← Book details Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 99

Sashe 3

Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan mummy sun kammala cin Abincin ne Mufida ta kwashe abubuwan da suka Bata ta nufi kichen, Inteesar ta goge wajen ta nufi kitchen dan wanke kwanika da sukayi amfani dashi, Mufida dama dakinta ta wuce, Mummy ce ke zaune a falo tana kallon news,
bayan Inteesar ta gama ta fito dai-dai lokacin wayar dake kan dinning ya fara ruri, Mummy ta juya ta kalli wayar tare da cewa
"Inteesar Dan Allah d'auki wayar nan na Son kikai masa Ina ganin ya mance da ita ne"
Rass gaban ta ya fad'i Jin abunda Mummy tace,ba yadda ta iya haka dole ta karasa ta dauki wayar da haryanzun take ruri sunan da ta gani a wayar shine my happiness,
Azuciyar ta ta ce budurwar sa ce ke kiransa cikin fad'uwar gaba ta nufi part d'insa tayi knocking sau uku taji shiru sai tayi tunanin ko barci yakeyi,don haka da sallama ta murda handle din k'ofar ta shiga,ba kowa sai kamshin turare dake tashi ta nufi bedside drawer ta Duk'a ta ajiye wayar dai-dai ya fito daga toilet kenan yana daure da towel a k'ugunshi sai karamin towel dayake tsane ruwan kansa juyowar da zatayi taji taci karo da mutum wani razanannen ihu ta saki cikin tsoro...

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.

Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya,to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Page0
Wani razanannen ihu ta saki tsoro ne ya sa ta fad'a jikin sa ba tare da ta sani ba,cikin hanzari ta kalleshi shi,idon ta ne yayi tozali da kwantaccen gashin kirjin sa da suka kwanta luf a faffad'en kirjin sa da sauri ta runtse ido tare da ja baya cikin tsoron sa, mugun kallo ya watsa mata tare da daka mata tsawa cikin d'aga murya yace,
"Uban waye ya baki izinin shigowa nan har cikin bedroom d'ina?"
Cikin tsananin tsoron sa da takeyi kanta a kasa, ta fara magana cikin in'ina ta ce,
"A'a Dddmma in in mu mm mm mummy ce ta ta tace na kawo maka wayar ka."
Ta karasa maganar tana nuna masa wayar da hannun ta
juyawa yayi ya kalli wayar da ta nuna masa,
Tsawa ta daka Mata tare da numa Mata hanyar kofar fita.

Cikin daga murya yace,
"Get out"
Cikin sauri-sauri gudu-gudu tabar dakin,ya bita da harara tare da karasawa ya rufe kofar da key yace,
"Mayya"
Ya koma cikin d'akin ya karasa gaban dressing mirror ya d'auka lotsion d'in shi ya fara shafawa.

Bangaren Inteesar kuwa yadda ta Fado falon Mummy ne yasa ta daga Kai ta kalle ta sauri.

"Ke lafiyarki kuwa ya haka kamar an koraki"
Girgiza Kai Inteesar tayi ba tare da tace komai ba,sake jin muryar Mummy tayi tana cewa,
"Ko Muhdeen d'in ne ya maki wani abun?"
Kai ta girgiza tare dacewa,
"Babu komai mummy ba korata yayi ba."
Shine kika shigo kamar wacce aka koro?"
Kanta ta sunkuyar cikin sanyin murya ta ce,
"Mummy zan tafi gida"
Mummy ce ta kalle ta tace,
lapiya yau zaki tafi yau da wuri haka?"
Kai ta gyad'a tace
"Eh Mummy bari na tafi dan nasan Umma na jira na."
Murmushi mummy tayi tare da cewa,
"Shikenan ki gaida Mani da umman taki"
Kai tsaye ta nufi hanyar fita Mummy tabita da kallo tana murmushi cike da son yarinyar.

Da sallama ta shiga cikin gidan, Umma da fitowarta kenan daga band'aki rike da bokiti alamun wanka tayi.

"Wa'alaiki Salam Inteesar har kin dawo?"
Murmushi ta k'ak'alo akan fuskar ta ta ce,
"Eh umma nagaji ne shine nace bari na dawo nayi sallah na d'an kwanta
"To shikenan "
Cewar ummin yayinda ta d'auki buta ta zauna a kujerar tsakar gida ta Soma alwala .

Inteesar ma dakin ta ta shiga ta ajiye hijabin ta,ta fito ta dauki buta ta shiga ban daki ta fito yazauna inda umma ta tashi,ta soma yin alwala cikin nutsuwa.

'Bangaren Muhdeen ma fitowa yayi daga part d'in a inda yasamu Mummy zaune ya kalleta yana murmushi.

