← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 99

Sashe 26

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kira ne ya shigo wayarsa, Jabeer ke sanar dashi sun iso,fita yayi ya masu jagora suka shigo.Su uku ne suka zo Jabeer, Salisu, Bilyaminu.A falon gidan ya sauke inda ya d'an tsaya suka gaisa sannan ya nufi cikin kitchen d'in ya sanar da ita zuwansu.Fridge ya bud'e inda ya kwaahi gorunan ruwa da na lemuka ya Kai masu.Ba jimawa itama ta fito daga kitchen d'in d'auke da tray an jera food flask a kai, dinning table ta nufa inda ta jera su,sannan ta k'araso wajensu tana fad'in
"Manyan bak'i sannunku da zuwa"
Suka amsa mata cikin fara'a har suna tsokananta da cewa wai ta rik'e masu aboki gana d'aya tunda yayi aure basu sake ganinsa ba.murmushi kawai tayi,don dama ita ba Mai damuwa mutane bane.Hira sukan tan ta'ba kad'an inda Jabir ke ce masa ya dawo bakin aiki don aiki ya masa yawa,kusan sati d'aya yana hutu.Dariya yayi Yana cewa
"In dawo ina?"
Jabeer ya sake maimaitawa da cewa
"Bakin aikinka mana "
Dariya yayi tare da cewa
"Haba Bross idan ka ce na dawo yanzun ai bakayi mani adalci ba,ina laifin ma nan da wata d'aya kaga lokacin na d'an more amarci ."
Dariya suka yi gaba d'ayansu.

Salisu ya d'aura da cewa
"Allah idan baka dawo nan da one week ba a kunnensa Dady don sai na fad'a masa,ba gara kai ba naka da sauk'i ba,Ni tawa matar Bata da lafiya laulayin ciki take kullun ba lafiya ga kasala da amai ga ciwon Kai da jiri,haka nake fita naje Asibiti ballantana Kai.Ta'be baki muhdeen yayi tare da cewa
"Allah ya bata lafiya,idan saboda lailayin mace ne ba zaka je aiki ba kuwa ashe zaka dad'e kana zaune a gida."
Gayara zama Jabeer yayi Yana kallon Muhdeen ya ce,
"Yauuwa Bross tunda naga tana jin maganarka kaje ka shawo mani kanta mana."
Kallon mamaki Muhdeen ke masa yana cewa
"Kayi mata laifi ne?sannan Kai baka san yadda zaka shawo kan mace ba har sai na shawo maka kanta?karka bani kunya Mana."
"Kai dai bari kawai,abun ya wuce tunaninka,kishi ne kad'ai ke damunta akan abunda bata da tabbas akai."
Gyad'a masa kai Muhdeen yayi ya ce,
"Kamar ya kishi kuma?dududu watan ku nawa da auren?"
"Kishin zance mana kawai don ta ganni da naje gidan tare da Inteesar shine fa..."
Bai Kai karshen maganar ba Muhdeen ya ja tsuki tare da watsawa Jabeer harara yana cewa,
"Aikin banza ai ta burgeni da tayi maka haka,na lura tun randa ka k'yallara ido akan wannan kucakar yarinyar sai wani rawar k'afa kake akanta sai kace a kanta ka fara ganin mace."
"Kar ka sake kiranta kucaka don ita ba kucka bace,kuma da kake cewa akanta na faraganin mace kusan haka ne,domin akanta na fara ganin mace da ta had'a komai da komai da komai
abunda nake buk'ata daga wurin mace.Kuma mata irinta basu da yawa sai ka tara mata d'ari dakyar zaka samu guda uku irinta.Duk namijin da zai kalli Inteesar bai hango qualities d'in da ke tattare da ita ba tabbas idonsa a makance yake.

