufi hanyar fita.
Bata zame ko ina ba sai k'ofar d'akin Muhdeen,tura k'ofar tayi tare da shiga,har toilet ta shiga bata ganshi ba tambayar kanta tayi da cewa
"Ina yaje ne kuma?"
Idanunta ya sauka akan gyalen d'an kwalin inteesar dake gefen gado, sai kuma d'an kunnenta guda d'aya shima a saman gadon, gabanta ne ya fad'i Wanda sai da taji wani abu kmar dutse ya danne mata k'irji.
"Me nake shirin gani ne haka? me d'an kwalain yarinyar nan yake yi. d'akin nidai nasan bazai ta'ba nemanta ba don bai d'auke ta a mace ba, wata kila ta shigo gyara masa ne d'an kunnen ya fad'i ta mance d'an?"
kwalinta.
"To wai Ina my love ya je ne? d'an jim taui tare da k'arewa d'akin kallo tayi sannan ta fice ga uban yinwa da ke cinta kuma ita bata iya girka komai ba ki ruwan zafi ba zata iya dafawa ba, rasa abunyi tayi Dan haka ta nufi d'akinta wayarta ta d'auka wayarta number Muhdeen ta shiga kira yakai sau biyar tana kirnsa bai d'aga ba dan haka ta ajiye wayar ta shiga tagumi tana mamakin sauyawar da Muhdeen yayi daga jiya zuwa yau ya canza mata sosai da sosai, fita tayi tare da Kiran Direban gidan ta aike shi yayi mta takeaway ko zata samu abincin da zata ci.
Inteesar da Mufida suna komawa wajen Umma suka tare ta farka, da farin ciki inteesar ta k'arasa wurinta ta rungume ta.
"Umma na ya jikinki?"
"Da sauk'i kunyi sallar?"
"Eh munyi Umma"
Mufida ce ta ce
"Sannu Umma ya jikinki?"
Murmushi ta yi
"Da sauk'i Mufida"
Kallon gefen su Mummy tayi tare da cewa sannu
"Sannunku Gwaggo"
Gwaggo da Mummy suka had'a baki wajen amsawa, sai a lokacin idanunta ya sauka akan Muhdeen, tana kallonsa taga ya zuba mata ido yana kallonta tare da sakar mata lallausan Murmushi, da sauri ta d'auke kanta tare da tura baki, karaf akan idanun Ummanta sai dai tayi shiru tunda tana fama da kanta,Mama Huraira ce ta ce da inteesar
"Inteesar tunda kika zo banga kinci komai ba, kina ta zama da yinwa."
Murmushi ta yi tare da cewa
"Mama Huraira na k'oshi"
Muhdeen ne ya kalle ta ya ce
"Me kika ci da kika k'oshi? biyo ni mu tafi office d'ina kici abinci"
Kunyar mutanen da ke wurin ne ya kama inteesar, shi kuma baiga abun jin kunya a wurin ba, fita yayi ta zauna kamar bata ji me ya ce ba, Mama Huraira ce ta kalle ta ta ce,
"Ba kiranki mijinki yayi ba?"
Tura baki tayi ta ce
"Nifa na k'oshi"
Had'e fuska Mama Huraira ta yi tare da cewa
"Bana son gardama"
Dan haka dole ta fita, tsaye ta same shi yana jiranta, Dan haka suna fita ya rik'e hannunta yaja suka fara tafiya hannunsu sark'e cikin na juna sunyi kyau sisai, tayi k'ok'ari ta k'wace hannunta amma ina ta kasa da haka ta bishi suka dinga tafiya a hankali, duk inda suka wuce mutane sai an kalle su yadda suka dace da juna, kasancewarsa Doctor da aka sani yasa mutane ke ta gaishe su, ita dai ko amsawa bata yi, har office d'insa suka nufa suna shiga ya tura k'ofar ya rufe , wayarta ce ta soma ringing ta ciro daga cikin jaka ganin sunan Usman ne yasa gabanta ya fad'i, har ta katse bata d'auka ba sau uku yana kira bata d'aga ba,ganin yanayinya yasa ya gane akwai wani abu .
"Ya ana kiran wayarki baki d'agawa."
"Eh kiran baida mahimmanci ne."
