← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 99

Sashe 56

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da misalin k'arfe goma na dare Gwaggo da Inteesar suna zaune a d'akin Inteesar suna fira,na bankwana har k'arfe goma sha biyun dare yayi, Gwaggo ce ta kalli Inteesar ta ce dare ya tsala
"Yakamata kije mijinki na jiranki"
"Ni Gwaggo ba abunda zan zan masa ki bari mu kwana tare na yau kawai."
"A'a duk fira dai idan ba k'arya zamu fad'a ba duk munyi ta, bana son gardama kije kawai d'akin mijinki."
Sanin haklin Gwaggo ne yasa Inteesar ta mik'e bayan tayiwa Gwaggon sai da ta fice.

A falo ta tsaya ta tabbatar ba Wanda yaganta ta shige d'akin da take kwanciya tana barci,don dama tun ranar da Allah ya k'wace ta hannun Muhdeen ya kuma yo alk'awarin duk ranar da ta shigo masa a irin wannan lokacin sai ya kar'bi hakkin aurensa a kanta, hakan yasa bata sake yarda take d'akinsa dadaddare ba, tana shiga d'ayan dak'in ta tura k'ofar tare da rage hasken d'akin.

Washe gari Gwaggo zata tafi Inteesar sai kuka take kamar wacce aka ce sun rabu kenan, haka Gwaggo ta dinga rarrashinta har ta gaji, k'arshe dai haka ta hak'ura ta kyaleta, Direban Mummy ne yazo d'aukarta,haka suka fice Muhdeen da Inteesar dake tsaye a harabar gidan bayan tafiyar Gwaggo suka koma cikin gidan, har suka shiga Bata daina kuka ba, jin muryarsa tayi yana cewa
"Ke ki rufe mani baki da zaki sakawa mutane kuka na ba gaira ba dalili, ko mutuwa akayi maki ne? to wallahi ki rufe mani baki kafin kisha mamaki anan."
Sanin cewa mai goyon bayanta bata gidan yanzun daga ita sai shi ne a gidan, kum tana tuna irin wahalar da ya gana mata a baya ne yasa tayi shiru.

"Ki tashi ku shiga kitchen, ki shirya abinci lafiyayyae mai kyau kafin na dawo da bak'uwa a cikin gidan nan."
Da sauri ta kalle shi ta ce
"Mummy ce zata zo?"
Koma wace ce idan tazo zaki ganta,sannan wancan d'akin ki share shi ku goge shi tas ko Ina yayi fess kisa turaren wuta."
Murmushi tayi cikin Jin dad'i don a tunaninta bak'uwa ce wacce zata samu abokiyar zaman gida da fira,don haka ta saki murmushi ta nufi kitchen.

Wayarsa ce tayi k'ara ya duba yaga ita ce, d'agawa yayi tare da cewa
"Hello Baby na"
Jin muryarta yayi tana cew
"Wai Baby har yanzun Bata tafi bane?"
"Yanzun nan ta tafi,na bada umarni ne a gayara maki d'akinki a girl's maki lafiyayyaen abinci."
Yamutse fuska tayi
"Wai kana nufin wannan kucakar yarinyar ce zata girka mani abinci? nifa bana son jagwalgwalo."
Dariya yayi tare da cewa
"Kada ki damu, tunda na iya kema zaki iya, yanzun dai bari nayi wanka nazo na d'auke ki."
"Okay l love you"
"Love you too baby"
Dagana nan ya katse kiran ya nufi d'akinsa don yin wanka zaije ya d'auko Sumayyarsa ta dawo kusa dashi, farin cikinsa zata dawo gidan.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*SADAUKARWA*
Wannan sadaukarwa ne a gare ki Autar Ammi (Sakeenah) kece ta farko da kika fara kira na a waya dan jin lafiya ta kwana biyu shiru baku ji ni ba, naji dad'i da nuna k'auna da kulawa, wannan shafin naki ne kiyi yadda kike so da shi, Allah yabar zumunci.
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi da cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa.
*JINJINA*
Jinjina ta musamman a gare ki members na *INTEESAR HAUSA NOVEL* Nagode sosai da kulawarku a gare ni, Allah yabar zaman tare.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page5
Daga nan ya katse kiran ya nufi d'akinsa don yin wanka, zaije ya d'auko Sumayyarsa ta dawo kusa da shi, farin cikinsa zata dawo gidan.

Bayan ta gama duk ayyuukan da zata yi ne ta shiga d'akinta wanka tayi, ta shirya cikin riga da siket na leshi, wayarta ta d'auka tana game, k'arar k'ofa taji ta mik'e da sauri duk da bata san wace irin bak'uwa ce tazo ba amma duk da haka da fara'arta ta bud'e k'ofar.