"Mummy bari naje masallaci ana shirin tada sallah"
Mikewa tayi ta ce,
"Nima bari na tashi adawo lapiya."
Bayan ya dawo daga masallacin ba kowa a Babban falon Kai tsaye part d'insa ya koma don yana son yayi waya da Sumynsa.kwanciya yayi akan gadon tare da daukar wayar say yayi dialing din number ta inda yayi sevin number ta da my happiness.
*LONDON*
kwance take akan lapiyayyen Royal chair,tana sanye cikin wando 3 quarter yallow da farin singilet kanta tayi Karin gashin attached ya zubo har gadon bayan ta,ga faratan ta zaro-zaro anyi masu fixing tare da ahafa masu shinning sai d'aukar ido suke.wayar ta dake hannun ta ta kalla ganin Kira ya shigo cikin tsananin Jin dad'i tayi picking din wayar tare da kaiwa kunne.cikin shagwaba tace,
"Haba my happiness meyasa tun since Ina Kiran ka baka dagawa why"?

Ta kara narkar da murya tare da cewa,
"Kuma Kai baka damu da ka kirani ba,sannan idan ni na kiraka baka picking sai kaga dama"
Murmushi yayi tare da cewa
"Sorry my Sumy ki garface ni bana kusa da wayar ne shiyasa.yanxun ma dawowa na masallaci kenan naga kiranki da kuma sak'on da kika turo."
Dariya tayi cikin Jin dadi tace,
Kaima fa kasan bazan iya jure hours ba tare da naji muryar ka ba."
Cikin Jin dadin yadda Sumayya ke nuna masa so yace,
"Nima haka ne a wuri na
zaro ido tayi tare da cewa
"Ba wani Nan nida zan kiraka sau uku kafin ka kirani sau d'aya.wani lokacin baka dagawa ko kuma idan ka d'aga kace
I'M busy right now but I will call you letter.kuma bazaka Kara Kira ba sai dai idan nice na Kira,
Kai ya girgiza don yasan gaskiya ta fad'a kuma shi idan Yana aiki a Asibiti baya son yawan d'aga waya musamman idan yaga Sumayya ke Kiran sa don yasan dogon fira zasuyi har dai idan Yana tare da patient.

"Kinga nasani amma yanayin aikin da nakeyi ne." Dai-dai nan Mummy ta turo k'ofar d'akin tare da sallama.daga Kai yayi ya kalle ta tare da cewa Sumayya Kinga zamuyi magana anjima."
Ta'ba fuska tayi tace
" meye kuma yanzun?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Mummy ce ta shigo"
Yamutse fuska tayi ta ce,
"Ohk to Ina gaishe ta."
ta katse wayar.kallon Mummy ya yi Yana murmushi yace
"Sumayya ce tace na gaishe ki"
Gajeren murmushi mummy tayi Wanda iya fatar baki ta tsaya bata Kai zuci ba,don har ga Allah sumayya bata kwanta mata ba tunda taga pictures d'in ta a wayar Muhdeen taji bata kwanta mata ba.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"Ina amsawa,kaxo ga Dadyn ku nan ya daw daga mitin d'in da yaje."
Ta juya ta fita mik'ewa ya yi yabi bayan Mummy.

Daga alk'amin
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DOMIN K'ARIN BAYANI*
09065327995
Love u oll
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad
akarwa, ilimantarwa da kuma nishad
antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad
ai ke maganin k
ishi_
*Alk
alaminmu
yancinmu*
Wannan kagaggen labari ne,ban Rubuta shi Dan cin zarafi kowaba.idan hali ko suna yazo,to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Page0
Mik'ewa yayi ya bi bayan Mummy kai tsaye upstair din suka nufa part d'in Dady,da sallama suka shiga,Daddy dake zauna kan kujera ya daura laptop akan table yana aiki akai,sanye yake cikin farin jallabiya fuskar sa sanye da farin gilashi,d'ago kai yayi tozali da Babban d'ansa mafi soyuwa a gare shi, murmushi yayi tare da amsa sallamar su.

"Mutanen Egypt barka da dawowa."
Muhdeen d'in ma murmushi ya yi tare da k'arasawa ya ya durk'usa ya gaida mahaifin nasa cikin girmamawa.

"Ina wuni Dady?"
Cikin sakin fuska ya amsa masa.

"Lapiya qalau Muhammad ya gajiyan tafiyar?"
Da Alhamdulillah ya amsa tare da zaunawa kan center carpet d'in dake shinfid'e a tsakiyar falon.

Dady ya rufe laptop d'in dake gaban sa ya juya ya kalli Mummy dake zaune a gefen sa ya ce,
"Ina mufida ce?"
"Tana d'akin ta tana barci"
cewar mummy
Maida dubansa wurin muhdeen yayi tare da cewa,
"Muhammad zuwa gobe idan ka huta sai ka leka asibiti ko?

Domin gaskiya aiki yana yiwa Jabeer yawa a asibitin."
Gyad'a Kai yayi alamun gamsuwa tare da cewa
"Dady insha Allah gobe zan koma aiki na"
"To Masha Allah.Allah yayi maka albarka."
Mummy ce ta amsa da Ameen.
Chapter 3 · 0% Book details