Sashe 57
Inteesar Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Knocking akayi a k'ofar falon, inteesar kama tana can kwance a d'akinta sai kuka take bata ma san anayi ba, Muhdeen ne ya tashi ya he ya bud'e k'ofar, k'anwar Mummynsa ce Aunty Abla tare da Hajiya Bilkisu mai gayaran Amarya, Murmushi Aunty Abla ta sakar masa tare da cewa
"Son wato ko ziyara baby ko?"
Sosa kai yayi tare da cewa
"Bisimillah ku shigo Aunty"
Shigowa sukayi suka zauna a falon inteesar, gaida su yayi cikin girmamawa, suka ansa masa cikin sakin fuska, daga nan ya k'walawa Sumayya kira tare da cewa
"Baby zo ga Aunty Abla ku gaisa, duk da bata so tashi ba haka ta mik'e ta k'araso falon tare da zama kujera ta kalle su tare da cewa
"Hy ya kuke?"
Kallon juna sukayi Aunty Abla da Hajiya Bilkisu, Muhdeen kuma ya dafe goshinsa cike da takaucin abunda Sumayyar tayi, ganin basu amsa va ta mik'e ta kalli Muhdeen ta ce
"Baby bari na kwanta na d'an huta "
Baice mata komai ba ta mik'e ta nufi d'akinta, kallonsa Aunty Abla tayi tare da cewa
"Son where is my daughter?"
Shiru yayi da bai gane wa take tambaya ba, kafin ya ce
"Wai Mufida kike tamabaya?"
Harara ta watsa masa tare da cewa,
"Annan gidan Mufida take da zan tambaye ka? ina 'yata inteesar take?"
"Tana d'aki Ina zaton kamar barci ma takeyi doke ta tashi don ita muka zo gani."
Mik'ewa yayi ya nufi d'akinta, koda ya shiga kwance ya same ta tana kuka? takaici ne yakama shi don yasan tabbas zasu gane inteesar tayi kuka, tsawa ya daka mata wanda hatta su Hajiya Bilkisu da suke falo sunji.
"Ke dalla tashi dukanki akayi ki kuma me?da zaki zo kina kuka ga bak'i munyi salon kija Mani matsala ko?"
Shiru tayi tunda ya fara magana
"To bari kiji, muddin kika bari suka gane wata matsalar wallahi sai nayi masifar 'bata maki rai, dai kukan da zakiyi mai dalili ne, ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuska kizo falo, mik'ewa tayi ta nufi toile shi kuma ya fita zuwa falon, bayanbta wanke ne ta nufi k'ofar zuwa falon.
Tana bud'e k'ofar ne taga su Aunty Abla, da sauri ta sauri ta k'arasa gare su ta rungume Aunty Abla, sannna ta rungume Hajiya Bilkisu ta ce,
"Oyoyo sannunku da zuwa, durk'usawa tayi ta gaida su cikin girmamawa.
"Ina wunni?"
Gaba d'ayansu suka amsa da
" Lafiya k'alau inteesar"
"Ido suka zuba mata ganin yadda ta d'an rame kuma ga fuskarta alamun taci kuka, mik'ewa tayi ta nufi kitchen don kawo masu abun ta'bawa, bayan ta nufi hanyar kitchen ne Aunty Abla ta kalli Muhdeen ta ce,
"Ya naga yarinyar nan ta rame? bata da lafiyane."
"Kafiyarta k'alau Aunty Abla."
Jinjina kai tayi ba tare da ta ce komai ba, inteesar ce ta kawo masu ruwa da lemu ta ajiye zata koma kitchen Aunty Abla ta ce,
"Ina kuma zaki?"
"Zan kawo maku abinci ne"
Murmushi sukayi dukansu inda Aunty Abla ta d'ora da cewa
"Kada ki damu yanzun daga gidan Hajiya Bilkisu muke, sai da muka ci abincin kafin muka zo nan."
Dawo wa tayi ta zauna Kan center carpet dake shimfid'e a wajen tana murmushi ta kwantar da kanta akan k'afar Aunty Abla sannan ta fara magana
"Aunty Abla ba Wanda yazo gani na sai Gwaggo, ko Mummy da Umma na basu zo sun ganni ba."
Murmushi Aunty Abla tayi tare da shafa gefen fuskarta ta ce,
"Jiya munyi waya da Mummy ta ce da zaran Gwaggo ta koma zata zo ta duba ki, nasan da Gwaggo bata nan da tuni tazo ta duba ki, kuma Ummanki kinsan tana da kawaici ba lallai tazo yanzun ba kiyi hak'uri Mummy zata zo maybe gobe ko jibi"
Shiru tayi tare da lamo akan cinyar Aunty Abla, shafa fuskar inteesar tayi abun mamaki sa taji sanyin hawaye a hannunta, kasancewar inteesar ta juyar da fuskarta gefe ba Wanda yaga hawayen da ke tsiyaya, lura da haka yasa Aunty Abla sa hannayenta ta goge mata hawayen, sanna ta ja hannunta zuwa d'aki ta ce,
"Taso mu shiga ciki."
Ba musu tabita suka shiga d'akin intesar tare da tura k'ofar, Muhdeen dai binsu da Ido yayi yana zullumin inteesar ta sanar da ita wani abu mara dad'i, Hajiya Bilkisu ma bayansu ta bi.
A Kan gado Aunty Abla ta zaunar da inteesar ita ma ta zauna gefenta, zuba mata Ido tayi na tsawon mintuna biyu tana nazarinta, dai-dai lokacin Hajiya Bilkisu ta shigo d'akin bakinta d'auke da sallama, gaba d'ayansu suka amsa sallamar ta shigo ta zauna saman side drawer, Aunty Abla ta ce,
"Daughter me ke faruwa?"
Sunkuyar da kanta k'asa tayi
"Bakomai Aunty Abla"
Girgiza kai tayi
"Akwai komai ki sanar dani, ba haka kike ba duk kin rame ga idanunki ma alamar kinci kuka,da alama kina cikin damuwa, nasan ba sonki yake ba zai iya musguna maki ba Wanda ya sani, shiyasa nake son ki sanar dani wata kila akwai irin taimakon da zan maki, yana dukanki ne?
"
Girgiza kai tayi alamar a'a
"Yana zaginki ko cin zarafinki?"
Nan ma kai ta girgiza alamar a'a
"Akwai wani abu da yake maki Wanda baki so ne"
Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba, ganin bata da niyyar magana sai hawaye kawai dake fita daga idanunta yasa Aunty Abla janyo ta jikinta ta rungume ta tare da d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi.
"Nasan kina cikin damuwa sosai duk da cewar ni kamar dangin miji ne a gare ki amma ina son ki d'auke ni matsayin uwa a gare ki, kamar yadda nake jinki kamar 'yar da na haifa a ciki na, kamar yadda ba zaki iya 'boyewa mahaifiyarki damuwarki ba haka nima kada ki 'boye mani yadda na same ki
a haka zuciya ta taji ba dad'i, inteesar me ke damunki ya zamantakewarki da Muhdeen yake?"
Goge hawayen fuskarta tayi ta shiga bawa Aunty Abla labarin zamansu tunda daga lokacin da yake bautar da ita da ayyukan da suka fi k'arfinta har zuwan Gwaggo Wanda lokacin ta samu 'yanci har zuwa yanzun da suke tare.
Aunty Abla da Hajiya Bilkisu sun tausaya mata sosai, ajiyar zuciya Hajiya Bilkisu tayi tare da cewa
"Kenan ba wani abunda ya ta'ba shiga a tsakaninmu na auratayya?