Kwatsam idanunta ya sauka a cikin na Sumayya, sai da gabanta ya fad'i, amma sai ta dake ta k'ak'alo murmushi a fuskarta cikin sakin fuska ta ce,
"Sannu da zuwa Aunty Sumayya."
Kallon banza tayi mata tare da tare da shigowa cikin falon, saura kad'an ta bangaje inteesar sai tayi saurin matsawa baya ta bata hanya, Muhdeen ne ya shigo hannunsa rik'e da jakkarta, kai tsaye falonta ta nufa tare da zama kan kujera ta ce,
"Wash baby na gaji."
Ajiye jakkar yayi tare da cewa
"Ayyah sorry, yanzun ki tashi kici abinci sai ki kwanta ki huta ko?"
Yamutse fuska tayi tare da cewa
"Ina yarinyar nan take ne? tazo ta zuba mun abinci naci."
Juyawa yayi ya kalli falon inteesar, ganin bata nan ne yasa ya k'wala mata kira, ashe tana kwance akan kujera tana tunanin sabuwar rayuwar da zatayi da Sumayya a gidan, ta ji muryarsa yana cewa
"Kina ina ne!"
Da jin haka tasan ita yake kira don haka ta mik'e ta nufi falon Sumayya, koda ta k'arasa zaune ta same shi yayin da Sumayya ta kwanta tayi filo da cinyarsa, kallo d'aya tayi masu ta kauda kanta gefe tare da cewa
"Gani"
Tsawon mintuna uku tana tsaye bai ce mata komai ba, ta d'auka baiganta bane don haka ta juyo ta kalle shi, sai taga idanunsa akanta kallonta yake sunkuyar da kanta tayi ganin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, jin muryarsa tayi yana cewa
"Baki ganmu bane"
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce
"Naganku"
"Okay, wulak'anci ne yasa kika share mu?"
Shiru tayi masa ba tare da ta ce komai ba, shi kuma abunda ya tsana kenan yayi magana ayi masa shiru kamar ba'aji ba, hakan yasa ya daka mata tsawa.

"Sa'anki ne ni da zanyi maki magana kiyi banza Dani?"
"Cikin sanyin muryarta ta ce,
"Kayi hak'uri"
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
"Baki ga Sumayya ta dawo bane?"
"Na ganta"
"Tsabar wulak'anci ne yasa kika share ta baki gaishe ta ba?"
Kafin tayi magana ne suka hi jiyo muryar Sumayya ta cewa
"I na kuwa zata gaishe ne bayan muna auren miji d'aya tana ganin dai-dai da ita nake, bari kiji na sanar dake abunda kika manta, ni nan mijina yana sona sosai auren soyayya mukayi auren na gani ina so mukayi, ba irin naki ba auren had'i da kwad'ayi irin na iyayenki yasa suka bayar da ke ga miutumin da baya k'aunarki baya sonki da k'aunarki aka k'k'aba masa ke, to bari kiji nan gidan tamkar kinzo aikatau ne, ki d'auka gidan aikinki be ba gidan aurenki ba, dan ba mijin da ya kalle ji a matsayin matarsa, koba haka bane baby na?"
Jinjina kai yayi tare da cewa
"Duk abunda kika fad'a ai gaskiya ce, ba k'arya "
Jinjina kai Sumayya tayi ta d'ora da cewa
"Kinji abunda ya ce da kunnenki ko 'yar matsiyata kawai."
Kallon Sumayya yayi, kallo mai cike da gargad'i Wanda ta gane manufarsa, amma sai tayi kamar bata gane ba ta d'ora da cewa
"Ko ke ba 'yar matsiya...

"Tsawa ya daka mata tare da cewa."
"Stop"
Da mamaki ta kalle shi da niyyar yin magana taga inteesar na wajen, don haka tayi shiru dan yadda taga fuskarsa ya canza tasan zai iya kunyata ta a gaban yarinyar da ta raina, idanun inteesar cike tab da k'walla don ba Wanda ya ta'ba mata irin cin mutuncin da aka mata yanzun, jin muryarsa tayi ya ce
"Kije ki kawo mana abuncin mu nan"
Ba tare da ta ce komai ba ta nufi dinning area dan d'auko masu abuncin .

A babban faranti ta jero masu shi, tazo ta ajiye tare da komawa ta kawo masu ruwanda drinks, ajiyewa tayi ta koma d'akinta tare da fad'awa kan gado ta saki marayar kuka.

Bayan tafiyarta d'aki ne Muhdeen ya kalli Summayya tare da cewa
"Kada ki zak'e akan yarinyar nan da yawa fa, dan zaki iya fuskantar k'alubale."
Kallon mamaku tayi masa tare da cewa
"Kodai ka fara son yarinyar na ne?"
Gajeren murmushi yayi tare da cewa
"Me kik gani"
Ya za'ayi Ina mata magana Dan tasan banbancin da ke tsakaninmu, kuma tasan matsayinta zaka dakatar Dani?"
"Ba haka bane naga kina neman wuce gona da iri ne, duk abunda zaki mata kada ki ce zaki ci mutuncin iyayenta, ko ki zage su bana so, kuma idan yarinyar ta kura Mummy ko Gwaggo a waya ta sanar dasu abunda kike mata me kike tunanin zai biyo baya? kindai san irin k'aunar da suke mata kema shaida ce, bana son abunda zai janyo muna matsala daga ni har ke "
"Amma ai kai ne da bakimka ka fad'i cewa nan kamar gidan aikinta na d'auka 'yar aiki aka kawo mani ba kishiya ba, don na fad'a mata shine laifi na?"
"Ba sai kin fad'a mata ba, ai aikinta zata san da hakan"
Hannunta ya janyo don ta sauko ta ci abincin, zama suka yi Kan center carpet.

"To ka kira ta ko muna zamu...'
Hannu ya d'aga mata alamar tayi shiru,inda ya bud'e food flask d'in ya d'auki plate
inteesar kuwa tana kwance a d'akinta sai sheshshek'ar kuka take,zagin da Sumayya tayi mata ne ke mata ciwo a zuciya .
Chapter 56 · 0% Book details