Take sai ga wani kira ya shigo, duba sunan me kran yayi Usman, take ya murtuk'e fuska don ya tuna cewa Usman ne saurayin da ke son inteesar, lokacin da Mummy ta matsa ya je gidansu inteesar ya gaishe ta Usman ya kad'e ta da mota, kuma shine wanda ya ta'ba kama ta tana waya da shi bayan aurensu har ya amshe mata wata gaba d'aya, kuma shine ya gansu ya d'auko inteesar a gaban motarsa tana tayi masa dariya shima yana mata kallon soyayya, take yaji wani d'aci a ransa har idanunsa suka rikid'e suka koma ja, text message ne ya shigo wayar ya mik'a mata hannu tare da cewa
"Bani wayar nan"
Shiru tayi tare da zuba masa ido banu alamar tsoronsa a tattare da ita kmar yadda ta saba tsoronsa, don haka itama sai ta had'e fuska kamar yadda ya had'e nashi fuskar.
*Daga alk'alamin*
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don neman k'arin bayani*
09065327995
Love you oll
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page5
--------Shiru tayi tare da zuba masa ido ba alamar tsoronsa a tattare da ita, kamar yadda ta saba tsoronsa, don haka itama sai ta had'e fuska kamar yadda ya had'e nashi fuskar.
Fusgar wayar yayi daga hannunta dai-dai lokacin da sak'o ya shigo ya fara karantawa kamar haka.
"ASSALAMU ALAIKI YA SARAUNIYAR MATA, DAN ALLAH KI DAINA AZABAR DA NI HAKA, KINSAN HALIN DA NA SHIGA NA RASHIN GANINKI KUWA?
YANZUN HAKA INA K'OFAR GIDANKU ANCE BA KOWA A GIDAN, DAN ALLAH KI TAIMAKA KI 'DAUKI WAYA TA KO ZANJI SANYI A ZUCIYA TA, DOMIN RASHINKI A RAYUWA TA TAMKAR JIRGIN SAMA NE BABU MATUK'I, I LOVE YOU."
Bayan ya gama karantawa ne ya kalle ta tare da cewa
"Wato har yanzun kina waya da tsohon saurayinki da igiyar aure na akanki ko?"
Murmushin takaici tayi ta ce,
"Igiyar aurenka yana wuyar matarka da ka baro a gida, dan ni ba igiyar aurenka a kaina, zaman da nake a gidan kurkukukun gidanka k'addara ta ce kuma tazo k'arshe da yardar Allah, dan zama da kai ya zama tsautsayi da k'addara, jiranka kawai nake ka sauwak'e mani naje na auri masoyi na mai son farin cikin rayuwa ta ba irinka ba mugu azzalumin mutum mai bak'ar zu..."
Kafin takai k'arshen maganar da tayi niyar fad'i sai ta ji saukar mari tass a gefen fuskarta, idanunsa gaba d'aya sun rikid'e sun koma jajir kamar garwashin wuta jikinsa har rawa take ya ma kasa magana sai kallonta take, itama dafe kumatunta tayi tana kallonsa sam bata ji zafin marin da ya mata ba, saboda bak'in ciki da ta k'unsa masa lokaci guda ya gusar da zafin marin, ko ba komai zuciyarta tayi fari tunda ta zama sanadiyar 'bacin ranta, fita yayi a fusace kai tsaye ya nufi office d'in Jabeer.
Bayan fitarsa itama ta nufi k'ofar fita ta janyo k'ofar ta jita a datse, ya rufe ta ya tafi da key d'in, komawa tayi ta zauna kan kujera mai zaman mutum uku tare da fashewa da kuka.
Jabeer na k'ok'arin fita da file a hannunsa Muhdeen ya shigo, ganin yanayinya yasa ya koma ya ajiye file d'in tare da k'arasawa kan kujerar da Muhdeen ya zauna, dafa kafad'arsa yayi tare da cewa
"Bross ya akayi ne? wa ya ta'bo ka ne?"
Uffan baice masa ba, shima yasan bazai tanka masa ba, don yasan halinsa dama idan har aka 'bata masa rai baya iya magana duk juyin da za'ayi kuwa bazai ta'ba magana ba idan ransa ya kai k'ololuwar 'baci, ba abunda yake tunawa kamar kalamanta da take cewa jira take ya sake ta ta auri wanda yake son farin cikinta ba irinsa ba mugu azzalumin mutum mai bak'ar zuciya, rintse idanunsa yayi tunawa da kalamanta, shi kansa ya yarda cewa yana jin son yarinyar a cikin zuciyarsa,bawanda baisan sanda son nata ya samu gurbi a cikin zuciyarsa ba.
Haka Jabeer ya dinga lalla'ba shi da kwantar masa da hankali har fushin nasa ya d'an sauka, Jabeer ne ya fita yayin da shi kuma ya d'an kishingid'a akan kujerar.