Dariya Salisu da Bilyaminu suka yi yayin da Muhdeen da Sumayya kuwa suka tsuke fuska.Salisu ya d'aura da cewa,
"Maganarka gaskiya ce,domin domin yarinyar kan Bata da makusa son kuwa k'in wanda ya rasa."
Bilyaminu ya d'aura da cewa,
"Gaskiya kam ku duba ranar da muka dawo daga reception muna jiran K'arasowar Jabeer, sai gashi da ita kunsan dai neman matan banza a wajen Bashir kamar d'an akuya baya ma zancen aure sai lalata da 'ya'yan mutane amma ranar da yaga Inteesar ya fara furta maganar aure Wai ya samu matar da zaiyi rayuwar aure da ita."
Muhdeen ne ya ya'be baki ya ce,
"Kun zauna kuna ta maganar wannan yarinyar idan shi ya kawo ku ta ki tafi can ku k'arata da zancenta amma ba gidana ba."
Jabeer ya ce,
"Au korarmu kake ko ruwa bamu sha ba?"
Sumayya ce tayi magana cikin jin dad'in kalaman mijin nata akan Inteesar ta ce,
"Kuyi hak'uri ga Abinci can da abunsa na shirya maku a dinning table."
Jabir ne ya fara mi'kewa ya na cewa
"Dama yunwa nake ji ne wallahi kasan mai dafa mani abincin ba lafiya,idan ma rowa yasa kake korarmu sai munci.Lokacin da mukayi aure gidan kowannenmu nan sai da kaci abinci sannan munzo gidanka bazamu ci ba?ai wallahi sai munci."
Muhdeen yayi dariya yana cewa
"Au abun ma bin bashi ne?."
Salaisu ya ce,
"K'warai kuwa bin bashi ne kaci na amaryar mu don haka muma sai munci."
Dariya sukayi gaba d'ayansu yayinda suka nufi dinning area.Bayan sun zazzauna sumayya tayi serving d'insu ta ajiyewa kowa a gabansa,ta zuba masu ruwa da lemu ta ajiye masu.Dai-dai lokacin wayar Muhdeen tayi ringing tashi yayi domin amsa kiran, Mummy ce ke kiransa falo ya k'arasa ya zauna Kan kujera.Bayan ta ajiye masu komai a gabansu ta zuba masu farfesun ne ta zauna tana jiran mijinta ya gama wayar ya k'araso.Jabeer kasancewar a yunwace ya ke ya Fara dibar jallop d'in yakai bakinsa tare da bisimillah,rintse ido yayi tare da ya mutse duska sakamakon uban gishiri da yajin da ya gigita k'wak'walwarsa ga shinkar duk karfi da sauri ya tofar da abincin k'asa tare da d'aukar kofin ruwa sai da ya shanye sannan ya ajiye.

Ba Wanda ya lura da Salisu shi kuma farfesun ya fara ci yana Kai naman bakinsa ya yamutse fuska,da sauri ya zaro hanki a aljihunsa ya saka naman da ke cikin bakinsa aciki ya dunk'ule a hannunsa Shima ruwa yasaha rabin kofi.Bilyaminu kuwa yana Kai cokalin abinci a bakinsa ya murtuk'e fuska Amma shi yayi k'arfin halin had'iye abincin Amma sai da ya rintse ido sannan ya Kora da ruwa.Sumayua kuwa duk Bata lura da abunda ke faruwa ba hankainta na Kan Mijinta da wayar da yakeyi.Jabeer ne ya kalli Salisu da Bilyaminu ya ce,
"Kunji abunda naji kuwa?"
Kai suka gyad'a masa ba tare da aunce komai ba.Ya cigaba da magana
"To Alhamdulillah ni kunga tafita."
Mi'kewa yayi suma suka mi'ke suka bi bayansa dai-dai lokacin da Muhdeen ya gama wayar da yakeyi,kallonsu yayi mamaki ya ce,
"Ya dai?har kun gama cin abincin ne?"
Wani irin dariya dariya Jabeer ya shek'e da shi Wanda sai da gaban Muhdeen ya fad'i,don yafi kowa sanin waye Jabeer idan yaji yayi irin wannan dariyar to tabbas ta mugunta ce.Jabeer ya ce,
"Eh mun gama cin abincin Alhamdulillah girkin Amarya yayi dad'i,kuje kuci naku aci dad'i lafiya.

Ya nufi k'ofar fita yayin da Salisu da Bilyaminu suka bi bayansa, kasancewar a motar Jabeer suka zo horn yayi Mai gadi ya bud'e masa suka fice daga gidan.Shiru muhdeen yayi yana nazarin kalaman Jabeer yasan ba banza ba, dinning area ya nufa abincin da Jabeer ya bari ne ya d'auki cokalin ciki ya d'iba tare da kaiwa bakinsa,da sauri ya tofar dashi k'asa ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in ya dafe kansa yana fad'in
"Sumayya kin kunyata ni a wurin abokaina,tunda nake ba'a ta'ba kunyatani irin na yau ba.kima mace ace baki San yadda ake gika abinci ba wannan want irin rayuwa ne?"
D'aga masa hannu tayi tana cewa
"Dakata haka nan dama ka auro ni ne don ka wulak'antani?,tunda nake a rayuwarta ban ta'ba yun'kurin shiga kitchen da niyyar gika komai ba,ko uwata da ubana basu ta'ba cewa na dafa masu Koda ruwan zafi ba Amma a Kan son da nake maka karon farko a rayuwat na shiga kitchen don na girkawa k'artin banza abinci baka yaba mani ba how dare you zaka ci mutuncina.Kuka ta saka masa,tunawa yayi da yanayin rayuwarta bata ta'ba yin girki ba Amma don ta faranta masa tayi hakan yasa ya rungumeta Yana rarrashinta.

Jabeer kuwa sai da ya biya gidajen abokansu ya sajke kowa a gidansa,Kai tsaye gidan Mummy ya nufa don hsky yunwa yake ji Yana driving yana dariyar gidan Muhdeen da suka baro a zuciyarsa Yana tausayawa Muhdeen wani 'bangaren zuciyarsa kuma baya tausayinsa, musamman idan ya tuna cin mutuncin da yayi masa lokacin da ya ce bai goyi bayan ya auri sumayya ba.
Chapter 26 · 0% Book details